Ashiru Nagoma: Mene ne ke damun tsohon darakta a Kannywood?

Ashiru Nagoma

Asalin hoton, Aminu Barci

Tun bayan da hotunan wani tsohon darakta a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood Ashiru Nagoma suka bayyana da ke nuna shi cikin hali na fitar hayyaci, maganganu suka fara yaɗuwa a tsakanin al'umma kan ainihin abin da ke damunsa.

Rahotanni dai sun ce Ashiru Nagoma ya daɗe a cikin yanayi mai kama da matsalar ƙwaƙwalwa, inda a wasu lokutan har za a gan shi tamkar "ba ya cikin hankalinsa."

Sai dai a ranar Alhamis ne Fauziyya D Sulaiman da ke da cibiyar taimaka wa marasa lafiya ta Creative Helping Needy Foundation CHNF, ta nemi izinin ƴan uwansa inda ta ɗauke shi zuwa asibiti don kula da shi.

Hajiya Fauziyya ta ce kafin sannan sai da ta fara tuntubar ƴan Kannywood a wani zaurensu na Whatsapp don jin ko sun yi wata hoɓɓasa ta taimaka wa Nagoma tun da ya shiga wannan matsala shekaru da dama da suka gabata.

"Sai suka ce min tun lokacin da suka ga halin da yake ciki sun yi ƙoƙarin taimaka masa don kai shi asibiti amma mahaifiyarsa ta hana, ta ce Allah Ya isa duk wanda ya kai shi asibitin masu matsalar ƙwaƙwalwa.

"Da suka ga abu ya so ya zama rigima sai suka bar batun," a cewar Fauziyya.

Tuni dai ƙarƙashin ƙungiyar tata ta CHNF, Fauziyya D Sulaiman ta kai Nagoma asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano AKTH, ɓangaren masu matsalar ƙwaƙwalwa.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ta ce: "A gida muka same shi amma fa sai da aka haɗa da dabara sannan ya yarda aka tafi da shi, ƴan sanda aka je da su aka ce an zo kama shi ya yi laifi, don shi bai taɓa yarda yana da matsalar ƙwaƙwalwa ba.

"A hakan ma ya yi ta maganganu yana cewa laifin me ya yi, a haka dai a muka lallaɓa aka kai shi," in ji Fauziyya.

Fauziyya ta shaida wa BBC cewa yanayin da Nagoma yake ciki da gani lamari ne na tsananin damuwa da ake kira depression. Sai dai duk da haka ta ce yana hira sosai har da amfani da waya, duk da cewa da an fara hirar za a ji ya saki layi.

Kazalika duk da yanayin da yake ciki Nagoma bai daina alaƙanta kansa da ƴan Kannywood ba don kusan ko yaushe yana zuwa matattararsu da ke Gidan Ɗan Asabe a Zoo Road da ke Kano.

"Ya kan je su ba shi ɗan abin ɓatarwa har su kan sa shi a talla ma. Wani lokaci ya dinga ce musu 'don Allah ku ba ni naira 100,000 zan yi fim,' in ji Fauziyya kamar yadda wasu ƴan Kannywood ɗin suka shaida mata.

Tasirin Ashiru Nagoma a Kannywood

Ashiru Nagoma fitaccen mai bayar da umarni ne a masana'antar Kannywood.

A shekarun baya ya yi tashe sosai wajen shirya manyan fina-finai kamar su Tutar So da Zakka da Bajinta da Ƙwalele da Tagwayen Mata da sauran su.

Wani fitaccen mawaƙin fina-finai a Kannywood Abubakar Sani ya shaida wa BBC cewa Ashiru Nagoma mutum ne da ya yi ƙoƙarin haɗa kan jaruman Kannywood sosai a baya da kuma jan kowa a jiki wajen saka su a dukkan fina-finansa.

"Ya yi ƙoƙari wajen haɗa kan jaruman Kannywood ta wajen saka da dama a duk fim ɗin da zai yi. Haka kuma yana ƙoƙari wajen saka waƙokin mawaƙa da dama na lokacin.

"Ya raya al'ada da bunƙasa harshen Hausa a fina-finansa. Sannan ya ringa yin fina-finai a kan matsalolin zamantakewa," in ji Abubakar Sani.

Mawaƙin ya ce da suka ga halin da yake ciki sun saurara ne don su ga me waɗanda suka fi kusanci da shi za su yi, don kar a ce sun yi azarɓaɓi, "amma yanzu an zo daidai kan gaɓar da za mu sa hannu a lamarin," in ji shi.

Shi ma fitaccen Darakta Falalu Ɗorayi da muka tuntuɓe shi ya ce a lokacin da yake kan shahararsa, Nagoma ya fi kowa yawan bayar da aiki a Kannywood.

"Za a iya cewa a lokacin Kannywood kamar One Man Industry ce, ya kan iya haɗa dukkan jaruman Kannywood a fim ɗaya kamar irin su Tutar So da Nagoma.

"Kuma mutum ne da ya taimaka wajen bunƙasa kalmomin Hausa a cikin fina-finansa sosai," in ji Falalu.

Jarumin kuma babban daraktan ya ƙara da cewa "Na yi imani da abu ɗaya, kowane abu ya kan yi lokaci da tashensa sannan ya shuɗe, Allah ne kaɗai Dauwamamme. Don haka kowa ma lokacin shahararsa za ta zo ta wuce.

"Masu ganin su ma lokacinsu ne yanzu, to zai shuɗe," in ji Falalu.

Shi kuwa fitaccen darakta Aminu Saira cewa ya yi tabbas Ashiru Nagoma babban jarumi ne ba na yasarwa ba da ya jima yana jan zarensa.

"Ba mu yi zamani da shi ba a Kannywood, domin yana gaba da mu, amma dai mun ga irin ayyukan da ya yi," in ji Saira.

Silar rashin lafiyarsa

Fauziyya D Sulaiman ta cewa BBC ƴan uwan Nagoma sun ce mata abin ya samo asali ne tun shekarar 2007 lokacin da bidiyon Maryam Hiyana ya yaɗu.

"To a cewarsu a lokacin ya saka kuɗaɗensa ya yi fina-finai wajen bakwai, sai lamarin ya faru inda hukumar tace fina-finai ta ce kar a sake sakin fim ɗin da Maryam Hiyana ta fito a ciki.

"A lokacin ne fa ya shiga ruɗani don rashin madafa ganin cewa ya narka kuɗi ya yi fina-finai da ita, amma dole zai yi asararsu tun ba su fita kasuwa ya mayar da kuɗ ba balle cin riba.

"Lamarin dai ya dagule masa ga asara da ya tafka wacce dole ta sa ya janye daga masana'antar, a hankali damuwar ta dinga tsananta har ta taɓa masa lafiyar ƙwaƙwalwarsa," in ji Fauziyya.

Ashiru Nagoma dai ɗan asalin jihar Kano ne kuma bai taɓa aure ba,

An samu damar kai Ashiru asibiti ne a yanzu tun da babu ran mahaifiyarsa da ta ƙi yarda a kai shi.

Ta rasu shekara bakwai da suka gabata, "amma rashin lafiyar tasa ta tsananta ne shekara biyu da suka wuce," in ji Fauziyyya Sulaiman.