Ku San Malamanku tare da Sheikh Hussaini Zakariyya

Bayanan bidiyo,

Bidiyon Ku San Malamanku tare da Ustaz Husaini Zakariyya

Sheikh Hussaini Zakariya babban limamin masallacin Juma'a na Banex da ke unguwar Wuse 2 a Abuja babban birnin tarayyar Najeiya ya ce sau uku yana samun damar zuwa ƙaro karatu a Jami'ar Musulunci ta Madina amma ya ƙi zuwa.

Shehin malamin ya faɗi haka ne a hirarsa da BBC cikin shirin Ku San Malamanku na mako-mako.

Malamin ya ce Sheikh Abubakar mahmud Gumi ne ya ƙarfafa masa gwiwa cewa gara ya tsaya a Najeriya ya ci gaba da karatu don ya haɗa da na zamani kar a bar shi a baya a wajen fahimtar duniya.

"Baya ga haka akwai malaman da suka dinga gaya min irin wannan magana cewa lallai kar na tsaya a karatun addinin kawai gara na haɗa da na zamani ganin yadda duniya ke sauyawa, cikin su har da marigayi Sheikh Musa Adam," in ji Ustaz Zakariyya.

Amma ya ce ya sha halartar daurorin da jami'ar ke shiryawa a Jami'ar Bayero ta Kano, kuma ya sha halartar taruka a ƙasashe irin su Saudiyya da Masar.

Wane ne Sheikh Hussaini Zakariyya?

An haifi Ustaz Hussaini Zakariyya Yawale a garin Kaduna ranar 1 ga watan Oktoban 1960 a unguwar Abakwa, wanda ya yi daidai da 10 ga Rabi'u Thani shekara ta 1380 bayan Hijira.

Mahaifinsa malamin addinin Musulunci ne na Mazhabar Malikiyya kuma a hannunsa ya fara karatu.

"Karatuna ne ya haife ni ya raine ni, a cikinsa na girma a cikinsa na tsufa, ina kuma son mutuwa a cikinsa.

Mahifinsa Sheikh Zakariyya Yawale, shi ne ɗalibin Sheikh Abubakar Mahmud Gumi na farko kuma Na'ibinsa mai ja masa baƙi a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna.

Malamin ya ce yana alfahari da malamansa uku a rayuwa da suka haɗa da mahaifinsa da Sheikh Isma'ila Iidris Zakariyya wanda ya assasa ƙungiyar Izala, sannan sai wanda ya sa shi a makaranta Sheikh Mahmud Gumi.

"Na rayu tsakanin makaranta da gidan Sheikh Gumi da kuma gidanmu.

Ya yi makarantar horar da malaman Arabiyya a Katsina. Sannan ya yi Jami'ar Bayero Kano inda ya karanta Larabci da addinin Musulunci da Tarbiyya.

Cikin malamansa na lokacin har da Sheikh Ahmad Kala Haddasana.

Lamarin Bitcoin

Bayan ya kammala digiri na farko ya so ya tafi ƙarin karatu sai dai nauyin iyali da na ƴan uwa ya yi masa yawa. Amma ya sha halartar taron ƙara wa juna ilimi.

Sai da ya shekara 60 sannan ya je ya yi digiri na biyu har ma ya yi rubutu a kan matsayin Bitcoin a addinin Musulunci a Jami'ar Keffi.

Ya yi hakan ne don fitar da matsaya mai amfani ga Musulmai don ka da a bar su a baya "don kuwa mu'amalar kuɗn intanet ɗinnan ta zo tare da zamani ne," in ji shi.

A yanzu kuma ya samu gurbin ƙaro karatun digirin-digirgir a Malaysia, annobar korona ce ta hana shi tafiya amma sai je daga baya.

Wasannin ƙuruciya

Asalin hoton, Huseyn Zakariyya Facebook

Ustaz ya ce ya yi wasanni na ƙuruciya da suka haɗa da ƙwallo ya da wasan damben Boxing da Tennis da Volley Ball da Hockey da kuma Karate.

"Na shahara sosai a wasan Hockey a yankin Katsina a lokacin."

Babban abin da ya fi faranta masa rai shi ne cin jarrabawar Grade II da ya yi a lokacin da aka yi wa makarantarsu tambari cewa ba a cin jarrabawar.

Abin da ya fi baƙin cikinsa kuma shi ne rashin mahaifiyarsa wadda ta tsaya tsayin daka wajen ba shi goyon baya a karatunsa da tarbiyyar rayuwarsa.

Baiwa da ayyuka

Malam ya ce Allah ya yi masa baiwar riƙe alwala tsawon yini.

Shi ne wanda aka fara tura wa yankin ƙasashen Igbo don kula da al'amuran wadanda suka musulunta don su koyi addini.

Shi ya fara fassara huɗuba da Turanci da Hausa a masallacin da ke ofishin jakadancin Saudiyya a Legas.

A shekarar 1990 kuma yana cikin limaman farko na masallacin rukunin gidajen 1004 da ke Legas.

Sannan a 1995 ya zamo limami na farko na Masallacin Syria da ke Barikin Dodon a Legas.

Malam yana da mace fiye da ɗaya da ƴaƴa 10 sai jikoki.