Biden Inauguration: Me Joe Biden zai fara yi?

President-elect Joe Biden

Asalin hoton, Getty Images

Joe Biden ya shafe shekara 50 a fagen siyasa inda yake ƙoƙari ya ga ya cimma wannan burin, sai dai bai taɓa tsammanin zai tarar da irin wannan ƙalubalen a gabansa ba. Waɗanne abubuwa zai fi mayar da hankali a kai?

Zai shafe kusan kwanaki goma yana dokoki na musamman da ƙarfin shugaban ƙasa ya ba sa iko.

Irin waɗannan dokokin ba su buƙatar amincewar majalisar tarayya.

Cikin manyan abubuwan da ke cikin jerin abubuwan da Biden ɗin zai mayar da hankali akwai batun haramcin da gwamnatin Trump ya saka wa wasu ƙasashen Musulmi na shiga Amurka inda Shugaba Trump ya ce ƙasashen barazana ne ga tsaron Amurka.

Haka kuma Mista Biden ɗin zai mayar da hankali kan batun yarejejeniyar sauyin yanayi ta Paris.

Ga sauran abubuwan da ake sa ran Biden ɗin zai mayar da hankali a kansu bayan an rantsar da shi.

Yaƙi da annobar korona

Matakin saka takunkumi a Amurka

Annobar korona ta kashe sama da mutum 400,000 a Amurka - ana sa rai cewa annobar korona da kuma tasirinta ne muhimmin abin da gwamnatin Biden za ta mayar da hankali a kai.

Mista Biden ya ce annobar ce "yaƙi mai muhimmanci da gwamnatinmu zai ta fuskanta" kuma shugaban ya yi alƙwarin aiwatar da sabon tsarinsa na yaƙi da korona nan take.

Ɗaya daga cikin matakan nasa akwai batun saka takunkumi a duk wani wuri mallakar gwamnatin tarayya haka kuma a duk lokacin da ake tafiye-tafiye tsakanin jihohi.

Sai dai har yanzu babu wani tabbaci kan cewa gwamnonin jihohin Amurka waɗanda akasarinsu ke sukar matakin saka takunkumi za su sauya ra'ayinsu kan lamarin - haka kuma babu wata doka da ta bai wa shugaban ƙasa ikon tilasta saka takunkumi a duka ƙasa.

Da alama Mista Biden ya gane hakan inda ya bayyana cewa da kansa zai yi ƙoƙari wajen ganin cewa ya shawo kan gwamnoni kan wannan lamari.

Asalin hoton, Los Angeles Times via Getty Images

Idan gwamnonin ba su amince ba, ya sha alwashin zai yi kira ga magaddai da jami'an birane su rungumi wannan tsarin nasa. Babu tabbaci har yanzu kan yadda za a aiwatar da wannan tsari.

Rigakafi miliyan 100 a kwana 100

Mista Biden na so ya gaggauta yin riga-kafi a Amurka inda yake da burin tabbatar da cewa an yi wa mutum miliyan 100 a cikin kwana 100 na farko da zai yi kan mulki.

Ɗaya daga cikin hanyoyin gaggauta yin riga-kafin ita ce ta fitar da duka riga-kafin da ake da su domin yi wa mutane a maimakon ajiye su ga waɗanda za a yi wa karo na biyu.

Asalin hoton, Getty Images

Ana kuma sa ran cewa shugaban zai ɗauki matakin gaggawa na tabbatar da cewa an samar da hanyoyin gwajin korona cikin sauri da kuma samar da kayayyakin aiki da magunguna da kuma kayayyakin kariya.

Sake shiga Hukumar Lafiya Ta Duniya, WHO

Daga cikin abubuwan da ake tunanin Biden zai yi, akwai batun sauya matakin da Amurka ta ɗauka a baya na barin Hukumar Lafiya Ta Duniya.

Mista Trump ya bayyana shirye-shiryen ficewa daga ƙungiyar ne a kwanakin baya inda yake zargin WHO ɗin da gazawa wurin daƙile korona bayan ɓullarta daga China

Dokoki na musamman da zai aiwatar - Ga wasu daga cikin sabbin dokokin da ake tunanin Biden zai aiwatar da zarar ya shiga ofis

  • Amurka za ta koma cikin yarjejeniyar Paris ta sauyin yanayi
  • Cire dokar da ta haramta wa wasu ƙasashen Musulmi shiga Amurka
  • Tilasta saka takunkumi a wurare mallakar gwamnatin tarayya da kuma yayin tafiya tsakanin jihohi
  • Ƙara wa'adin haya ga ƴan haya da waɗanda ake bi basussuka sakamakon annobar korona
  • Ci gabada dakatar da biyan basussukan ɗalibai a lokacin annobar

Matakan tattalin arziƙi

Sauƙaƙa wa ƴan haya da masu gidaje

Kwamitin kamfe na Mista Biden ya bayyana cewa akwai shirye-shiryen da gwamnatin ke yi na tsawaita lokaci ga ƴan haya da ke gidajen haya da waɗanda ake bi basussuka - haka kuma da batun dakatar da biyan bashin da ɗaliban tarayya suke yi.

Kwamitin karɓar mulki na Biden ya shaida cewa Biden ɗin na ƙoƙarin fitar da shiri na musamman inda zai ba wasu ma'aikatu umarnin bayar da kayan agaji ga iyalai da ke aiki a ƙasar, sai dai babu wani ƙarin bayani kan irin abubuwan da za a bayar.

Tiriliyan $1.9 ga tattalin arziƙin Amurka

A makon da ya gabata ne Mista Biden ya sanar da cewa za a fitar da tiriliyan $1.9 domin bayar da tallafi ga mutanen ƙasar sakamakon irin raunin da annobar korona ta yi wa tattalin arziƙin ƙasar.

Asalin hoton, The Boston Globe via Getty Images

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Idan majalisar tarayya suka amince da wannan kuɗin, hakan zai haɗa da biyan dala 1,400 ga kowa a Amurka.

Haka kuma shugaban ya yi tsarin bai wa makarantu tallafin kudi domin su sake buɗewa ba tare da wata matsala ba, haka kuma yana so makarantun su buɗe a cikin kwanaki 100 bayan kama aiki.

Hakan zai zama ƙari ga dala biliyan 900 na kuɗin tallafi da majalisar ta amince a Disamban bara.

Da wuya ƴan majalisa daga Jam'iyyar Republican su ƙi amincewa da kudirin, wanda hakan zai zama ƙari ga bashin da Amurka ta kashe a yaƙi da annobar korona, haka kuma Mista Biden zai buƙaci duka jam'iyyun biyu su haɗa kansu.

A yanzu dai ƴan Democrats su ke da iko da duka majalisun biyu, amma da tazara kaɗan.

Kawo ƙarshen sabbin dokokin harajin da Trump ya sa

Ba bayar da tallafin Trump ne kawai abin da sabon shugaban ya sa a gaba ba. Ya yi alƙawarin soke sauye-sauyen da Mista Trump ya yi a dokokin haraji.

Mista TRump ya yi sauyin ne a 2017, a farkon shugabancinsa kuma Biden ya ce ba a yi adalci ba musamman ga ƙananan masana'antu.

Haka kuma Biden ya ce zai ruɓanya harajojin da kamfanonin Amurka su ke biya kan ribar da suka samu daga ƙasashen waje.

Amma fa wannan ƙudirin nasa zai bi ta hannun majalisa tukuna.

Muhalli da Sauyin Yanayi

Zai mayar da Amurka Yarjejeniyar Paris

Wani abu da Mista Biden ya ce zai yi a ranarsa ta farko a mulki shi ne komawa yarjejeniyar Paris ta sauyin yanayi, wata yarjejeniya da ta ƙunshi tabbatar da tsare yanayi ƙasa da 2.0c.

Trump ya janye Amurka ne daga yarjejeniyar a 2015, inda ta zama ƙasa ta farko da ta yi haka.

Mista Biden ya ce yana so ya yi aiki da majalisar dokokin ƙasar wajen sa dokar da za ta bai wa Amurka damar rage fitar da gurɓatacciyar iska zuwa shekarar2050.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Soke dokokin sauyin yanayi

Wani abu kuma da sabon shugaban ya ce zai yi shi ne soke wasu manufofin sauyin yanayi da Trump ya kafa.

Mista Biden ya ce zai tattauana sosai kan gurɓatacciyar iskar da motoci ke fitarwa da tsare kashi 30% na kasa da ruwan ƙasar zuwa 2010, sannna zai rufe filin Arctic National Wildlife Refuge da ake haƙar mai.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Sabuwar gwamnatin ta ce a shirye ta ke ta taƙaita fitar da iskar methane a yayin sarrafa man fetur da iskar gas.

Manufofin Ci Rani

Soke dokar shiga ƙasar

Dokar da Mista TRump ya sa kwana bakawai bayan hawansa mulki a 2017 ta hana ƴan wasu ƙasar shiga Amurka na ɗaya daga cikin dokokin da Biden zai soke.

Asalin hoton, AFP

Da farko dokar haramcin ta shafi wasu ƙasashen Musulmi bakwai ne amma daga baya an yi sauye-sauye bayan da kotu ta sa baki a maganar.

A yanzu kasashen Iran da Libya da Somalia da Syriya da Yemen da Venezuela da Koriya ta Arewa ne ke ƙarƙashin dokar haramcin.

Za a sauƙaƙa wa 'yan gudun hijira zama ƴan ƙasa

Wani babban alƙawari da Mista Biden ya ɗauka shi ne na gaggauta aikewa majalisa ƙudirin doka da za ta bai wa 'yan gudun hijira sama da miliyan 11 da ke zaune a ƙasar damar zama ƴan Amurka.

A lokacin yaƙin neman zaɓensa, Mista Biden ya ce zai kafa da kwamitin da zai haɗa yara ƴan ci rani 545 da aka raba da iayyensu a iyakar Amurka.

A watan Disamba, tawagar Biden ta ce za ta buƙaci lokaci don ta soke ɗaya daga cikin manufofin Mista Trump mai suna Migrant Protection Protocols da ta tursasa wa dubban masu neman mafaka a ƙasar su jira a Mexico kafin kotuna a Amurka su saurari kokensu.

Jami'ai sun ce wannan na iya ɗaukar wata shida.

Kawo ƙarshen gina katanga

Mista Biden ya yi alƙawarin tsayar da ginin katangar da Mista Trump ke alfahari da ita - katangar da ya fara ginawa tsakanin Amurka da Mexico. Kamfe din Biden ya kira wannan gini "ɓarnar kuɗi".

Ya kuma ce maimakon ɓatar da kuɗin da a ke yi a katangar, za a yi amfani da kuɗin wajen tsaurara matakan tantancewa a iyakokin ƙasar.

Asalin hoton, AFP

Kawo sauye-sauye a batutuwan wariyar launin fata da shari'a

Baya ga batutuwan cutar korona da tattalin arziƙi da sauyin yanayi - Mista Biden ya ce dole ne ya duba batun wariyar launin fata.

Ya yi alƙawarin kafa rundunar da za ta taimaka wajen kawo sauyi a rundunar 'yan sandan ƙasar a kwanaki 100 na farko.

Kare auren jinsi ɗaya

Ya yi alƙawarin taimakawa masu auren jinsi ɗaya da mutanen da suka sauya jinsi ta hanyar zuba kuɗi a ɓangarorin da ke kare waɗannan rukuni na mutane daga cin zarafi.

Sannan ya ce zai kawo ƙarshen haramcin da aka ɗora wa mutanen da suka sauya jinsi na shiga aikin soja da dawo da hanyoyin wayar wa da yara kai kan batutuwan sauya jinsi a makarantu.

Ya kuma ce zai sa hannu kan dokar daidaito wadda za ta bai wa 'yan maɗigo da 'ya luwaɗi damramaki.

Kwantarwa da ƙawayen Amurka hankali

Sabon shugaban ya ce yana da shirin sasantawa da ƙawayen Amurka da aka samu rashin jituwa da su kuma ya yi alƙawarin "Amurka na nan tare da su", inda ya ce dole ne Amurkar ta "nuna wa duniya a shirye ta ke ta sake jagorantar duniya kuma ta zama misali ga sauran ƙasashe".

Ya ce a ranarsa ta farko a babban ofishin shugaban ƙasa ko Oval Office, zai aika sako ga ƙawayen ƙasar na NATO cewar |mun dawo kuma muna nan tare da ku".

Duk da cewa ba Mista TRump ne shugaban ƙasa na farko da ya matsawa 'yan ƙungiyar NATO lamba ba wajen ƙara kasafin kuɗi a kan tsaro, ya yi masu barazana a wasu lokuta da cewar zai janye daga gamayyar.