Me ya sa har yanzu kasashen Afirka ba su fara kaddamar da allurar riga-kafin korona ba

Asalin hoton, AFP
Afirka ta Kudu na da adadi mafi yawa na wadanda suka kamu da cutar korona a Afirka
Afirka ta Kudu ita ke da fiye da daya bisa uku na duka yaduwar cutar korona a kasashen Afirka kuma adadin wadanda ke kamuwa na karuwa bayan bullar sabuwar nau'in cutar.
Amma ba kamar wasu daga cikin kasashen da annobar korona ta fi shafa ba a fadin duniya, har yanzu Afirka ta Kudu bata fara shirin bayar da allurar rigakafin korona ba.
Shin Afirka ta Kudu ta samu ruwan alluran rigakafin korona?
Shugaba Cyril Ramaphosa ya ce Afirka ta Kudu ta samu allurar rigakafi kimanin miliyan ashirin, wanda ake sa ran fara rabawa a farkon rabin shekarar 2021.
Amma babu cikakkun bayanai kan takamaimen lokacin da za a kaddamar da shirin wanda za a yiwa mutane kusan miliyan arba'in allurer rigakafin.

Asalin hoton, Getty Images
Afirka ta Kudun tana kokarin samu alluran rigakafin ta hanyoyi uku:
•Ta hanyar shirin Covax da Kungiyar Lafiya ta Duniya ke jagoranta
•Ta hanyar tsare-tsaren da Kungiyar Hadin Kan Afirka ta yi
•Ta hanyar kwangiloli tsakanin kasashe da kamfanoni masu sarrafa allurer rigakafi.
Shirin Covax wani shiri ne da kasashen duniya suka saka kudadensu don tallafawa wajen samar da alluran rigakafin da nufin tabbatar da cewa duka kasashen sun samu adadin da ya kamata na ingantattun allurarn rigakafin.
Afirka ta Kudu na sa ran samun adadin allurarn rigakafin ga kashi 10 bisa dari na yawan al'ummar kasar ta hanyar shirin na Covax , kuma an fada mata cewa za ta same su daga watan Aprilu zuwa na Yuni.
A shekarar da ta gabata ne Kungiyar Hadin Kan Afirka ta nada tawagar gudanar da aikin samar da alluran rigakafin, don samar wa da kasashen Afirka adadin allurarn rigakafin na korona.
Amma da alamu ba za a iya samun alluran rigakafin har na tsawon watanni.
Ma'aikatar lafiya ta ce ta yi wata yarjejeniya tsakaninta da cibiyar samar da ruwan allurai ta kasar India, mafi girma wajen sarrafa alluran rigakafi a duniya, kan samun adadin alluran rigakafin kimanin miliyan daya da rabi.
Da farkon fari dai kasar na son yi wa ma'aikatan kiwon lafiya rigakafin ne. Amma kuma da adadin ma'aikatan miliyan daya da dubu dari biyu da aka kiyasta, da alamu kashin farko na alluran rigakafin ba zai wadatar ba.
Shin ya kamata a ce Afirka ta Kudu ta samu alluran rigakafin tun tuni?
An shiga damuwar cewa kasashe matalauta da tsaka-taki da dama , an bar su a baya a fagen samun alluran rigakafin a duniya.

Asalin hoton, AFP
Amma kuma, masu suka sun bayyana cewa, bai kamata a ce Afirka ta Kudu mafi karfin tattalin arziki a Afirka ta kasance a wannan matsayi ba.
''Gaskiyar magana ita [Afirka ta Kudu] bata samu ko kuma tsara yadda za a samu wadatattun ruwan alluran da za a yiwa jama'a da dama rigakafin ba, idan aka yi la'akari da yadda ya kamata a duba abubuwan da ka iya faruwa a gaba,'' in ji kungiyar tuntuba ta Progressive Health Forum, wacce ta kunshi manyan masana harkokin kiwon lafiya a kasar.
Me gwamnati ta ce?
Dr Anban Pillay, mukaddashin darakta janar na Ma'aikatar Lafiya ya ce , kasar na tattaunawa da kamfanonin sarrafa magunguna tun daga watan Satumbar bara.
"An yi tattaunawa da dama a cikin shekarar da ta gabata," in ji Dr Pillay.
Ya kare muradan tsare-saren gwamnati.
"Ruwan alluran rigakafin da sauran kasashen suka saya, allurai ne da ba lallai su yi daidai da bukatun Afirka ta Kudu ba ta bangarori da dama," ya bayyana.
Ya ce ruwan alluran rigakafin na kamfanin Pfizer/BioNTech ba zai isa a yiwa dimbin mutane ba, musamman ma a kauyuka, saboda bukatar da sukae da shi na samun wurin ajiya mai ma'aunin sanyin da ya kai 70C.
Ya yi nuni da cewa kwamitin bayar da shawarwari ya yi gargadi kan amfani da ruwan alluran.
"Muna jiran zuwan sauran ruwan alluran rigakafin da za mu iya amfani da su wajen kaddamar da shirin yi wa mutane da yawa rigakafin, amma har yanzu ba a samu ba tukuna," ya ce.
Ya kuma ce wasu kasashen sun fara amfani da alluran rigakafin ba tare da kammala yin gwaji ba, wanda masu lura da amfani da maguguna a Afirka ta Kudu ba za su amince da hakan ba.
Me yasa kasashen Afirka har yanzu basu samu alluran rigakafin ba?
Kasashen Afirka da dama
Shirin kaddamar da rigakafi na bukatar ruwan allurar rigakafin. Kasancewar kasashen Afirka ba za su iya sarrafawa da samar da ruwan alluran rigakafin cutar korona ba, dole ne sai da sus hu shigo da su daga waje.
Samun nasarar kaddamar da shirin yin rigakafin ka iya sake hada Afirka da sauran kasashen duniya, yayin da zai kara inganta tsarin kiwon lafiya a nahiyar.
Amma kuma gazawar kasashen ka iya jefa nahiyar cikin mummunar barazanar annobar cutar korona, da kuma matsalolin da za ta haifar musu kan tattalin arziki da cigaban kasashen.
Ya batun yake a kasar Ghana?
Kasar Ghana na daga cikin kasashen Afirka da suka dukufa wajen ganin cewa sun samu ruwan allurer rigakafin koronar domin kaddamar da shirin yiwa jama'a a cikin wannan shekarar.
Shugaban kasar Nana Akufo-Addo ya nada wani kwamiti da zai duba yadda za a shigo da allurer rigakafin mai inganci, wacce ba za ta cutar da jama'a ba.
Amma kuma duk da kokarin da gwamnatin kasar ta ce tana yi
A Najeriya kuma fa?
A cikin watan Disambar shekarar da ta gabata ne yunkurin gwamnatin Najeriya na sayo allurar rigakafin korona ya gamu da kace-nace, bayan da inda 'yan majalisun tarayya suka nuna shakkun game da shirin gwamnatin kan yadda za ta iya alkinta ruwan allurar bayan auno su zuwa cikin kasar.
Sai dai a baya-bayan nan mahukuntan sun ce kasar a shirye take ta karbi kashin farko na ruwan alluran rigakafin korona daga wajen nan da karshen watan Janairu.
Gwamnatin na son ta yi wa kasha 40 bisa dari na yawan al'ummar kasar rigakafin nan da zuwa karshen wannan shekarar, inda ta ce za ta yi wa kasha 30 bisa dari zuwa cikin karshen shekara.
Mahukuntan sun ce bayan yi wa shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo allurer rigakafin koronar na kamfanin Pfizer, ana sa ran kashin farko na ruwan allurer zai samu a cikin wannan watan.
Daga bisani kuma za a rarraba wa manyan masu rike da mukaman gwamnati da ma'aikatan kiwon lafiya don su wayar da kan jama'a kafin a fara kai wa ga sauran 'yan kasar.
"Mun tsara yadda za mu samar da isassun alluran rigakafin ta hanyar karkasawa. Muna ta burin yi wa kasha 70 bisa dari na yawan al'ummar kasar don tabbatar da ganin an dakile yaduwar cutar," in ji wani jami'n gwamnatin Najeriyar.
Rashin wurin adanawa
Amma kuma masana sun ce inda matsalar take shi ne wuraren adana ruwan alluran rigakafin.
Sun ce najeriyar ba ta da ingantattun wuraren adana alluran rigakafin da ke bukatar ma'aunin sanyi na 70C.
Kana kuma ga tsadar shi kansa ruwan alluran rigakafin, da hakan mawuyaci ne a ce Najeriya ta iya samarwa da yawan al'ummar kasar a nan kusa, in ji masanan.
Kasashen na fuskantar kalubale na samun isassun alluran rigakafin korona saboda tsananin tsadarsu.
Amma kuma shirin COVAX da kungiyar lafiya ta duniya WHO ke jagoranta na kokarin tabbatar da ganin kasashe kamar Najeriya ba a bar su a baya ba in ji mahukuntan kasar.
Najeriyar da tattaunawar cinikayya da kamfanoni masu sarrafa ruwan allurer rigakafin a kasashen Birtaniya da China da kuma Russia, kuma ta ce ta fi son ta samu irin wadnda ke da sauki wajen adanawa.
Sudan ta Kudu
Kasar Sudan ta Kudu ta ce a shirye ta ke ta fuskanci wannan kalubale na kokarin samar da allurer rigakafin korona ga 'yan kasar.
"Ba mu san me gobe za ta Haifa ba, saboda har yanzu wasu abubuwan ba a bayyane suke ba,'' in ji Evans Arko Shawish'', in ji babban jami'in gangamin allurer rigakafin cututtuka masu yaduwa a ma'aikatar lafiya ta Sudan ta Kudu,'' amma a shirye muke mu fara gudanar da shirin allurer rigaafin yaki da cutar ta korona gadan-gadana kasar."
Akwai yiwuwar rashin wayar da kan jama'a da kuma yada jita-jita game da sahihancin alluran rigakafin zai iya shafar yadda al'ummomin kasashen za su yarda da shugabanninsu su amince da rigakafin.
Masana sun ce dole kasashen Afirka sun yi kokarin shawo kan wannan matsala muddin suna son su cimma burin yi wa yawan al'ummarsu rigakafin kamuwa da cutar ta korona.
Hukumomin lafiya na kasa da kasa sun ce, kafin kasashen na Afirka su kai ga nasarar cimma wannan buri na yi wa akalla kasha 60 bisa dari na yawan al'ummarsu rigakafin, akwai bukatar samun adadin biliyan daya da rabi na ruwan allurar rigakafin wanda aka kiyasta za su lakume kudi daga tsakanin kimanin dala biliyan takwas zuwa sha shida.

Asalin hoton, Reuters
Wani bincike da Jami'ar Duke a Amurka ta gudanar yan una cewa baya ga kasashe masu karfin tattalin arziki, akwai kasashe matalauta da dama da suka tabbatar da yarjejeniyar cinikayyar allurer rigakafin.
A cikin kasashe 20 da aka annobar korona ta fi muni, da dama sun riga sun fara gudanar da shirin allurer rigakafin.
Kuma a cikin kasashen da suke da yawan wadanda suka kamu fiye da mliyan daya, baya ga Afirka ta Kudu, akwai sauran da hara yanzu bas u far aba kamar su Colombia, da Peru, da Ukraine da kuma Iran.
Kasashen da suka yi nisa wajen gudanar da allurer rigakafin korona
Tun a cikin watan Yulin shekarar da ta gabata ne kasashe masu karfin tattalin arziki kamar su Birtaniya da sauransu, sun rattaba hannun yarjejeniya na samun alluran a yayin da suke kan gwaje-gwaje da kuma kokarin sarrafa ruwan allurar rigakafin.
Birtaniya
Kuma masana sun bayyana cewa kasashen da suka iya fara biyan kudi da wuri, sun eke da damar samu akan kari.
Yanzu haka ana kan gudanar da yin allurer rigakafin na korona karo ba biyu a Birtaniyar, yayin da aka sake amincewa da fara kasha na uku.
Isra'ila ta yi zarra wajen rigakafin korona.
Israel's Covid vaccine rollout is the fastest in the world — here are some lessons for the rest of us
Yayin da Amurka da Birtaniya da kasashen Turai suka yunkura wajen shirin gudanar da allurer rigakafin korona, kasar da ta yi musu fintinkau it ace Isra'ila.
A ranar 19 ga watan Disambar shekarar bara ne Firaminista Benjamin Netanyahu ya zama mutum na fako da aka yi wa allurer rigakafin a kasar.
An kuma bai wa masu shekaru da suka wuce shekaru sittin da wadanda ke da barazanar kamuwa da cutar da kuma ma'aikatan kiwon lafiya fifiko.
Ta yi wa sauran kasashen da suka fara gudanar da rigakafin zarra.
Kuma har yanzu kuma duk da dokar kullen koronar da aka shiga a kasar, kusan mutane sama da miliyan daya da rabi ne suka samu aka yi musu allurar rigakafin ta farko, kamar yadda wani binciken kiwon lafiya na duniya a kasar ya bayyana.
Kasar India
A kwanakin da suka gabata ne kasar India ta kaddamar da gangamin farko na rigakafin kamuwa da cutar korona mafi girma a duniya, da ake sa ran yi wa mutune miliyan 300 kafin watan Yulin wannan shekarar.
Kasar ta India da aka kiyasta cewa yawan al'ummarta ya kai kimanin biliyan 1,3 ta soma gudanar da allurar rigakafin na korona a daidai lokacin da ake cigaba da fama da matsalar yawan yaduwar cutar.
Har iya yau kasar ko baya ga yi wa ma'aikatan kiwon lafiya rigakafin, ta ce ta ware karin mutane dubu dari da hamsin da za su taimaka wa malaman kiwon lafiya wajen zartar da aikin rigakafin a wasu cibiyoyin allurai 700 da kasar ta tanada.
Haka kuma, wasu kasashe kamar Brazil da Mexico da suka iya fara gwajin allurer rigakafin, sun yi amfani da hakan a matsayin wata hanya ta samun shigo musu da ruwan alluran.