EFCC: Tsoffin jami'an gwamnatin Najeriya da za a tuhuma a shekarar 2021

BABACHIR RAMALAN

Hukumar EFCC a Najeriya ta fitar da sunayen tsoffin jami'an gwamnati da za a ci gaba da sauraren ƙararsu a wannan shekarar.

Hukumar ta ce a ko yaushe tana cikin shirin kama masu laifukan cin hanci da rashawa.

Ga jerin mutanen kamar haka:

George Turnah

George Turnah shi ne tsohon mai bai wa Dan Abia, tsohon Daraktan Hukumar NDDC mai Kula da Ci Gaban Yankin Neja Delta, shawara.

An sake tsare Turnah ne ran 22 ga watan Janairu tare da Ebis Orubebe da Uzorgor Silas Chidiebere bisa zargin samun kuɗi ta hanyar damfara da sama da faɗi da kuɗi da yawansu ya kai Naira 2,894,500,000.

Sannan ana zarginsu da wulaƙanta martabar muƙamansu.

An fara shari'arsu ne a 2017 kuma ana sa rai za a ci gaba a ranakun 15 da 16 da 17 na wannan shekara ta 2021 a gaban Alƙali Mohammed Turaki na Babbar kotu da ke zamanta a Fatakwal.

Adesola Amosu

Tsohon babban hafsan sojin sama ne kuma babban jami'i a Rundunar Sojin Saman Najeriya.

Mista Amosun na fuskantar shari'a ne a gaban Justice Chukwujekwu na babbar kotun tarayya da ke zama a unguwar Ikoyi a jihar Legas.

Haka kuma ana tuhumarsa ne tare da Air Vice Marshall Jacobs Adigun, wani tsohon jami'i a bangaren kuɗi na rundunar sojin saman.

Tare da wani jami'ain Air Commodore Owodunni Olugbenga, wani tsohon darekta a ɓangaren kuɗi duk dai a rundunar.

Duk dai ana zarginsu ne da karkatar da kuɗin rundunar Naira biliyan 21 don yin harkar gabansu.

Za a ci gaba da sauraren ƙarar a ranakun 12 da 15 da 20 na watan Afrilun 2021.

Babachir Lawal

Babachir Lawal

Ana sauraren shari'ar tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ne a gaban Alƙali Charles Agbaza na babbar kotun babban birnin tarayya da ke Jabi a Abuja.

An yi wa shari'ar Babachir laƙabi da "grass-cutting scandal" wato badaƙalar yanke ciyawa.

Babachir na fuskantar shari'a ne tare da ƙaninsa Hamidu Lawal da wani Suleiman Abubakar da Apeh John Monday da wasu kamfanoni biyu - Rholavision Engineering da Josmon Technologies.

Ana zarginsu da haɗa baki wajen aikata mugayen laifuka da karkatar da kuɗin da yawansu ya kai Naira miliyan 544.

Hukumar EFCC ta ce ta gabatar da shaidu biyu da takardu da dama don tabbatar da ƙararta a kansu.

Za a ci gaba da sauraron ƙarar ran 17 ga watan Fabrairun 2021.

Abubakar Mohammed Sani

Mataimakin shugaban hukumar gidan yari na jihar Katsina wanda ake zargi da samun kuɗi da yawansu ya kai Naira 2,850,000 daga mutanen da ya yi wa alƙawarin ba su aikin gwamnati.

An fara tsare shi ne ran 9 ga watan Disambar 2020 a gaban Alƙali Hadiza Sabi'u Shagari ta babbar kotun tarayya a Katsina kuma ya ce bai amsa laifin ba.

An dage shari'ar sai ranar 3 da 4 fa watan Febrairun 2021.

Mukhtar Ramalan Yero

Tsohon gwamnan jihar Kaduna na fuskantar shari'a a gaban Alƙali Z.B Abubakar da ke babbar kotun tarayya a Kaduna.

Ana zarginsa da sa hannunsa a "raba" Naira miliyan 700 da tsohuwar ministar mai Diezani Allison-Madueke ta samar don yin maguɗi a zaben shugaban ƙasa na 2015.

Mukhtar Ramalan Yero

Asalin hoton, FACEBOOK

Ana tuhumar Yero tare da tsohon ƙaramin minista Nuhu Somo Waya da tsohon shugaban jam'iyyar PDP na jihar Kaduna Abubakar Haruna Gaya da tsohon sakataren jihar Hamza Ishaq.

An ɗage ƙarar sai ranar 23 ga watan Fabrairun 2021.

Kabiru Tanimu Turaki

Shari'ar tsohon ministan harkoki na musamman tare da mai taimaka masa na musamman, Sampson Okpetu ta ci gaba ranar 25 ga watan Janairun 2021.

Ana zarginsu da yin sama da faɗi da kuɗin Naira miliyan 714.6 inda Justice Inyang Ekwo ke sauraren ƙarar a wata babbar kotu da ke Abuja.

An dage sauraron ƙarar sai ranar 9 ga watan Fabrairun 2021.

Babangida Aliyu

Shari'ar tsohon gwamnan jihar Neja ta fuskanci matsaloli da dama tun da EFCC ta fara tuhumarsa a 2017.

Tuni aka gurfanar da shi a gaban alƙalai da dama.

Babangida Aliyu

Asalin hoton, OTHERS

An gaza ci gaba da shari'ar tasa ranar 18 ga watan Janairun 2021 saboda alƙalin da ke sauraren ƙarar, Justice A.B Aliyu ba ya nan.

Don haka, sai aka dage ta sai 29 ga watan Maris 2021.

Ana tuhumar tsohon gwamnan ne tare da Shugaban Ma'aikatansa, Umar Nasko bisa zargin almundahana da kudi Naira biliyan 2.

Haka kuma EFCC ta zarge shi da karkatar da kuɗin asusun gyara muhalli na jihar don yin harkokin gabansa.

Andrew Yakubu

Justice Ahmed Mohammed na babbar kotu da ke Abuja ya tsayar da 7 ga watan Fabrairun 2021 a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan buƙatar EFCC ta kai ziyara babban bankin Najeriya, reshen jihar Kano don bincike kan kuɗi $9,772,800 da £74,000 da aka alƙanta da Yakubu.

Mista Yakubu dai tsohon Darakta ne a kamfanin mai na ƙasa NNPC.

EFCC na tuhumar Yakubu almundahana bayan bayanai da ta samu da wani mai kwaramata bayanan sirri.

EFCC ta kai farmaki gidansa da ke unguwar Sabon Tasha a garin Kaduna kuma ta yi nasarar gano kudi a wata ma'ajiya ta musamman da wuta ba ta iya lalatawa.

An ɗage ranar sauraron ƙarar sai 29 ga watan Maris, 2021.

Mohammed Adoke

Shari'ar tsohon ministan shari'a kuma Antoni Janar na Najeriya, Mohammaed Adoke, kan almundahana wadda ya kamata a yi ranar 11 ga watan Janairun 2021 ta tsaya cik saboda wanda ake ƙarar bai zo ba.

Mohammed Bello Adoke

Asalin hoton, @OFFICIALEFCC

Dama dai Justice Inyang Ekwo na babbar kotu da ke Abuja ne ke sauraren ƙarar.

An ruwaito cewa Adoke ya maƙale a Dubai bayan da ya kamu da cutar korona. Kotun ce ta ba shi damar tafiya Dubai din don duba lafiyarsa.

An bayyana cewa yana daf da dawowa Najeriya ne lokacin da ya fahimci yana ɗauke da cutar.

Ana tuhumar Adoke ne tare da Aliyu Abubakar kan almundahana. Ana sa ran za a ci gaba da shari'ar ne ranar 1 ga watan Maris din wannan shekarar.

Olisa Metuh

An daɗe ba a ji duriyar shari'ar almundahana da ake yi kan tsohon kakakin jam'iyyar APC Olisa Metuh ba.

EFCC ta tabbatar da an yanke masa hukunci ranar 25 ga watan fabrairun 2020.

Sai dai bayan bitar hukuncin, EFCC ta dangana ga Kotun Ƙoli don yin watsi da Kotun Ɗaukaka Ƙara bisa hujjar cewa kotun ta yi wasu kura-kurai a hukuncin.

Sai dai ran 16 ga watan Disambar 2020, Kotun daukaka ƙarar ta tabbatar da ƙarar da Metuh ya shiga kuma ta yi watsi da hukuncin da Justice Okon Abang ya yanke masa a babbar kotu da ke Abuja.

A lokacin Metuh ya riga ya fara wa'adin da aka yanke masa na shekara 7 a gidan yarin Kuje.

Amma a yanzu, EFCC ta koma Kotun Ƙoli inda ta buƙaci ta yi watsi da ƙarar kotun ɗaukaka ƙarar.

Orji Uzor Kalu

orji uzor kalu

Tsohon gwamnan jihar Abia kuma tsohon Bulaliyar Majalisar Dattijan Najeriya ya fara zaman wa'adin da aka yanke masa na shekara 12 a gidan kason Kuje lokacin da Kotun Ƙolin ƙasar ta yi watsi da hukuncin da Justice Idris Mohammed ya yi a wata babbar kotu da Legas.

Kotun Ƙolin ta bayyana cewa a lokacin da alƙalin da ya saurari ƙarar ya yanke hukunci, an yi masa ƙarin girma zuwa alƙalin kotun ɗaukaka ƙara don haka ba shi da hurumin yanke hukuncin.

Don haka ne kotun ƙolin ta buƙaci a sake yi wa Kalu shari'a kan zargin almundahana da Naira biliyan 7.1.

A kan haka ne wata babbar kotu a Abuja ta sa 2 ga watan Fabrairun 2021 a matsayin ranar sauraren ƙarar.

Abdulrasheed Maina

Abdulrasheed maina

Asalin hoton, FACEBOOK/ABDULRASHEED_MAINA

Bayan gabatar da shaidu 9 a shari'ar don tabbatar da almundahana da Maina ya yi na kuɗin fansho Naira biliyan 2, ya buƙaci kotun ta sallame shi ranar 9 ga watan Disamba 2020 a gaban kotun Justice Okon Abang da ke Abuja.

Justice Abang ya ɗage ƙarar zuwa 10 ga Disambar 2020 don bai wa Maina damar kare kansa sannan EFCC ta bayyana dalilanta na ƙalubalantarsa.

Sai dai a ranar ne Maina ya yanke jiki ya faɗi a kotun.

Dama kafin nan Maina ya ƙi bayyana a kotu bayan bayar da belinsa inda ya ja har aka kama mai tsaya masa, Sanata Ali Ndume a madadinsa.

EFCC ta haɗa kai da ƴan sandan ƙasa da ƙasa aka kama Maina a Nijar kuma aka dawo da shi gida Najeriya don fuskantar shari'a.

Murtala Nyako

Murtala Nyako

Ranar 16 ga watan Janairun 2020 ne EFCC ta rufe ƙarar da ta ke yi ta almundahanar Naira biliyan 29 da tsohon gwamnan Adamawa Nyako ya yi.

Sai dai maimakon su ƙalubalanci ƙarar, Nyako da sauran waɗanda ake ƙara cikin har da ɗansa Abdul-Aziz sai su ka ce kotu ta yi watsi da ƙarar.

Wannan ne ya sa Justice Okon Abang ya sa 26 ga Fabrairun 2021 ranar da za a sake zaman sauraren buƙatarsu.

Gabriel Suswam

Shari'ar Gabriel Suswam ta kasance ɗaya daga cikin shari'o'in tsoffin gwamnoni da aka dade ana yi.

gabriel susmwa

Asalin hoton, Getty Images

Ranar 2 ga watan Nuwambar 2020 ne aka gurfanar da tsohon gwamnan tare da kwamishinan na kuɗi Omodachi Okolobia a gaban Justice Ahmed Mohammed na wata babbar kotu da ke Abuja.

Ana zarginsu ne da yin sama-da-faɗi da kuɗi Naira biliyan 3.1.

Alƙalin ya umarci kotu ta bi duka bayanan da suka danganci ƙarar bi-da-bi don tabbatar da cewa sun cika kuma an sa hannu a kansu.

Wannan ne zai ba da dama a ci gaba da shari'ar daga inda aka tsaya.

Doyin Okupe

Doyin Okupe

Asalin hoton, FACEBOOK

Okupe dai tsohon mai taimakawa Goodluck Jonathan ne na musamman.

EFCC na tuhumar Okupe ne da kamfanoninsa biyu da sama-da-faɗi da kuɗi da karkatar da kuɗi N702,000,000.

Justice Ijeoma Ojukwu ta wata babbar kotu da ke Abuja ta ɗage zaman sauraren ƙarar Okupe ran 16 ga Nuwambar, 2020.

Winifred Oyo-Ita

Tsohuwar Shugabar Hukumar Ma'aikatun Gwamnati na fuskantar tuhumar cin hanci da rashawa da sama-da-fadi da kuɗi wanda yawansu ya kai Naira miliyan 570.

Ana tuhumar Oyo-Ita tare da wasu kamfanoni.

An ci gaba da shari'arsu a gaban Justice Taiwo Taiwo na wata babbar kotu da ke Abuja ranar 28 ga Janairu, 2021.