Shaidu sun bayyana yadda jirgi ya yi hatsari a Abuja

Shaidu sun bayyana yadda jirgi ya yi hatsari a Abuja

Latsa hoton sama ku kalli bayanin yadda abin ya faru

Shaidun da suka gane wa idonsu sun bayyana yadda wani jirgin sojoji ya yi hatsari a Abuja ranar Lahadi.

Kakakin rundunar sojin sama ta Najeriya Air Vice Marshal Ibikunle Daramola ya ce dukkanin mutum bakwai da ke cikin jirgin ne suka mutu a hatsarin.

Babban Hafsan Sojin Sama na Najeriya Air Vice Marshal Oladayo Amao ya kafa kwamitin bincike kan musabbabin hatsarin.

Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya ce jirgin mai suna King Air 350 ya yi hatsari ne bayan ya samu matsalar na'ura a lokacin da ya tashi, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter.

Vice Marshal Daramola ya faɗa wa BBC cewa jirgin na kan hanyarsa ta zuwa ceton mutum 42 ne da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar Neja kafin ya juya zuwa Abuja saboda matsalar na'ura.

Jirgin wanda ba shi da girma ya faɗo ƙasa a kusa da garin Basa da ke babban birnin ƙasar, Abuja.

Waɗanda suka gane wa idonsu sun faɗa wa BBC cewa sun ji ƙara mai ƙarfi kafin jirgin ya kama da wuta.

Tazarar kilomita 100 ne tsakanin Minna, babban birnin Jihar Neja, da kuma Abuja.

Bayanai sun ce jirgin yana cikin wadanda Najeriya ta yi sayo domin ayyukan tsaro da leken asiri a ƙasar.

Sunayen sojojin da suka rasu

Rundunar sojan sama ta Najeriya ta bayyana sunayen mutum bakwai da suka rasa rayukansu a hatsarin kamar haka:

  • Flight Lieutenant Haruna Gadzama (Captain)
  • Flight Lieutenant Henry Piyo (Co-Pilot)
  • Flying Officer Micheal Okpara (Airborne Tactical Observation System (ATOS) Specialist).
  • Warrant Officer Bassey Etim (ATOS Specialist)
  • Flight Sergeant Olasunkanmi Olawunmi (ATOS Specialist)
  • Sergeant Ugochukwu Oluka (ATOS Specialist)
  • Aircraftman Adewale Johnson (Onboard Technician).

Shugaba Buhari na alhini

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya miƙa ta'aziyyar rasuwar fasinojin jirgin da ya yi hatsari a Abuja ranar Lahadi.

Shugaban ya bayyana alhininsa ne cikin wani saƙon Twitter, inda ya kwatanta sojojin a matsayin "jajirtattu".

"A madadin Gwamnatin Tarayya, ina miƙa ta'aziyyata ga 'yan uwa da abokan waɗanda suka rasu," in ji Buhari.