Daga baƙonmu na mako: Yadda iyaye a Najeriya kan biya kudin makaranta amma a bar su da nauyin koya wa 'ya'yansu karatu

School children

Asalin hoton, UNICEF/FACEBOOK

Bayar da ilimi a matakin farko shi ne shimfiɗar da ake buƙata domin cim ma muradin samar da ingantaccen ilimi ga ƴan ƙasa.

A Najeriya bai wa yara ilimi a matakin farko wajibi ne kuma kyauta a tsarin doka. Makarantun da ke wannan mataki su ne nasiri da firamare, inda ƙananan yara ƴan shekara uku zuwa 11 ne galibin ɗaliban.

Saboda rauninsu na rayuwa, ana so a dinga lallaɓa su, a ririta su, kuma a ba su kulawa ta musamman wajen koyar da su. Hakan na nufin sai malamai sun bi su a hankali kuma su sa su bisa kyakkyawar turbar karatu.

Sai dai, bisa ga dukkan alamu, tsarin bayar da ilimi a matakin farko a Najeriya ba ya tafiya yadda ya kamata. Wannan tasgaro da aka samu, bai rasa nasaba sakacin wasu gwamnatoci kan sha'anin ilimi, ciki har da rashin kulawa da makarantu mallakinsu - inda a bisa tsari, kyauta ya kamata a rika bai wa yara ilmi.

To amma domin nema wa kai mafita, iyaye da dama musamman a birane sun fi maida hankali ga kai 'ya'yansu makarantu masu zaman kansu duk da tsadar kudin makaranta idan aka kwatanta da makarantun gwammnati.

Wannan kuma ya sanya karin mutane da kungiyoyi na ta bude makarantu masu zamna kansu - galibi kuma ana ganin ba domin kishin ilmi ba, sai domin kasuwanci da neman kudi.

Kuma waɗannan makarantu sun mamayi harkar ilimi a ƙasar, musamman a matakan Firamare da Sakandare.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Na fahimci akwai gwamnatocin wasu jihohi ƙalilan da ke ƙoƙarin taƙaita tasirin irin waɗannan makarantun.

Wasu makarantu na bata rawarsu da tsalle

Ko shakka babu, makarantu masu zaman kansu na bayar da gagarumar wajen ci gaban harkar ilimi a dukkan matakai a Nijeriya, musamman wajen cike gibin da ake samu saboda gazawar makarantun gwamnati.

To amma sannu a hankali, da dama daga cikin waɗannan makarantu na ɓata rawarsu da tsalle, kamar yadda lamuransu ke nunawa a baya bayan nan. Da dama daga cikin iyaye da mariƙa yara, waɗanda ƴaƴansu ke halartar irin waɗannan makarantun, suna ƙorafin cewa, makarantun sun mayar da su saniyar tatsa, domin sun fi mayar da hankali a kan neman kuɗi fiye a maimakon ilimantar da yara. Sanannen abu ne galibin makarantu masu zaman kansu suna da ɗan karen tsada.

Wasu makarantun ba su yarda iyaye su saya wa 'ya'yansu kayan makaranta a kasuwa ba - sai dai su saya a hannun makarantun, galibi a farashi fiye da na kasuwa. Kama daga litattafai na karatu da rubutu, zuwa kayan sa wa na makaranta wato inifam - kai hatta jaka wasu makarantun ba su yarda a saya wa yara a wani wuri idan ba a makarantar ba.

Haka nan iyaye da dama na kokawa kan adadin jinga wato assignment da akan bai wa ɗalibai barkatai. Wannan aikin na karatu ko rubutu da akan bai wa ɗalibai, su tafi da shi gida, su yi, yana ƙara musu azama da shauƙin karatu. Hasali ma, yana cikin manhaja da kuma jimshikin karatu a dukkan matakai tun fil azal.

To amma a baya-bayan nan iyaye da kuma masu lura da lamura na cewa malamai da dama kan tabta wa dalibai jinga fiye da kima, inda a wasu lokutan kusan assignment ko jingar takan fi koyarwa a cikin aji yawa. Wasu na zargin cewa kamar wasu malaman na guje wa nauyin dake kansu na koyarwa ne su fake jinga kana su maida nauyin koyar da yaran kan iyaye a gida.

Kalubalen da ake fuskanta

Ko da ya ke dama ya kamata iyaye su rika tallafa wa malamai wajen yi wa yaransu bitar karatu a gida, da kuma yin jingar, to amma masana na ganin idan jingar ta fi koyarwa a makaranta yawa, akwai illa.

Wasu iyayen su kansu ba su yi karatun da zai ba su dama har su iya koyar da yaran ko kuma taimaka masu wajen yin jingar a gida ba, wasu kuma ba su cikakken lokacin da a kullum za su keɓe domin taimaka wa ƴaƴansu wajen yin jingar da suka taho da ita daga makaranta, baya ga sauran dawainiyoyin da suka wajaba a kan iyaye.

Ala tilas wasu iyayen kan ɗauki karin malami ya rika taimaka wa ƴaƴansu da darussa a gida suna yi wanda ke nufin karin kashe kudi. Marasa hali kuwa, sai ƴaƴansu su jagwalgwala abin da za su iya yi na jingar, ko kuma, idan ba su yi ba, su fuskanci hukunci a makaranta. Wannan yanayi na kara takura yara da iyayensu - idan tafiya ta yi nisa kuma ka iya yin illa ga karatu da kuma fahimta ta yaran.

Sai dai ƴan magana na cewa, "Idan ɓera na da sata, daddawa ma na da wari". A wannan zamanin, wasu iyayen tamkar gasa suke yi game da irin makarantu da suke tura 'ya'yansu. Wasu daga cikinsu, bisa kuskure, sun ɗauka tsadar makaranta ita ke nuna ingancinta. Wasu makarantun sun gano lagon wasu iyayen.

Mene ne makarantun ke cewa?

Asalin hoton, OTHER

Bayanan hoto,

Sai dai wasu masu makarantu masu zaman kansu na musanta zarge-zargen da ake yi masu

Sai dai wasu masu makarantu masu zaman kansu na musanta zarge-zargen da ake yi masu, suna ganin wadanda ke zarginsu da fifita neman kuɗi a kan ilimantar da yara ba su fahimci lamarin ba ne. Alhaji Malami Salihu, Shugaban ƙungiyar Masu Makarantu Masu Zaman kansu Ta Ƙasa (NAPPS) a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, ya shaida mani cewa suna karɓar kuɗin makaranta ne gwargwadon ɗawainiya da ɗalibai da suke yi.

Malami ya ci gaba da cewa, su ma suna dawainiya sosai wajen tafiyar da makarantu. Ya ce da waɗannan kuɗaɗen ne suke biyan malamai da sauran ma'aikata da kuɗin haya ga waɗanda ba a cikin ganinsu suke ba. A cewarsa, hatta gwamnati na samu a jikinsu saboda suna biyan ta haraji da sauran kuɗaɗe nan da can.

Game da batun bayar da jinga mai dimbin yawa da dalibai kan yi a gida kuwa, ya ce akwai bukatar iyaye su fahimci cewa batun bayar da ilimi bai taƙaita ga makaranta ba kaɗai, su ma iyaye akwai gudummawa da ya kamata su dinga bayarwa a gida dangane da karatun na ƴaƴansu. Ya kara da cewa ba a bai wa yara aikin karatu da ya fi karfinsu, kuma ana basu jingar ne domin kada su shagala idan suka tafi gida.

Ina mafita daga matsalar?

Ta kowacce fuska za a kalli wannan lamari'abu guda da ya tabbata shi ne, tsarin bayar da ilimi a matakin farko a Najeriya ya tabarbare kuma yana bukatar gyara.

Da farko, Manhajar Karatu a ƙasar na buƙatar a yi mata garam bawul. Sannan kuma a dinga sabunta ta daga lokaci zuwa lokaci, don ta dacewa da bukatun ci gaban kasa da makomarta - ta fuskar kimiya da fasaha da tattalin arziki da kuma zamantakewa da tarbiya, ta yadda Najeriya za a iya cimma burinta na yin gogayya da sauran kasashe.

Kamata yi malamai da hukumomin makarantu su sanya muradin bai wa yara ilmi mai inganci a gaba da duk wata bukata kana a rika kula da hakkokin malaman makarantu domin kara masu kaimi.

Ita gwamnati ta inganta makarantu mallakinta, kana ta ƙara saka ido kan al'amuran makarantu masu zaman kansu a duk matakai na ilimi a ƙasa. Hakan zai hana su miƙe ƙafa da da kuma ci da gumin iyaye da ake zarginsu da yi. Su ma iyaye su na da rawar takawa wajen kula da ilmin 'ya'yansu da kuma tattaunawa daga lokaci zuwa lokaci tare da hukumomin makarantu domin fahimtar juna da kuma cimma matsaya mafi dacewa kan ilmin yara.

Ƴan magana na cewa, "Bai kamata a kama mai dokar barci yana gyanygaɗi ba."

Saboda haka, ya zama wajibi, gwamnati ta waiwayi makarantunta na Firamare da Sakandare da nufin fitar da su daga cikin mummunan hali da suke ciki. Sakacin gwamnati ne tunda farko ya sa harkar ilimi ta yi matukar tabarbarewa.

Muddin ilmi a matakin nasiri da firamare ya inganta, to akwai kyakkyawan fatan cewa sauran matakai na gaba su ma za su inganta, ta yadda yara da kuma al'uma ba ki daya zata samu kyakkyawar makoma.

Wannan maƙala ce ta musamman daga baƙonmu na mako: Umar Yunus, ɗan jarida mai zaman kansa a Jos, babban birnin jihar Filato da ke Najeriya.