Enugu: Yadda kudirin biyan gwamnoni da matansu fansho ya haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya

Kudurin ya haifar zanga-zanga a Enugu

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Kudurin ya haifar zanga-zanga a Enugu

Majalisar Dokokin Jihar Enugu ta jingine wani ƙudirin dokar fansho na tsofaffin gwamnoni da mataimakansu da matansu wanda ya haifar da ce-ce-ku-ce a kafofin sada zumunta da kuma zanga-zanga.

Matakin ya biyo bayan suka da ƙalubalantar kudirin da jama'a suka yi a ranar Talata kan kuɗirin da ke neman biyan tsoffin gwamnonin da mataimakansu da matansu biliyoyin naira a matsayin fansho na har tsawon rai.

Haka kuma an nuna hotunan wasu mutanen Enugu a kafofin sada zumunta suna gudanar da zanga-zanga domin adawa da kudurin dokar.

Jaridar Cable ta ce ta samu kwafi na kudirin dokar kuma a ciki ta ga an yi wa gwamnoni ƙari da kusan kashi 900 na abin da za su dinga ƙarba duk shekara idan sun sauka.

Kudirin kuma a cewar jaridar ya shafi biyan matan tsoffin gwamnonin na jihar Enugu kuɗaden alawus duk shekara da suka kai kusan naira miliyan 12.

Batun wanda ya ja hankali da haifar ce-ce--ku-ce da zanga-zanga ya tilasta wa majalisar dokokin jihar fitowa ta bayyana cewa ta jingine kudirin.

An nuna hoton bidiyon shugaban Majalisar dokokin jihar ta Enugu yana yi wa masu zanga-zanga a harabar majalisar jawabi.

A cikin bidiyon an ji shugaban majalisar Edward Uchenna Ubosi yana cewa yanzu suka jingine kuɗirin

"Ku bari mu yi nazari kan kudurin, karatu na farko kawai aka yi bayan gabatar da shi. sai mun diba mun ga abin da za mu cire ko mu ƙara," in ji shi.

Me ake cewa?

Ƴan Najeriya da ke tsokaci a Twitter na ganin ya kamata gwamnati da ƴan majalisar Enugu su mayar da hankali kan ayyukan ci gaban al'umma amma ba azurta gwamnoni ba.

@UchePOkoye ya ce: Samar da ayyukan ga matasa ya kamata ƴan majalisar Enugu su mayar da hankali akai

@AkingbolaR tambaya ya yi cewa: Shin wai akwai magabata a Enugu kuwa, wai me suke cewa akai.

A ra'ayin @the__henry cewa ya yi: Enugu ta ma'aunin talauci ya kai kashi 58.1 tana son biyan gwamnoni fansho har tsawon rai. Allah ya sa ma an yi watsi da shi.