Yadda ake ƙayyade sadaki mafi ƙaranci da nisabin Zakkah da haddin sata a Musulunci

Farashin sadaki na hawa yana sauka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Farashin sadaki na hawa yana sauka

Addinin musulunci ya fitar da hanyoyi na ƙayyade nisabin Zakkah da lissafin diyya da mafi ƙarancin sadaki da haddin sata.

Kwamitin Fadar Sarkin Musulmin Najeriya na fitar da bayani kan nisabin Zakkah da mafi ƙarancin sadaki da haddin sata da kuma diyya daga lokaci zuwa lokaci.

Daga ranar 19 ga watan Maris na 2021 nisabin Zakkah ya kai N1,810,160, kuɗin sadaki mafi ƙanƙanta da haddin sata ya kai N22,627.

Lissafin diyya kuma a yanzu ya kai N90,508,000, kamar yadda Kwamitin Fadar Sarkin Musulmin Najeriya ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

Yadda ake ƙayyadewa

Domin sanin yadda ake ƙayyade nisabi da kuma lissafin diyya da mafi ƙarancin sadaki da haddin sata, BBC ta tattauna da Imam Murtadha Gusau, babban limamin masallacin Juma'a na Nagazi-Uvete na Alhaji Abdur-Rahman a Okene.

Malamin ya ce ana kiyasi ne da darajar zinari - farashin da ake sayar da cikakken nauyin zinari. Wato kamar naira dubu 21 da ake sayar da giram (4.25).

  • Nisabin Zakkah

Nisabin zakkah na kuɗi shi ne zinari 20 - idan a naira ne kuɗin Najeriya, za a yi lissafin nawa naira za ta sayi zinari 20.

  • Diyya

Zinari 1,000 ne lissafin diyya na kashe ran musulmi. Idan misali a kuɗin Najeriya ne za a yi lissafin nawa naira za ta sayi zinari 1,000, abin da ya bayar shi ne kuɗin diyya.

  • Sadaki da haddin sata

Ana ƙayyade mafi ƙarancin sadaki da haddin sata daga rubu'i - wato kashi ɗaya bisa huɗu na zinari.

Wato idan an raba zinari kashi hudu nawa misali naira za ta saye shi - shi ne nisabin sadaki da haddin sata da za a yanke hannun ɓarawo idan an bi ka'idoji da shari'a ta gindaya cewa ba a cikin yunwa da talauci ya shiga ya yi sata ba, sai a yanke masa hannu.

Ta waɗannan hanyoyin da aka bayyana a sama ake fitar da ƙiyasin sadaki mafi kankanta da diyyar rai da kuma nisabin zakkah.

Amma lissafin yana hawa kuma yana sauka ta la'akari da dajarar zinari da kuma darajar kudi. Misali a watan Janairu a Najeriya mafi ƙarancin sadaki ya kai N23,946, inda kuma yanzu ya dawo kan N22,627 a watan Maris.

Kuma kamar yadda ake amfani da naira haka masu amfani da dala da yuro da fan za su yi amfani wajen yin lissafin nisabin zakkah da mafi ƙarancin sadaki da haddin sata da kuma kudin diyyar ran musulmi.

Dole sai adadin da aka ƙayyade na sadaki?

Asalin hoton, Getty Images

Imam Murtadha ya ce idan an bi ra'ayin malaman hadisi ko nawa aka biya na sadaki ba laifi ba ne.

"Malaman fikihu ne suka yanke cewa dole sadaki sai ya kai adadin kashi ɗaya bisa huɗu na zinari sannan aure ya ƙullu."

"Amma ga malaman hadisi ana iya ƙulla aure idan sadakin bai kai adadin da aka ƙayyade ba domin suna dogaro da wani hadisin daga Manzon Allah SAW inda Annabi ya yi sadaki da abin da ba kudi ba," in ji malamin.

Ya ce lokacin da annabi ya aurar da wata mata ga wanda surorin Al Kur'ani kawai ya haddace ya nuna ko ba kuɗi ana yin sadaki.

Imam Murtadha ya ce: "Ana sadaki da kuɗi da kuma abin da ba kuɗi ba."

Bayanan bidiyo,

Hirar BBC da angon mata biyu a rana ɗaya

Kuma malamin ya ƙara da cewa a shari'a ko nawa nawa mutum ya biya ba laifi ba ne.

Ya danganta da yarda da amincewaar juna tsakanin mace da namiji. "Duk abin da mace ta amince yana iya zama sadaki - tana iya cewa ma ta yafe sadakin"

"Idan mutum yana da halin biyan miliyan 10 a matsayin sadaki idan ya biya ba laifi ba ne."

Amma malamin ya ce annabi ya kwaɗaita da yin rangame a wurin aure - annabi ya faɗa cewa duk auren da ya fi sauki shi zai fi albarka - hakan ya nuna ana son a sawwaka wurin aure.

"Amma ko nawa aka biya na sadaki, aure ya yi."