Muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a makon nan

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a makon da ya gabata a Najeriya, daga Lahadi 14 ga Maris zuwa Asabar 20 ga Maris.

Tsadar kayayyaki a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

A ranar Litinin hukumar ƙididdiga ta Najeriya wato NBS ta fitar da rahotonta inda ta ce an samu hauhauwar farashin da ya kai kashi 17.33 cikin ɗari a watan Fabrairun da ya wuce.

Alƙaluman sun nuna cewa tashin farashin ya ƙaru ne da kashi 1.54 a Fabrairun 2021 idan aka kwatanta da kashi 1.49 a watan Janairu. Kuma farashin kayan abinci ya tashi da kashi 21.79 a Fabrairun da ya gabata idan aka kwatanta da kashi 20.57 a watan Janairu.

Hukumar ta ce wannan ne karon farko da aka samu irin wannan tashin farashi a cikin shekaru hudu da suka wuce.

Alƙaluman hukumar sun nuna farshin kayan abinci ya yi tashin gwauron-zabo a makwanni biyun da suka wuce lokacin da kungiyar fataken dabbobi da kayan abinci da ƴaƴanta suka yi yaji inda har ta kai ga sun datse hanyar kai kayayyaki daga yankin arewacin Najeriya zuwa kudanci.

Rahoton ya nuna cewa tashin farashin kayan abinci ya shafi kayan abinci irin su burodi da nama da kifi da dankali da kuma farashin kayan miya da na kayan marmari ko kayan lambu.

Satar ɗalibai da malamai a makarantar firamare a Kaduna

Asalin hoton, Getty Images

Harin da aka kai wata makarantar firamare a kauyen Rema da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna ya ja hankali kasancewar karon farko da ƴan bindiga suka kai karkata ga makarar firamare sabanin satar ɗalibai da suka saba a makarantun sakandare.

A ranar Litinin ne gwamnatin Kaduna ta ce an kai hari makarantar firamare kuma an saci ɗalibai da malamai.

Amma daga baya gwamnatin ta ce babu wani ɗalibi da ƴan bindiga suka sace a makarantar amma kuma an tafi da wasu malaman makarantar guda uku.

Wannan na zuwa ne yayin da jami'an tsaro suka daƙile yunkurin sace wasu ɗalibai a wata makaranta a jihar ta Kaduna.

Har yanzu hukumomi na ci gaba da kokarin kubutar da ɗaliban kwalejin horas da ma'aikatan gandun daji fiye da talatin da har yanzu suke hannun 'yan bindigar.

Ɓullar baƙuwar cuta a Kano

Asalin hoton, Getty Images

Ɓullar wata baƙuwar cuta a Kano arewa maso yammacin Najeriya ya tayar da hankali a jihar.

Hukumomin lafiya a jihar Kano sun tabbatar da mutuwar mutum hudu sakamakon bullar cuta a jihar.

Shugaban kwamitin kar-ta-kwana na cibiyar dakile cutuka masu yaduwa da ke asibitin Muhammadu Abullahi wasai, Dakta Bashir Lawal ya ce tabbatar da cewa sun samu bullar wata cuta da ba a kai ga gano ta ba, wadda mutanen da ta kama ke fitar da jini da amai da gudawa.

Kwararren likitan ya ce "Mutum hudu sun mutu dalilin wannan cuta, ta kashe biyu a asibiti da kuma kashe mutum biyu da suke jinya a gida.

"Ya zuwa yanzu cutar ta kama mutum 189 wadanda suke asibitoci mabambanta da aka ware domin yaki da wannan cuta" in ji likitan.

Rahotanni dai sun danganta cutar da shan wani lemu dan tsami da ya haifar da ɓarkewar Fitsarin jini da amai.

Sunday Igboho ya fitar da Yarabawa daga Najeriya

Asalin hoton, SUNDAY IGBOHO

A ranr Alhamis ne mutumin da ke ikirarin fafutukar kare hakkin Yarabawa, Sunday Igboho, ya ce kabilar Yarbawa za ta balle daga Najeriya saboda rashin adalcin da ake yi mata.

A cewarsa, sun dauki matakin ballewa daga Najeriya ne sakamakon kashe-kashen da makiyaya suke yi wa Yarbawa a jihohin kudu maso yammacin kasar.

Ya yi kira ga dukkan Yarbawa su amince da matakan da shugaban kungiyar kafa kasar Yarbawa ta Nigerian Indigenous National Alliance for Self-determination, Farfesa Banji Akintoye yake dauka na tabbatar da kasar Yarbawa mai cin gashin kanta.

A kwanakin baya, Mai magana da yawun shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu, ya ce Babban Sifeton Ƴan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya bayar da umarni a kamo Sunday Igboho bayan ya yi barazanar korar Fulani daga yankin kaɓilar Yarabawa.

Sai dai har yanzu ba a kama shi ba kuma ana ganinsa yana yawo a bainar jama'a.

'Watsi da tsarin karɓa-karɓa a 2023 a jam'iyyar PDP'

Asalin hoton, @PDP

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wani kwamitin tuntuɓa da jam'iyyar adawa ta PDP ta kafa a Najeriya ya bayar da shawarar a duba cancanta maimakon bin tsarin karɓa-karɓa yayin tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 mai zuwa.

Mambobin kwamitin sun ce duk da cewa wasu na ganin ya kamata a fifita yankunan arewa maso gabas da kudu maso yamma, amma kowane ɗan Najeriya ya cancanci a ba shi damar yin takara ƙarƙashin tutar jam'iyyar.

A ranar Laraba ne gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed wanda shi ne shugaban kwamitin mai mamba 14, ya bayyana matsayar kwamitin yayin da yake gabatar da rahoto ga shugabanni a sakatariyar jam'iyyar ta ƙasa da ke Abuja.

An kafa kwamitin ne domin gano dalilin da ya sa jam'iyyar ta yi rashin nasara a babban zaɓen 2019 da zummar bayar da shawarar yadda za ta sake ɗare wa mulkin Najeriya.

Amma sai babban kwamitin jam'iyyar da ake kira National Executive Committee (NEC) ya amince da shawarwarin da kwamitin ya bayar kafin a aiwatar da shi.

Neman ɗage haramcin wa'azi kan Shiekh Abduljabbar

Majalisar malaman Musulunci ta ƙasa a Najeriya, (Nigeria Council of Ulama,) ta yi kira ga Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya ɗage haramcin yin wa'azi kan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara tare da buɗe makaranta da masallacinsa.

An ruwaito Sheikh Dan'azumi Tafawa Balewa, yana magana da manema labarai a garin Bauchi a ranar Alhamis, yana cewa majalisar ta damu da haramcin da aka yi wa malamin.

Ya ce bisa damar da kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowa na yin addinin da yake so da kuma adalci, ya kamata Ganduje ya ƙyale Abduljabbar ya ci gaba da wa'azi.

"Wannan 'yanci da kundin tsarin mulki ya bayar ya yi daidai da koyarwar Alƙur'ani mai tsarki a wajen da Allah ya ce 'Babu tilastawa a addini," in ji malamin.

"Muna girmama ra'ayoyin mutane mabambanta kuma burinmu shi ne mu yi tayin tattaunawa da fahimta tsakanin Musulmai masu mabambantan ra'ayoyi.

Gwamnatin Kano dai ta hana Abduljabbar gudanar da wa'azi tare da yi masa ɗaurin talala a gidansa bayan an zarge shi da yin kalamai a wa'azinsa da za su iya tayar da fitina a ƙasa.