Abin da Kanawa ke cewa kan gina sabuwar gadar da Ganduje zai yi a Hotoro

Gadar Buhari ta Kano

Asalin hoton, Kano Govt

Mazauna Jihar Kano da ke arewacin Najeriya suna bayyana ra'ayoyi daban-daban kan yunƙurin gwamnatin jihar na gina sabuwar gada a shataletalen unguwar Hotoro.

A ranar Talata majalisar zartarwar jihar, cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai Muhammad Garba ya fitar, ta amince da kashe naira biliyan tara don gina gada mai hawa uku a shataletalen unguwar Hotoro da ke birnin.

Sanarwar ta ce gwamnatin za ta gina gadar ne da kudin da za ta aro daga Babban Bankin Najeriya, kuma kafin gwamnatin ta kammala wa'adinta za ta biya kudin.

Shataletalen Hotoro ya yi ƙaurin suna wajen cunkoson ababen hawa musamman da safe da kuma yamma, inda take cunkushewa a wasu lokutan har a shafe sa'o'i a haka.

Hanyar ita ce mashigar birnin Kano daga jihohin Arewa Maso Gabas kamar Bauchi da Gombe da Adamawa da Borno kuma tana ɗaya daga cikin mashiga birnin daga Jihar Jigawa.

Duk da cewa akwai masu sukar gina gadar da dama, a hannu guda kuma an samu masu kare matakin na gwamnati sannan ita ma gwamnatin ta fadi dalilan yin gadar.

Matsayar masu sharhi

Dr Kabiru Sufi, malami a kwajein share fagen shiga jami'a ta CAS Kano kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, ya ce ginin gadar na da muhimmanci kuma akwai akasin hakan.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

"Gaskiya gina gadar abu ne mai muhimmanci sosai idan aka yi la'akari da yadda wajen yake cunkushewa da ababen hawa a kowane lokaci, yin gadar zai kawo sauƙin al'amura.

"Amma kuma a baya akwai alamun gwamnatin tarayya na shirin aiwatar da aikin gina gadar tun da dama titin Kano zuwa Maiduguri da gadar za ta ratsa na gwamnatin tarayya ne.

"Don gaskiya kudin da gwamnatin jiha za ta kashe ya yi yawa sosai. Da za a bari gwamnatin tarayya ta shiga cikin lamarin ta gudanar da aikin da zai fi, duk da cewa dai ita gwamnatin tarayya aikinta kan ɗauki lokaci sosai kafin a kammala shi."

Dr Sufi ya ce a baya alamu sun nuna sosai cewa gwamnatin tarayya ta so yin aikin don har ta fara ɗaukar bayanai na biyan waɗanda za a rushewa gine-gine a wajen diyyarsu.

"Amma a yanzun ma bai ɓaci ba, gwamnatin jiha na iya farawa sai dai zai yi kyau su yi yarjejeniya da gwamnatin tarayya ta biya ta kuɗaɗen da ta kashe bayan kammala aikin.

"Don wadannan kuɗaɗe da za a kashe a kan gina gadar nan sun isa a yi wa Kano gagaruman ayyuka na ci gaba da dama waɗanda su ne al'umma suka fi buƙata da gaggawa," a cewar malamin.

Me masu suka ke cewa?

Tun kafin gwamnatin ta amince da gina wannan gada ta shataletalen Hotoro, wasu mutanen jihar na da ra'ayin cewa kamata ya yi gwamnatin ta mayar da hankali kan samar da ruwa da inganta harkar lafiya.

Nura Mustapha Wudil ma ya ce: "Raya zukatan ɗan Adam shi ne abin da ya kamata gwamnati ta mayar da hankali a kai.

"Babban tashin hankalin da muke fama a yau shi ne matsalar rashin tsaron da muke fama da shi, kuma raya zuƙatan al'umma ne ya haifar da hakan."

Usman Shagari ma cewa ya yi "gwamnati ya kamata ta gina mana irin katafaren gidan ruwa haka a Wudil, da an taimaki rayuwar jama'a".

A shafin Facebook ma mutane sun yi ta tofa albarkacin bakinsu.

Wani mai sharhi kuma malami a Jami'ar Cologne da ke Jamus, Muhsin Ibrahim, ya ce gina gadar ba shi ne abin da aka fi buƙata ba don al'ummar Kano sun fi buƙatar abubuwan da suka shafi inganta ilimi da harkar lafiya.

"Duk da cewa ina son ganin an ƙayata wurare domin hakan alamu ne na ci gaba, amma a ganinsa ba a zo wajen ba a buƙatun al'umma don samar da ilimi da ayyukan yi sun fi muhimmanci a yanzu," a cewarsa.

A shafin Twitter kuwa @Votehauwa ce ta ce: "Don Allah gwamna ka nemi ƙwararru su tsara maka shirin ci gaba ga jihar Kano

"Gina gadoji a inda harkar ilimi da lafiya ke buƙatar garanbawul ba abin da ya kamata ba ne. Na san mutanen da za su iya yin aikin tsara ci gaban nan ba tare da an biya su ko sisi ba."

Me gwamnati da masu goyon bayan gina gadar suka ce?

A sanarwar da gwamnatin Kanon ta fitar, ta ce aikin na daga cikin ƙudurorin gwamnatin Gwamna Ganduje na rage cunkoson ababen hawa a tsarinta na mayar da Kano hamshaƙin birni da kuma inganta harkokin kasuwanci.

"Idan ba a yi wurare irin wannan ba to za a samu ƙalubale," in ji Kwamishina Muhammad Garba.

Ya ci gaba da cewa: "A maganar ilimi gwamnati na bakin ƙoƙarinta na cewa za a ba da ilimi kyauta a matakin firamare da sakandare kuma Alhamdulillah ana gudanar da wannan tsari.

"Kuma a harkar lafiya ma gwamnati tana namijin ƙoƙari wajen gina asibitoci a yankunan masarautun da muke da su.

Wani Musbahu A Ahmad ya ce; "Ni dai ina goyon bayan gadar nan don wata rana ko lokacin azumi haka wallahi idan cunkoso ya rincaɓe sai mutum ya sha ruwa a wajen har sai a yi Sallar Asham, don haka ina goyon baya 100 bisa 100."

A Twitter kuwa @DgRaamp ne ya ce "Masha Allah. Ci gaba mai matuƙar kyau ga jihar Kano da al'ummarta. Allah Ya ja da ranka babanmu."

@ArcYuyu ma cewa ya yi: "A kan batun gina abubuwan more rayuwa, Ganduje ya yi zarra ta nan, kuma ba shi da mahaɗi a wannan lokacin. An gaishe ka."