Lafiya Zinariya: Illolin karancin jini a jikin mace mai ciki

Lafiya Zinariya: Illolin karancin jini a jikin mace mai ciki

Wasu daga cikin illolin da karancin jini ke haifarwa ga mace mai juna biyu sun hada da bari da haihuwa lokaci bai yi ba, ko mabiyiya ta rabu da jikin mahaifa da kuma ciwon zuciya.

Yayin da wannan matsala ta rashin isasshen jini kan shafi jaririn da ke ciki.

Yakan sanya jariri ya samu karancin nauyi, ko a haife shi bakwaini.

Yakan kuma janyo mutuwar dan tayi a ciki ko mutuwarsa jim kadan bayan haihuwa.