Usman Alkali Baba: Kalubale biyar da ke gaban sabon Sufeton ƴan sandan Najeriya

Mukaddashin sufeton 'yan sandan Najeriya DIG Usman Baba Alkali

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya nada DIG Usman Alkali Baba a zaman sabon Mukaddashin Babban Sufeton 'yan sandan kasar.

Sabon sufeton ya maye gurbin Mohammed Abubakar Adamu, wanda shekarunsa na ritaya suka cika a farkon wannan shekarar. Ministan harkokin 'yan sanda Maigari Dingyadi ya bayar da sanarwar ranar Talata.

Dama dai tsohon sufeton 'yan sandan Najeriyar Mohammed Adamu ya yi ritaya, amma a ranar 4 ga watan Fabrairun shekarar nan shugaba Buhari ya kara masa wa'adin wata uku, amma watanni biyu kawai ya yi aka nada sabon sufeton.

DIG Usman ya samu mukamin ne a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar kalubalen rashin tsaro a sassa daban-daban na kasar, kama daga satar mutane domin neman kudin fansa, da barayin shanu, da rikici tsakanin manoma da makiyaya da na baya-bayan nan wato hare-hare kan ofisoshin ƴan sanda a yankin kudu maso gabashin ƙasar.

Shin ko wadanne kalubale ne ke gaban sabon mukaddashin sufeton 'yan sandan Najeriyar?

BBC ta ji ta bakin Malam Kabiru Adamu mai sharhi a kan lamuran tsaro a Najeriya da yankin Sahel, kuma shugaban kamfanin Bicon Consultancy, inda ya zayyana ƙalubale biyar da ke gaban Usman Baba.

1. Gyara alaƙar ƴan sanda da al'umma

Gyara rashin yarda tsakanin al'umma da jami'an 'yan sanda, wanda yana da nasaba da abubuwa da yawa da suka faru a baya saboda an wayi gari al'umma ba su yarda da jami'an tsaro ba musamman 'yan sanda.

Kuma gyaran wannan yana bukatar jajircewa da ya kamata shi IG zai yi. Dole ya yi kokarin gyara aikin 'yan sanda domin su fahimci aikin da suke yi domin jama'a suke yi ba domin su muzguna musu ba.

Idan ba a manta ba a shekarar da ta gabata wasu 'yan Najeriya sun fito domin nuna fushinsu kan cin zarafin da rundunar 'yan sanda mai yaki da fashi da makamai da muggan laifuka wato SARS ke yi wa jama'a.

2. Inganta rayuwar jami'an ƴan sanda

Sai kuma gyara ainahin yanayin da 'yan sanda ke aiki a ciki, inda ya kunshi gyara musu albashi, da muhalli, da alawus, da ba su cikakken horo, saboda 'yan sanda na cikin wani yanayi maras kyawu sakamakon rashin abubuwan da suke bukata.

Ana ganin hakan na daga cikin dalilan da ke tunzura su shiga wasu ayyuka da ba su dace ba. Idan ana son 'yan sanda su yi aiki yadda ya dace dole a inganta musu rayuwa.

Bai wa 'yan sanda horon sanin makamar aiki, yin amfani da kudin da ke cikin asusun da gwamnatin tarayya ta kafa na Police Trust Fund, wanda daman an kafa shi ne domin amfani da kudin wajen sayen makamai da walwalar 'yan sanda da kuma ba su horo.

Wannan zai taimaka matuka wajen tabbatar da cewa sun ƙware a fannin aikinsu yadda ya kamata. Dole a sauya salon yadda ake daukar ma'aikatan ƴan sanda aiki da magance rashin hadin kan da ke tsakaninsu.

4. Dawo da martabar ƴan sanda

Dawo da martabar 'yan sanda ta yadda za su karbi aiki kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, wato ba da tsaro na cikin gida.

An wayi gari a yanzu kusan sojoji ke aikin 'yan sanda a jihohin Najeriya. Domin haka sabon mukaddashin sufeton 'yan sanda na bukatar ya dawo musu da martabarsu wajen gudanar da ayyukan da dama can nauyin yinsu ya rataya ne a wuyan ƴan sandan.

Mai do da martabarsu zai sa ita kanta gwamnati za ta samu karfin gwiwar bar musu aikin ba tare da an sake sanya sojoji cikin lamarin ba.

Samar da makaman zamani da kundin tattara bayanai na zamani, da samar da dakunan adana bayanai, da rashin tsare mai laifi na dogon lokaci.

5. Samar da isassun jami'an ƴan sanda

Samar da isassun ma'aikata karkashin hukumar 'yan sanda, saboda akwai bangarori da dama a Najeriya da ke aikin 'yan sanda amma kuma aikin 'yan sanda suke yi.

Misali hukumar kare hadurra ta kasa wato Road Safety, kowa ya san aikin da suke yi 'yan sanda ne ya kamata su yi shi, akwai kuma Civil Defence su ma kamata ya yi a ce suna karkashin ma'aikatar 'yan sanda.

Don haka babban kalubalen da ke gabansa shi ne ya hade kan hukumomin tsaro domin aiki tare da samar da tsaron cikin gida yadda ya kamata.

A karshe Kabiru Adamu ya ce matukar aka hada kan jami'an tsaro da dinke barakar da ke tsakaninsu babban makami ne na samar da rundunar tsaro mai karfi.

Amfani da ma'aikatan da ake da su domin cimma tsaron cikin gida da tsare kasa baki daya ƙasa shi ne abin da 'yan Najeriya ke da buri da kuma fatan ganin sabon mukaddashin sufeton 'yan sandan zai yi tsayuwar daka wajen magancewa.