Ordinary President: Mai shirin Brekete Family Ahmed Isah na shan yabo da suka ga ƴan Najeriya

Ahmed Isah
Bayanan hoto, An ga Ahmed Isa yana zabga wa wata mace mari a bidiyon binciken BBC bayan an zarge ta da ƙona wata yarinya a ka

Binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye kan shirin Brekete Family ya ja hankalin ƴan Najeriya inda suka bayyana ra'ayoyi mabambanta kan wani ɓangare game da shirin da binciken ya gano.

Ahmed Isah, mai rajin kare haƙƙi a Najeriya da ke taimaka wa mutane wajen neman haƙƙinsu a rediyo da talabijin, ya sha yabo da suka sakamakon bidiyon BBC da ya nuna shi yana marin wata mace.

Ahmed wanda aka fi sani da 'Ordinary President' wato jagoran talakawa, ya shahara ne sakamakon shirin da yake gabatarwa mai suna "Berekete Family" a gidan rediyon Human Rights Radio da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

An gan shi yana zabga wa wata mace mari cikin wani bidiyon binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye, wadda aka zarga da cinna wa wata ƙaramar yarinya wuta a kanta bisa zargin cewa mayya ce yayin da yake tsaka da gabatar da shirin.

Ya zuwa yanzu, Ordinary President bai mayar da martani ba game da abin da aka gan shi yana aikatawa bayan sakin bidiyon.

Tun bayan wallafa bidiyon ne 'yan Najeriya suka dinga bayyana mabambantan ra'ayoyi, inda wasu ke ganin a matsayinsa mai kare haƙƙi bai kamata ya ci zarafin wani ba, wasu kuma na cewa "ta cancanci fiye da haka".

Bayanan bidiyo, Binciken Africa Eye kan shirin Berekete Family

Abin da 'yan Najeriya ke cewa

Tun farko, da BBC ta tambayi Ahmed Isah dalilin da ya sa ya mari matar yayin da ake ɗaukarsa a bidiyo, sai ya ce: "Na yi hakan ne domin na yi amfani da bidiyon da zummar koya wa mutane darasi".

Sai dai batun ya raba kan dubban 'yan Najeriya inda suka bayyana ra'ayoyi masu karo da juna a Twitter.

An yi amfani da 'Ordinary President' sau 17,500 ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, an kuma yi amfani da 'Ahmed Isah' sau 3,448.

"Ordinary President ya yi daidai. Ni kaina wallahi haka zan yi," a cewar wata mai suna petty patootie (@neptracy).

Kauce wa Twitter, 1
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1

Shi kuwa wani mai suna iamRainOver 1 Billionaire (@RainSegzy) cewa ya yi: "Kamata ya yi mu mayar da hankali kan yarinyar da abin ya shafa, ba wai mu goyi bayan abin da Ordinary President ya aikata ba."

Kauce wa Twitter, 2
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 2

Ita ma Gbemisola @gbemy01 cewa ta yi: "Waɗanda ke ganin marin bai dace ba ya kamata su ma su ƙona kansu."

Kauce wa Twitter, 3
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 3

Ramadan (@successfulaboki) ya ce: Na shafe shekaru ina bin ayyukan Ordinary President...Abu ɗaya da zan faɗa game da shi shi ne, lallai ya kamata ya gyara halinsa na fushi. Gaba ɗaya dai, mutumin kirki ne."

Kauce wa Twitter, 4
Ya kamata a bar bayanan Twitter?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 4

Abin da ake zargin matar da aikatawa

Kamar yadda bidiyon ya nuna, an kawo yarinyar ce 'yar shekara shida cikin zauren gabatar da shairye-shiryen na Brekete Family bisa zargin cewa wata 'yar uwar mahaifinta ce ta saka kalanzir kuma ta kunna mata wuta a kai.

Nan take Ahmed Isah ya kira kwamishinan 'yan sanda na birnin Abuja kuma cikin ƙasa da awa ɗaya suka isa wurin. Kazalika, ya yi alƙawarin ba ta tallafin kusan naira miliyan biyu.

Bayan bincike, an kama wadda ake zargin.

Ordinary President ya nemi a kawo matar domin yi mata tambayoyi. Sai dai ganin cewa ta kasa amsa masa tambayoyin game da dalilin da ya sa ta aikata abin da ake zarginta da shi, sai ya zazzabga mata mari fiye da sau ɗaya.

Kamar yadda rahoton ya nuna, yarinyar na ci gaba da samun kulawar likitoci a asibiti bisa tallafin kuɗin da Ordinary President ya tara mata, wanda da ma abin da yake yi kenan a cikin shirin nasa na Brekete Family.