'Suna kashe mu saboda mu 'yan Shi'a ne'

  • Daga Swaminathan Natarajan da Inayatulhaq Yasini
  • BBC World Service
Roshan Ghanznawi.

Asalin hoton, Roshan Ghaznawi

"An shafe shekaru ana kai mana farmaki.''

Lokacin da bama-namai uku suka fashe a unguwar su Roshan a farkon wannan watan tare da halaka mutum 85, ta tabbatar cewa saboda nuna wariya ne ya sa al'ummarsu suka shafe shekaru suna shan wahala.

Roshan 'yar Hazara ce, kabilar da ta kunshi kashi 15 zuwa 20 na yawan al'ummar of the Afghanistan, amma wadanda kamannin su na yankin Tsakiyar Asiya ya banbanta su da akasarin sauran 'yan kasar ta Afghanistab, haka ma addinin su.

Kasancewar akasarin 'yan kabilar Hazara mabiya Shia ne ya sa suke fama da hare-haren 'yan Sunni masu tsattauran ra'ayin addinin Islama.

Mai rajin kare hakkin biladama da ke fafutikar 'yancin samun ilimi, ta shaida wa BBC game da yadda ta kubuta daga hare-haren bama-bamai uku da aka kai a wurare daban-daban, kuma cin zarafin nuna wariya da ta ke fuskanta ita da al'ummar ta a kullum.

"Mun fita daban, kuma hakan ne ya sa wasu ke saurin gane mu, su ci zarafin mu, su kai mana hari,'' in ji Roshan Ghaznawi.

Hare-haren bama-bamai a makaranta

Asalin hoton, Getty Images

Hare-haren ranar 8 ga watan Mayu ya fada kan makarantar sakandare a yankinsu na Hazara a Kabul babban birnin kasar Afghanistan, tare da hallaka dalibai 'yan mata.

Fashewar bama-baman sun faru ne a unguwarta, Dasht-e-Barchi, kuma ba tare da ɓata lokaci ba Roshan ta je asibiti don duba wadanda suka jikkata.

"Abin bakin ciki ne a duk lokacin da aka kai hari kan ƙananan yara da ɗalibai da gangan.

"Hari ne na rashin tausayi da Imani,'' Roshan ta shaida wa BBC.

Ta gigice a lokacin da ta gane wa idanunta yadda 'yan mata da dama ke tare da litattafansu har a kan gadajen asibiti.

A matsayinta na wacce ita ce ta farko da ta kammala karatun jami'a a cikin iyalansu, Roshan ta san irin wahalar da 'yan mata ke sha wajen samun damar ilimi.

"Wata yarinya wacce ta rasa abokan karatunta da dama na ta kuka sosai. Amma duk da haka ta fada min cewa za ta sake komawa makaranta da zarar ta samu dama,'' in ji Roshan.

Asalin hoton, Getty Images

Babu wanda ya fito ya yi ikirarin kai harin; Jami'an gwamnatin Afghanistan sun dora alhakin faruwar hakan a kan maakan Taliban, amma kuma kungiyar ta musanta hannu a kai.

Mayakan Sunni kamar Kungiyar Kasar Musulunci (IS) na daukar 'yan kabilar Hazara a matsayin 'yan bidi'a, kuma sun sha ƙaddamar da munanan hare-hare da kashe-kashe a kansu.

Shekara daya cif kenan, da aka kai hari kan sashen masu haihuwa a asibitin yankin, tare da hallaka mata da jarirai 24.

An kai sauran wasu hare-hare, kuma duka a lokacin Roshan tana wurin da aka ƙaddamar da uku daga cikinsu.

Jajircewa

Matan Afghanistan kasa da kashi 30 bisa dari ne ke iya karatu da rubutu, kuma an dade da haramta wa mata damar samun ilimi, musamman lokacin da kungiyar Taliban ke riƙe da ikon kasar (shekarar 1996 zuwa 2001).

Babu makarantu da kayan karatu wadatattu, an fi bai wa 'ya'ya maza fifiko yayin da batun haramta wa 'ya'ya mata samun damar ilimi ya ƙara ƙaruwa.

Asalin hoton, Roshan Ghanznaw

Tashin hankalin ya ƙara zama wani babban cikas ga 'ya'ya mata.

"Yan matan na karatu a waje, a cikin wata rumfa ko kuma a sarari, kuma makarantar makare take da dalibai.

Babu abubuwa kamar su wuraren ba-haya, da dakunan karatu da ajiyar litattafai, kana suna fuskantar matsaloli a wajen makarantar in ji Barr.

Jajircewar 'yan matan ce da kuma fatan da iyayen ke da shi na fita daga kangin talauci ya sa al'amura ke tafiya a makarantar.

Wurin da bai dace ba, a lokacin da bai dace ba

Asalin hoton, Getty Images

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wannan ba shi ne karon farko da aka taba kai harin bama-bamai a makaranta da Roshan ta shaida abubuwan da suka biyo baya na ayyukan mugunta ba.

A ranar 16 ga watan Nuwambar shekarar 2014, ta tsallake rijiya da baya a wani harin ƙunar bakin wake da aka kai kan kwambar motocin wata 'yar majalisar dokoki Shukria Barakzai.

Roshan na tafiya zuwa jami'a a wannan ranar, kuma ta lura da wata yarinya da ta yi mata murmushi.

Cikin kasa da minti daya bayan nan ne ta ji wata babbar kara kuma a lokacin da ta juya sai ta ga wani mummunan al'amari.

Barakzai ta tsira da ranta bayan da ta samu raunuka kadan, amma mutane uku da suka hada da wannan karamar yarinya sun mutu nan take.

Sai bayan kai harin ne Roshan ta gano sunanta.

"Jikin Kutzia ya rabu gida biyu. Daya bangaren ya fada can a gefen titi. Ban iya zuwa jami'a ba a cikin wannan mako, na yi ta rusa kuka.''

Roshan na da shekara 20 a wancan lokacin, kuma tana aiki da kungiyoyi masu zaman kansu da ke fafitikar samar wa da 'ya'ya mata 'yancin samun ilimi.

Ta rarraba litattafai da sauran kayayyaki kana ta fara bayyana a kafar talabijin tana magana a kan ilimi da bukatun al'ummarta.

Nuna ƙiyayya a fili

Asalin hoton, Roshan Ghanznawi

Roshan ta san wahalar da ke tattare da 'yan matan Hazara ta samun karya lagon haramcin da ake yi musu na zuwa makaranta.

Ba ta fara makaranta a kan lokaci ba - iyayenta talakawa ne kuma masu sana'ar saƙa ne marasa ilimi da ba su bai wa ilimin 'ya'ya mata fifiko ba.

A matsayinta na babbar 'ya a cikin 'ya'ya biyar, Roshan ta fara saƙa dardumomi a gida kafin ma ta fara koyon rubuta harafi.

Ta yi karatu tuƙuru kuma ta burge malamanta. Ba ta kai shekara 10 ba a lokacin da ta fara fuskantar tsangwama ta nuna wariya a karon farko.

"Wata yarinya ta ce, 'Ku leburori ne. Ku ƙazaman mutane ne,'' Roshan ta tuna. Ta wuce gida tana rusa kuka.

'Coolie' wata kalma ce ta nuna wariya da ke bayyana mutanen da ke aikin ƙarfi na wadanda ba su da ilimi.

Roshan ta girgiza ƙwarai kan wulakancin da aka yi mata, amma duk da haka nuna wariyar ta ci gaba da faruwa har a lokacin da take karatun lauya a jami'a.

"Wasu samari suka fara zagina. Sun daka min tsawa, 'ke mai cin naman ɓera, me kike yi a cikin jami'a?'"

Rashin gane gangar jiki

Asalin hoton, Getty Images

A shekarun baya-bayan nan, nuna wariya ga 'yan kabilar Hazara ta juye ta zama cin zarafi a fili.

Masu gwagwarmaya da makamai kan riƙa kai har ikan taron jama'a suna haddasa mutuwar mutane da dama, kuma taron zanga-zanga ya zama abu mafi sauki a gare su.

A shekarar 2016, al'ummar Hazara suka fara wata gagarumar zanga-zanga don bukatar wutar lantarki a gidajensu.

Zanga-zangar birnin Kabul ce da Roshan ta samu kanta cikin harin bam na biyu.

"Na tuna ganin wani kyakkyawan aboki a cikin taro. Mun wayi juna a jami'a.''

Roshan ta ce ta ji a wani mummunan yanayi a jikinta cewa wani abu zai faru da abokinta.

Yayin da zanga-zangar ta soma kankama, wata babbar fashewa ta faru a tsakiyar taron, tare da hallaka mutane 100.

Gashin Roshan ya kama da wuta ya ƙone. Ta ji jikinta ya mutu ta kuma kasa gane me yake faruwa.

Ƙawaye da abokan karatu da Roshan ta yi magana da su suka yi musayar litattafai sun hallaka. Kyakkyawan abokin da ta sani na kusa da inda bam din ya tashi.

"Ba a iya gane gangar jikinsa. Fuskarsa ta lalace gaba daya. Mahaifiyarsa ta gane gawarsa ta hanyar wata alama a tafin ƙafarsa da kuma agogonsa.''

Ƙarfin hali

Asalin hoton, Roshan Ghanznawi

Roshan ta ce waɗannan hare-hare ba su sanyaya gwiwar al'ummarta wajen ƙoƙarin inganta harkar ilimi da rayuwarsu ba.

Ta ce cikin shekaru 20 da suka gabata, mutane da dama daga cikin al'ummarta sun samu ilimi, kuma sun fita daga ƙangin aikin leburanci da aikatau a gidaje sun zama lauyoyi da malaman makaranta da sauransu.

Ta yi amanna cewa hadin kai yana da matuƙar muhimmanci wajen kawo ƙarshen cin zarafi da nuna wariya da al'umarta ke fuskanta, kana ta ce ta san cewa kowa yana yi musu kallon raini.

"Na kan ke kauwanni, da gidajen cin abinci, da wuraren bukukuwan al'adu, da jami'a a matsayin mai alfahari da ƙabilar Hazara.

Manyan aminaina su ne 'yan kabilar Pashtun da Tajik. Babu wani rashin jituwa a tsakaninmu.''

A kusa da gida

Asalin hoton, Roshan Ghanznawi

Daya harin da aka kara kai wanda Roshan ta samu kanta ciki ya faru ne a shekarar 2019, kuma a kusa da gidansu ne.

"Harin bam din an kai kan wata makaranta a yankin Hazara kusa da gidanmu. A wannan hari, na kusa rasa ƙanwata,'' ta ce.

Jim kadan bayan kanwar Rosha Parwana ta fita daga cikin gida zuwa makaranta, wata ƙarar fashewa ya girgiza gidanmu.

Roshan ta ji tsikar jikinta ta tashi. Fargabar mummunan al'amari, mahaifiyarta ta fita hayyacinta.

Tafiyar minti uku ce daga gidan zuwa cikin makarantar kuma fashewar ta faru a kan hanyar ne.

Yayin da ta bude kofar gidan, Roshan ta hangi gawawwakin ƙananan yara da iyayensu mata a kan tituna.

"Ƙanwata na ƙarƙashin tarin gawawwakin. Jinin mutane ya rufe fuskarta. Tana gaba na amma na kasa gane ta.''

Parwana ta shiga halin dimauta amma ba ta samu raunuka ba. Kusan kasha 60 bisa dari na mutanen sun mutu a harin bam din.

Asalin hoton, Roshan Ghanznawi

Amincewa

Asalin hoton, Roshan Ghanznawi

Gagarumar tattaunawa tsakanin gwamnatin Afghanistan da kungiyar Taliban har yanzu ba ta taɓo batun ƙabilu 'yan tsiraru ba, amma Roshan na son gwamnati ta tsaurara matakan tsaro a yankin Hazara ba tare da jinkiri ba, don dakatar da sake kai hare-hare.

Tana cike da fatan ganin ranar da ko wace al'umma za ta kasance cikin kwanciyar hankali a Afghanistan, amma tana ta ƙoƙarin nuna yaƙinin ta - a wasu lokuta ta kan yi wasu-wasi game da barin kasar gaba daya.

"Ba na son in haifi yara a inda za su riƙa fuskantar hare-haren bama-bamai da harsasai a kullum,'' ta ce.

Tana fargabar cewa me yiwuwa ta riga ta saba da tashin hankali, kuma ta soma amincewa da yanayin.

"Bayan shaida irin wadannan kashe-kashe akai-akai, na soma sabawa da su,'' ta ce.

"A wasu lokutan ma ba na jin wata damuwa.''