Rikicin Isra'ila da Falasdinu: Rayuwa a Zirin Gaza

Bread seller on Gaza City on 19 May

Asalin hoton, Getty Images

Birnin Gaza wanda ke da yawan al'umma kusan miliyan biyu, yana da tsawon kilomita 41 ko kuma mil 25, da kuma fadin kilomita 10, yankin da ke kewaye da tekun Bahr Rum, da kasashen Isra'ila da Masar.

Rikici tsakanin Gaza da Isra'ila a baya-bayan nan ya kazanta zuwa mummunan tashin hankali da hakan ya sa Majalisar Dinkin Duniya yin gargadi na "gagarumin yaki".

Gaza wanda tun asali kasar Masar ce ta mamaye, kasar Isra'ila ce ta kame yankin a lokacin yakin Gabas ta Tsakiya a shekarar 1967.

Isra'ila ta janye dakarunta da 'yan kasarta mazauna yankin 7,000 a shekarar 2005.

Yankin ya kasance karkashin ikon kungiyar Hamsa ta mayaka masu kaifin kishin Islama, wacce ta fatattaki dakarun da ke goyon bayan hukumar Falasdinu (PA) a wancan lokacin, bayan rikicin shekarar 2007.

Tun daga wannan lokaci, kasashen Isra'ila da Masar suka takaita kai-komon jama'a da kaya zuwa ciki da waje, a wani abu da suka bayyana da daukar matakai kan mayakan.

Kungiyar Hamas da Isra'ila sun gwabza fada takaitacce a shekarar 2014, kana a shekarar 2021 fadan ya sake rincabewa.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An lalata gine-gine da dama a rikicin na kwanan nan

Shin menene ya rura wutar rikicin?

Rikicin Gaza ya fara ne bayan shafe makonni ana fito-na-fito a yankin Gabashin Kudus da ya rikide ya zama mummunar arangama a masallaci al'Aƙsa wanda Musulmai da Yahudawa ke darajtawa.

A ranar 10 ga watan Mayu kingiyar Hamas ta fara harba rokoki bayan da ta gargadi Isra'ila da ta janye daga wurin, wanda ya haifar da hare-hare ta saman a mayar da martani.

Musayar hare-haren sun kara zafafa inda ba tare da bata lokaci ba rikicin ya kara zama mafi muni da aka taba samu tsakanin Isra'ilar da Gaza tun bayan na shekarar 2014.

Rokoki sun lalata hanyoyin wutar lantarki

Daukewar wutar lantarki ya zama ruwan dare a Gaza. Kafin karuwar rikicin baya-bayan, gidaje a Gaza na samun wutar lantarki da ake jujjuyawa na sa'oi takwas-takwas.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Dauke wutar lantarki ya zama ruwan dare a Gaza

Tashin hankalin baya-bayan nan ya lalata hanyoyin wutar lantarki tare da haifar da koma bayan samun man fetur. Kamar yadda ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai lura da agajin jin ka (Ocha) ya bayyana, akasarin gidaje yanzu suna samun wutar lantarki na tsawon sa'oi uku zuwa hudu ne kacal a ko wace rana.

Zirin na samun akasarin wutar lantarkinsa ne daga Isra'ila tare da karin gudumawar tashar samar da wutar lantarki daya kadai da ake da ita a Gaza da kuma kadan daga kasar Masar.

Duka tashar samar da wutar lantarkin Gaza (GPP) da kuma injinan janareto na mutane da dama sun dogara ne ga man inji, amma kuma an toshe hanyar samar da shi daga Isra'ila, da hakan ya haifar da karin damuwa.

Rufe tsallaken kan iyakoki

Tun bayan da kungiyar Hamsa ta karbe iko a Gaza a shekarar 2007, kasar Masar ta rufe kan iyakarta da Gaza.

A shekarar da ta gabata aka kara tsaurara maakai don kokarin hada yaduwar cutar korona.

An rufe duka tsallaken Rafah zuwa cikin kasar Masar da tsallaken Erez zuwa cikin kasar Isra'ila a cikin kwanaki 240 kana a bude a cikin kwanaki 125 a shekarar 2020, kamar yadda kididdigar hukumar Ocha ta nuna.

Asalin hoton, AFP/Getty

Bayanan hoto,

Masar ta rufe iyakarta da Gaza a rufe tun shekarar 2007

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A shekarar 2019 mutane kusan dubu saba'in da takwas (78,000) ne suka fice daga Gaza ta cikin kan tsallaken Rafah amma a shekarar 2020 hakan ya ragu zuwa dubu ashirin da biyar (25,000).

A arewaci, tsallaken zuwa cikin Isra'ila a Erez shi ma ya ragu sosai a shekarar 2020 - saboda dokokin annobar korona.

A cikin wannan shekarar mutane kusan dubu takwas (8,000) ne suka fice daga Gaza ta cikin tsallaken Erez, akasari marasa lafiya ko kuma mutanen da ke musu rakiya ne zuwa neman magani a Isra'ila.

Kafin tashin hankalin baya-bayan nan, an soma samun zirga-zirgar ababan hawa. Wasu kwambar motocin masu abayar da agaji tuni aka amince su wuce, amma in baya ga haka duka tsallaken na cigaba da kasancewa a rufe.

Ana kai farmaki kan hanyoyin karkashin kasa

Kusan kasha tamanin bisa dari (80%) na yawan al'ummar Gaza sun dogara ne ga agajin da suke samu daga kasashen waje, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana, kana mutane kusan miliyan daya ne suka dogara da abincin agajin da suke samu a kullum.

Rufe kan iyakokin da Isra'ila ta yi ya yi mummunan tasiri kan zirga-zirga a ciki da wajen Zirin da kuma harkokin cinikayya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An gina ramuka a ƙarƙashin iyakar Masar don shiga da kayayyaki da makamai

Kungiyar Hamsa ta gina hanyoyin karkashin kasa don kokarin wucewa, wanda ta ke amfani da su wajen shigo da kaya cikin Zirin kana a matsayin cibiyar gudanar da ayyukan sojin ta na karkashin kasa.

Isra'ila ta ce su ma hanyoyin karkashin kasar mayakan na amfani da su ne wajen yin bad-da-sawu kuma ana kai musu hare-hare ta sama.

Ita ma cutar korona ta yi mummunan tasiri kan tattalin arzikin yankin, amma yanzu y afara nuna alamun farfadowa, kamar yadda Bankin Duniya ya bayyana a lokacin da fadan ya barke.

Cunkuso da kuma lalatattun gidaje

Gaza na da yawan cunkoson jama'a mafi girma a duniya.

Kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana, 'yan gudun hijira kusan dubu dari shida (600,000) a Gaza na zaune ne a sansanoni takwas masu cunkoso.

A tsaka-tsaki dai akwai mutane fiye da dubu biyar da dari bakwai (5,700) a ko wane fadin murabba'in kilomita - iri daya da na yawan al'umma a birnin London - amma kuma wannan adadi ya karu da fiye da dubu tara (9,000) a birnin Gaza.

Isra'ila ta ayyana yankunan tudun mun tsira a kusa da kan iyaka a shekarar 2014 don kare kan ta daga hare-haren rokoki da kutsen masu tayar da kayar baya. Yankin ya rage yawan filin da ake da shi wanda mutane za su iya zama ko su yi noma a kai.

Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa an lalata ko kuma rushe gidaje kusan dubu dari da arba'in(140,000) a tashin hankalin shekarar 2014, kuma tuni ta tallafa wa iyalai kusan dubu casa'in (90,000don su sake gina gidajensu.

OCHA ta ce daruruwan gidaje ne suka lalace a fadan baya-bayan nan, amma zai dauki lokaci kafin a iya tantance takamaimen yawan asarar da aka tafka.

Cibiyoyin kiwon lafiya sun cunkushe

Bangaren kiwon laifya a Gaza na cikin matsanancin hali saboda dalilai da dama. OCHA ta bayyana cewa rufe hanyoyin da Isra'ila da Masar suka yi ya haifar da tsaiko wajen samun kayan kiwon lafiya daga Gabar Yamma ta Kogin Jordan, da kuma rikicin siyasar cikin gida tsakanin hukumonin Falasdinu - wanda ke da daukar nauyin samar da kiwon lafiya a yankunan Falasdinawa - kana dole a dora alhakin duka a kan kungiyar Hamas.

Majalisar Dinkin Duniya ta taimaka ta hanyar kafa cibiyoyin kiwon lafiya 22. Amma adadin asibitocin da dakunan shan magani sun lalace ko kuma rushe a lokacin rikicin baya-bayan nan da Isra'ila.

Asalin hoton, Reuters

Marasa lafiya daga Gaza da ke bukatar taimako a Gabar Yamma ta Kogin Jordan ko asibitocin Gabashin Kudus dole su fara samun amincewar bukatun na su daga hukumar ta Falasdinu (PA) da kuma takardar izinin shiga daga gwamnatin Isra'ila - a shekarar 2019, yawan adadin takardun amincewar ga marasa lafiya na su fita daga Zirin Gaza kashi 65 bisa dari (65%) ne.

Cikin watannin kadan da suka gabata, halin da aka shiga da kiwon lafiya ya kara ta'azzara ne saboda annobar korona.

A cikin watan Afrilu, an samu karuwar matsalar kusa 3,000 a rana a Gaza. An samu mutanen da suka kamu da cutar fiye da dubu daru da arba'in (104,000) tun bayan barkewar annobar, kana mutane fiye da dari tara da arba'in da shida (946) ne suka mutu da cutar.

Kungiyar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargadin cewa tsaurara rufe kan iyakokin ba sun takaita ne kawai ga hada samun kiwon lafiyar ceton rayuka bane ga wadanda rikicin ya rutsa da su, amma suna haifar da koma-baya na kokarin yaki da cutar korona.

WHO din ta ce yana shafar ''muhimman'' shirye-shiryen bayar da allurar riga-kafi kana yana kara haifar da barazanar yaduwar cutar yayin da mutane ke neman mafaka a wurin 'yanuwa ko kuma matsugunai na gaggawa.

Cikas ga kwambar motocin abincin agaji

Mutane fiye da miliyan daya ne a Gaza aka kasafta a matsayin ''matsakaita zuwa masu matsanancin bukatar abinci'', kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana, duk da cewa da dama suna samun agajin abinci.

An bude tsallaken kan iyakoki don barin kwambar motocin abincin agaji shiga, amma kuma lugudan wuta ya haddasa tsaikon rarraba kayyakin.

Dokokin da Isra'ila ta tsaurara kan samun filayen noma da kamun kifi sun rage yawan abincin da 'yan Gaza ke samar wa kan su.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Iyalai da yawa na rayuwa ne a sansanonin 'yan gudun hijira

Ba a amince musu yin noma a yankin da Isra'ila ta ayyana a matsayin tudun-mun-tsira ba - mai fadin kilomita 1.5 ko kuma mil tara (0.9) a bangaren kan iyakar Gaza - kana hakan ya haddasa karancin samar da abincin da aka kiyasata tan dubu saba'in da bakwai (75,000) na amfanin gonar da ake nomawa a ko wace shekara.

Isra'ila ta kafa dokar takaita kamun kifi da hakan ke nufin 'yan Gaza za su iya yin kamun kifin ne kawai a wasu wurare masu nis ana bakin tekun.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce idan aka cire takunkumin, kamun kifin zai samar da ayyukan yi da kuma hanyoyi mafi sauki na samun abinci mai gina jiki ga mutanen Gaza.

Bayan karuwar tashin hankalin baya-bayan nan, Isra'ila ta haramta kamun kifi a Zirin Gaza na wucin gadi. A cikin shekarun baya ta kafa dokoki da dama kan wuraren kamun kifi, da ya haifar da cikas ga hanyoyin samun kudaden shiga masunta kusan dubu biyar da kuma masu sana'oi makamantan haka.

Karancin ruwan sha ya zama ruwan dare

Mutane da dama a Gaza na fama da matsalar karancin ruwan sha. Ruwan famfo ya kasance da dandanon gishiri kuma gurbatacce, bai dace a sha ba.

Asalin hoton, Reuters

Yayin da akasarin gidajen Gaza ke kan bututun samar da ruwan sha, Ocha ta ce iyalai kan samu ruwan famfon na sa'oi shida zuwa takwas ne a ko wane kwanaki hudu a shekarar 2017 saboda karancin wutar lantarko.

Hakan ya sake raguwa saboda hare-haren baya-bayan nan.

Kungiyar Lafiya ta Duniya ta tsara adadin ruwan shan da ake bukata a rana a kan lita dari kan ko wane mutum - don samun na sha, da wanki, da wanka, da kuma na girki.

A gaza akan samu kusan litoci 88 na bukatar ruwan shan.

Hanyoyin magudanar gurbataccen ruwa da ba-haya babbar matsala ce.

Duk da cewa kashi 78 bisa dari (78%) na gidajen jama'a suna hade da bututan magudanar gurbataccen ruwan da ba-baya, matatar ruwan ta gajiya. Ocha ta ce ana tace fiye da lita miliyan dari na gurbataccen ruwan da ake tur awa cikin tekun Bahar Rum a kullum.

Sabuwar atatar ruwan ta fara aiki ne a farkon shekarar 2021 don taimakawa wajen shawo kan matsalar.

Amfani da makarantu a matsayin matsugunai

Kananan yara da dama na zuwa makarantun da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa, kuma akasarin su na zama a matsayin matsugunai ga mutanen da suka tsere daga lugudan wutar da ake yi.

Kamar yadda hukumar lura da 'yan gudun hijira ta Falasdinu ta bayyana, kashi 64 bisa dar (64%) na makarantun ta 275 na bin tsarin karba-karba ne, akwai lokacin karatun safe, akwai kuma na yamma.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mutane da yawa na neman mafaka a makarantun MDD daga luguden wuta

Azuzuwan kan dauki adadin dalibai 41 ko wanne a shekarar 2019.

Adadin dalibai daga shekara 15 zuwa 19 da ke karatu yanzu kashi casa'in da tara (99%)- ya karu sosai ne a cikin shekaru kadan da suka gabata.

Rashin aikin yi a tsakanin matasa ya karu

Gaza na da mafi yawan adadin matasa a duniya, da kusan kasha sittin da biyar bisa dari (65%) na yawan al'umma kasa da shekara 25, kamar yadda binciken hukumar CIA yan una.

Matasa da dama ba su da aikin yi.

Wani rahoton hukumar OCHA daga shekarar 2020 ya ce rashin aikin yi a tsakanin matasan ya kai kashi 70 bisa dari (70%), saboda annobar korona.