Rikicin Isra'ila da Gaza: Labarin yaran Falasdinawa da suka mutu a rikicin

  • Daga Jack Hunter
  • BBC News
A child walks through rubble in Gaza

Asalin hoton, Anadolu Agency

Bayanan hoto,

Yara 61 aka ba da rahoton cewa sun mutu a Gaza, biyu kuma a Isra'ila

A cikin mutum 219 da aka kashe a Gaza, a kalla 63 daga ciki ƙananan yara ne, kamar yadda ma'aikatar lafiyarta wacce mayaƙa masu gwagwarmaya da makamai ke riƙe da iko.

A cikin mutum 10 da aka kashe a Isra'ila, ƙananan yara biyu na cikin waɗanda suka mutu, in ji ma'aikatar lafiya ta kasar.

Ga labaran wasu daga cikin yaran da aka hallaka.

'Ya'yan iyalan al-Kawalek, masu shekaru 5 zuwa 17

Asalin hoton, Al-Kawlak family/DCIP/NRC

Bayanan hoto,

Yara mai shekara tara daga hagu da Rula mai shekara biyar daga dama an kashe su tare da dukkan iyayensu a ranar Lahadi

Lokacin da harin Isra'ila ya fada kan titin al-Wihda a tsakiyar birnin Gaza a ranar Lahadi, iyalan al-Kawalek a kalla 13 ne aka yi amanna sun hallaka, bayan da ɓaraguzan ginin gidansu ya binne su.

Akasarin wadanda harin ya rutsa da su kananan yara ne daga watanni shida.

''Babu abin da muka riƙa gani sai hayaƙi," daya daga cikin iyalan da ta tsira da ranta, Sanaa al-Kawalek, ta shaida wa kafar yada labarai ta yanar gizo Felesteen Online.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

"Ina iya ganin ɗana a kusa da ni kuma ina rungume da shi, amma ba na iya ganin komai.''

Dakarun tsaron Isra'ila (IDF) sun bayyana harin bam ɗin a matsayin ''ba dai-dai ba'' kuma ba da gangan ne suka haddasa asarar rayukan fararen hula ba.

Mai magana da yawaun rundunar ya ce hare-hare ta sama ya haddasa ruftawar hanyoyin ƙarƙashin ƙasa, da kuma suka haddasa rugujewar gidaje a kansu.

Cikin wadanda suka hallaka akwai 'yan uwan juna, Yara mai shekaru 9, da Rula mai shekaru 5. Dukannin su sai da aka duba lafiyarsu a asibitin Hukumar Lura da ƴan gudun Hijira ta kasar Norway (NRC).

'Ya'yan na al-Kawalek masu ladabi ne da a ko da yause sukan kammala aikin makarantar da aka ba su a kan lokaci, daya daga cikin malamansu da bai amince a bayyana sunansa ba ya shaida wa BBC.

Wani hoto da yake mamaye shafukan yanar gizo ya nuna Aziz al-Kawalek mai shekaru 10, wanda shi kadai ya rayu a cikin iyalansu, yana zaune a kusa da gawar mahaifiyarsa.

Ido Avigal, mai shekaru 5

Asalin hoton, Twitter

Bayanan hoto,

Ido Avigal mai shekara biyar ya mutu a harin roka da Hamas ta kai

Ana tunanin mafi kankantar shekaru cikin 'yan kasar Isra'ila da harin ya rutsa da su a ranar Larabar da ta gabata a kudancin garin Sderot shi ne Ido Avigal, wani yaro mai sheakara biyar.

Ido ya hallaka a cikin wani daki da aka tanada don kariya daga harin, a wani abu da rundunar sojin Isra'ila ta bayyana na ''ba kasafai'' yake faruwa ba.

Mahaifiyarsa ce ta janyo shi ta kai shi dakin kariyar a lokacin da ta ji ƙarar jiniyar makamin rokar a yammacin Laraba a garin na Sderot, kamar yadda jaridar Times ta Isra'ila ta bayar da rahoto.

Makamin rokar ya huda cikin karfen kariyar da aka yi amfani da shi wajen rufe tagar dakin da yake ciki, ya kuma jikkata mahaifiyarsa da yayarsa. Ya mutu bayan wasu sa'o'i sakamakon raunukan da ya samu.

"Wani makamin roka ne da ya fado a dai-dai wata kusurwa, kuma cikin sauri da kuma dai-dai wuri,'' mai magana da yawun rundunar tsaron Isara'ilar IDF Hidai Zilberman ya bayyana.

"Muna cikin gida kuma yara duk sun gaji da zama wuri guda, don haka mata ta Shani ta fita da su gidan 'yar uwarta wanda gida biyu ne tsakani,'' mahaifin Ido, Asaf Avigal, ya shaida wa gidan talabijin na Channel 13.

"Ka gafarce ni ban zame maka garkuwa daga makamin rokar ba,'' Mista Avigal yake fada a lokacin jana'izar ɗansa.

"Kwanaki kadan da suka gabata, ka tambaye ni: 'Baba, me zai faru idan jiniyar ta buga a lokacin muna waje?' Na fada maka cewa muddin kana tare da ni za ka samu kariya. Na yi karya.''

Watanni kadan da suka gabata, Mista Avigal da matarsa sun yi magana game da basirar da karamin ɗansu Ido ke da ita, kamar mai shekaru 50 ne da jikin ɗan shekara biyar.

Ya kan yin kira ga mahaifinsa da ya bar abin da yake yi da na'urar komfuta don ya samu lokaci da shi. "Kallon komfutar ya isa haka - ka kasance a tare da ni,'' ya kan fada.

Mahaifiyar Ido na ci gaba da kwanciya a asibiti.

Nadine Awad, mai shekaru 16

Nadine Awad, mai shekaru 16- daliba kuma Balarabiyar Isra'ila na tare da mahaifinta mai shekara 52 da safiyar ranar Laraba, a lokacin da makamin rokar ya fada a kan motarsu da gidansu, ya hallaka su duka.

Mahaifiyarta wacce ita ma ke cikin motar ta samu munanan raunuka, in ji likitoci.

Danuwan Nadine, Ahmad Ismail, ya ce ya ji ƙarar makamin rokar lokacin da ya fada cikin gidan iyalan a birnin Lod, kusa da birnin Tel Aviv, inda Falasɗinawa da Yahudawa ke zaune wuri guda.

"Lamarin ya faru cikin sauri,'' ya shaida wa wani dan jarida Khan. ''Ko da a ce muna so mu tsere wani wuri, ba mu da maɓoya mai kariya.''

Nadine yarinya ce mai shiga rai a shekarar karatunta na farko a babbar makaranta, tana da burin zama likita, wadanda suka san ta suka bayyana.

Shugabar makarantarta ta ce ''tana da burin sauya duniya''.

"Yarinya ce ta musamman, mai ƙwazo da basira. Tana da burin sauya al'amuran duniya," Shirin Natur Hafi ta shaida wa wata kafar gidan rediyo a yankin, kamar yadda jaridar Times ta Isra'ila ta bayar da rahoto.

Nadine na kan gudanar da ayyukan da suka danganci kimiyya da dama tare da makarantun Yahudawa a yankin, kuma ta yi aniyar shiga cikin al'amuran kimiyya, in ji Miss Hafi.

'Ya'yan iyalan al-Hadidi, masu shekaru 6 zuwa 13

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jariri Omar ne kawai ya rayu a cikin zuri'arsu

A ranar Juma'a 'ya'yan Muhammad al-Hadidi hudu - Suhayb, mai shekara 13, da Yahya, mai shekara 11, Abderrahman, shekaru takwas Osama, shida.

Sun sanya tufafin su mai kyau suka tafi ziyartar gidan 'yan uwansu a kusa, a cikin sansanin 'yan gudun hijira na Shati da ke wajen birnin Gaza, don bikin ranar karamar Sallah wanda ya kawo karshen watan azumin Ramadan.

"Yaran sun saka kayansu na Sallar Idi, sun dauki kayan wasansu suka nufi gidan kawunsu don yin bikin,'' mahaifinsu mai shekaru 37 ya bayyana wa manema labarai.

"Sun kira da yamma suna roƙona da in amine su kwana a can, na ce musu babu damuwa."

Washegari, hari ya fada kan ginin da suke ciki, jaririnsu mai watanni biyar ne kawai ya rayu bayan da aka zaro shi daga cikin ɓaraguzan inda yake kwance kusa da gawar mahaifiyarsa.

"Suna da kariya a cikin gidajensu, ba sa dauke da makamai, ba su harba makaman roka ba,'' Mista Hadidi ya ke bayani a kan 'ya'yansa.

''Me suka aikata da har suka cancanci haka? Mu fararen hula ne.''

A cikin tarkacen akwai kayan wasan yara, da wani katakon wasan Monopoly, kana a kan kantar ɗakin dafa abinci akwai farantan abincin da ba a gama ci ba daga taron shagulgulan sallah.

"Lokacin da yarana suka kwanta barci, suna cike da fatan cewa lokacin da suka farka komai zai wuce. Amma yanzu sun rasa rayukansu.

"Kewar su ce kawai ta rage min, da kuma ƙamshin jikinsu a cikin gidana,'' Mista Hadidi ya shaida wa jaridar Times a birnin London.

Ibrahim al-Masry, mai shekaru 14

Ibrahim al-Masry na cikin wasa tare da 'yan uwansa a kofar gidansu a arewacin Gaza a makon da ya gabata, lokacin da harin ya fada kansu, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Ibrahim da ɗan uwansa Marwan, da sauran danginsu da dama sun mutu nan take.

"A kullum lokacin watan azumin Ramadan su kan fito su yi wasa a bakin titi a dai-dai wannan lokaci na kafin buda-baki," mahaifinsu Youssef al-Masri, ya shaida wa jaridar The Independent.

"Ba mu hangi faruwar hakan ba, mun dai ji wasu manyan ƙarar fashewa biyu…. Kowa na ta gudu a kan titin, yara jina-jina, iyaye mata na ta rusa kuka, jini a ko ina.''

Ɗan uwansu da shi ma ake kira Ibrahim ya ce, a lokacin suna cika buhunan karan alkama don su je su sayar a kasuwa ne.

"Muna ta farin ciki da annashuwa, a daidai lokacin da suka fara kai mana harin bam, komai a kewaye da mu ya kama da wuta,'' ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

"Na ga yadda 'yan uwana suka kama da wuta, suka kuma tarwatse.''

Hamza Nassar, mai shekaru 12

Hamza Nassar ya bar gidansu a Gaza a yammacin Larabar da ta wuce don samo wasu ganyayyakin da mahaifiyarsa za ta dafa abincin buda-baki na azumin watan Ramadan, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Bai sake dawowa gida ba.

Hamza yaron kirki ne, kuma ɗalibi mai ƙwazo, mahaifinsa ya shaida wa gidan talbijin na Al Jazeera.

Tala Abu al-Ouf, mai shekaru 13

Asalin hoton, Abu al-Auf family/DCIP/NRC

Bayanan hoto,

An kashe Tala Ayman Abu al-Ouf tare da ɗan uwanta mai shekara 17

Irin harin da ya fada gidan iyalan al-Kawalek ne ya yi sanadiyyar mutuwar maƙwabciyarsu Tala Abu al-Ouf mai shekara 13, da kuma ƴaƴanta Tawfik mai shekaru 17.

Mahaifinsu, Dr Ayman Abu al-Ouf shima ya mutu a harin. Shi ne shugaban sashen bayar da magunguna a asibitin al-Shifa na birnin Gaza, inda yake lura da ɓangaren ɗaukar mataki kan cutar korona.

A cikin 'yan kwanaki kafin harin, Dr Abu al-Ouf na shafe sa'o'i a asibitin yana gudanar da aiki, aminan iyalan suka shaida wa BBC.

Malamin makarantar Tala da bai amince a bayyana sunansa ba, ya bayyana ta a matsayin "daliba mai ƙwazo'' da ke shekarar karatu ta bakwai.

Tala na sha'awar darussan addini kana, tana son karatu da haddar Alkur'ani,'' malamin ya shaida wa BBC, ya ƙara da cewa a ko da yaushe cikin shirin jarrabawa take.

Tana kuma halartar shirin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta kasar Norway (NRC) don taimaka wa ƙananan yara dawowa cikin hayyacinsu daga ɗimuwa.

"Sun riga sun sha wahala sosai,'' in ji Hozayfa Yazji, manajan hukumar lura da 'yan gudun hijirar ya shaida wa BBC.

"Ya kamata a dakatar da wannan mummunan abu… ya kamata a dakatar da tashin hankalin, don a saboda wadannan kananan yara su samu makoma mai kyau.''

Karin wasu rahotanni daga wakilan BBC Alexandra Fouché, Angy Ghannam, da Ahmed Nour, da Tala Halawa, da Dana Doulah da kuma Joana Saba