Janar Attahiru: Buhari da Osinbajo na shan suka kan kin halartar jana'izar sojoji

Buhari da Osinbajo

Asalin hoton, Presidency

Ƴan Najeriya sun sako Shugaba Muhammadu Buhari a gaba da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo musamman a Twitter saboda rashin halartar jana'izar Babban Hafsan sojin ƙasa da sojoji 10 da hatsarin jirgin sama ya kashe a Kaduna.

A ranar Asabar a Abuja aka binne Babban Hafsan sojin Najariya Janar Attahiru tare da sojoji 10 da suka mutu a hatsarin jirgin sama a ranar Juma'a yayin wata ziyarar aiki daga Abuja zuwa Kaduna.

Sojojin da suka mutu sun ƙunshi Janar guda uku da suka haɗa da Birgediya Janar Kuliya babban jami'in leƙen asiri na sojin Najeriya da Birgediya Janar M Abdulkadir da kuma Birgediya Janar Olayinka.

Tun a ranar Juma'a da hatsarin jirgin saman ya faru fadar shugaban Najeriya ta fitar da sanarwa da ke cewa "Buhari ya yi matuƙar kaɗuwa game da hatsarin jirgin saman da ya yi sanadin mutuwar babban hafsan sojan ƙasa Janar Ibrahim Attahiru da kuma wasu jami'an soja.

Buhari, wanda ministan tsaro Janar Bashir Magashi (mai ritaya) ya wakilce shi wurin jana'izar sojojin, ya yaba wa Janar Attahiru kan jajircewarsa a yaƙin da yake jagoranta da masu tayar da ƙayar baya tare da bayyana shi a matsayin "Babban hafsan soji kuma jagoran da ake kwaikwayo da shi.

Duk da wasu manyan jami'an gwamnati da gwamnoni sun halarci jana'izar sojojin amma rashin halartar Buhari ne ya fi jan hankalin ƴan Najeriya.

Wasu na ganin mutuwar sojoji babban al'amari ne a Najeriya, kuma rashin halartar shugaban ƙasa da mataimakinsa ya nuna rayuwar sojojin ba komi ba ne.

Wasu kuma masu mayar da martani na bayar da dalilai na tsaro da annobar korona a matsayin abin da ya sa shugabannin suka ƙauracewa wurin jana'izar sojojin yayin da kuma wasu suka ce ba saɓa doka ba ne don shugaba bai halarci jana'iza ba.

Wasu kuma na ganin mahawarar da ake ba ta da wani amfani, abin da ya fi amfani ga ƴan Najeriya shi ne jimami da kuma yi wa ƙasa addu'a kan wannan babban rashin sojojin da aka yi.

Abin da ƴan Najeriya ke cewa

Asalin hoton, Presidency

An yi ta tafka mahawara a Twitter kan rashin halartar Buhari a matsayinsa na Babban Kwamandan sojojin Najeriya da mataimakinsa wurin jana'izar sojojin da suka mutu inda ƴan Najeriya da dama ke suka da caccakar shugabannin.

Sunan Babban Kwamandan sojojin Najeriya C-in-C da Buhari da Osinbajo da Janar Attahiru sun kasance waɗanda aka fi tattaunawa a Twitter a Najeriya.

Kawo yanzu an yi amfani da sunan C-in-C fiye da dubu 116, an kuma yi amfani da sunan Buhari kusan sau dubu 60 yayin da kuma aka yi amfani da sunan Osinbajo fiye da 6,000.

@BonettGwazah ya ce: Gaskiya na yi mamakin a ce Buhari ko kuma Babban Kwamandan sojojin Najeriya bai halarci jana'izar Janar Attahiru ba. Haka ma mataimakin shugaban ƙasa.

@FaladeTolu_ ya ce: Idan har C-in_C, Buhari bai daraja mutuwar Babban Hafsan sojin Najeriya ba, to wa zai ce sojojin da ke fagen daga ya damu da su!

@BrightJaye ya ce: Buhari na iya karɓar baƙuncin shugabannin Chadi da Nijar ba tare da tura wakilai ba amma ba zai iya halartar jana'izar Babban Hafsan Soja ba. Wannan tamkar saƙo ne ga ƴan Najeriya cewa bai damu da ƙasar nan ba.

Wasu kuma sun ta yaɗa hoton tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan lokacin da ya halarci jana'izar tsohon Babban Hafsan sojojin Najeriya Janar Andrew Azazi wanda ya mutu a hatsarin jirgin sama tare da tsohon gwamnan Kaduna Patrick Yakowa a watan Disamban 2012.

@Amiiiinu ya ce: Tsohon Babban Kwamandan sojojin Najeriya Goodluck Jonathan ya halarci jana'izar Janar Andrew Azazi a jihar Bayelsa.

Martani

Wasu ƴan Najeriya kuma sun mayar da martani.

@GoziconC ya ce: Shin Jonathan ya halarci jana'izar tsohon mai gidan shi, Shugaba Ummaru Musa Yar'adua a 2010? Ina son wani ya nuna min hoton Jonathan a wurin jana'izar, daga nan muke da damar yin gardama da wani

@xndagi ya ce : Don shugaba Buhari bai halarci jana'izar Janar Attahiru ba, ba cin amanar ƙasa ba ne. Kuma ba aikata wani laifi ba ne. Idan wannan ya dame ka kan rashin halartar shi, maganin ƙwari na Snipper naira 400 yake kawai. Sai ka taimaka wa kanka ka taimaki Najeriya

@malam_noor ya ce: Batun Buhari bai halarci Jana'iza ba ya mamaye asalin muhimman abin da ya faru na mutuwar manyan sojojinmu. Kamata ya yi a yi ma su addu'a.

@jarmari01 ya ce: Ko da a ce Buhari da mataimakinsa Osinbajo sun halarci jana'izar, wasu sai sun sami wani abin faɗa kan halartarsu.

@Gordonzblaq ya ce: Shugaba Buhari wata ƙila killace kansa ne saboda balaguron da ya yi zuwa Paris, shi ya sa bai halarci jana'izar Babban Hafsan sojojin Najeriya ba da sauran sojojin da suka mutu.