'Hoton da ya sa na kusa fita daga zauren Whatsapp na gidanmu'

Collage art of three people looking at their phones, standing in front of Covid virus symbols with a large WhatsApp symbol above them

Asalin hoton, Aishwarya

Zaurukan Whatsapp na ƴan gida ɗaya a Indiya na iya zama wurare masu ɓata rai a daidai wannan lokacin, yayin da cutar korona ke ci gaba da kashe dubban mutane duk rana a ƙasar.

Amma a iyalan da kawo yanzu annobar ba ta shafe su ba, saƙonni da hotuna na barkwanci kan janyo ɓacin rai, a cewar wakiliyar BBC kan harkokin jinsi Megha Mohan.

Yayin da ɗan yatsana ke shawagi a daidai inda zan danna na fice daga zauren, na fahimci cewa wannan ne karon farko da na yi tunanin ficewa daga zauren Whatsapp na ƴan gidanmu.

Duk da cewa ina yawan ficewa daga zauruka da dama ba tare da jin kamar na yi laifi ba, duk cikinsu babu wani ɗan uwana a zauren.

Kuna iya tunanin yadda zaure mai matukar hayaniya da mutanen da ke cikinsa ke zaune a nahiyoyi uku zai kasance? Hayaniyar ta wuce tunaninku.

Ana aiko sakonni kullum, a ko wane lokaci. A lokacin da waɗanda ke Indiya ke shirin kwanciya bacci, a lokacin ɓangaren iyalin da ke Amurka ke fara aiko hotuna da bidiyon ƴaƴansu da sauran batutuwan da suka shafi ƙasashen duniya kamar zaɓe ko mutuwar auren taurarin fina-finai.

Ina yawan amsa sakonni, musamman da "emoji". Ban fiye fara hira ba. Amma a ƴan makonnin da suka gabata, na aika wani hoton bangon jaridar New York Times ran 26 ga Afrilu zuwa zauren iyalinmu na Whatsapp.

Bangon na ɗauke da labarin yadda cutar korona ta mamaye Indiya, da hotunan gwamman wuraren ƙona gawa mutane na tsaitsaiye suna alhini sanye kayan kariya. Kan labarin ya ce, "Ƙona Gawarwaki Ba Ta Ƙare Ba".

Ba jimawa wani ɗan uwana ya aiko shafin wata maƙala da aka wallafa a Australiya da ke zargin Firaiminista Modi da ingiza Indiya cikin hallaka.

A daidai wannan lokacin ne wani ɗan uwanmu da ke zaune a Indiya ya fara magana ba ƙaƙƙautawa.

"Ko wace ƙasa ta fuskanci annobar nan kuma babu gwamnatin da ta yi nasarar shawo kanta," ya rubuto. "Kuma kafafen yaɗa labarai ba sa faɗin gaskiya...suna da ajandarsu."

Asalin hoton, Aishwarya Mullamuri/Instagram @jffpix

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wani ɗan uwan namu ya biyo wannan bayani da hoton barkwanci na "meme". Ga kalaman da suka biyo bayan hoton: "Gaba ɗaya duniya ta shiga damuwa kan Indiya, Indiyawa kuwa na damuwa kan ko mai aikinsu za ta zo yau ko ba za ta zo ba ." Ya sako "emoji" mai nuna alamun dariya da hawaye.

Na fara jin irin ɓacin ran da ake yawan ji idan aka daɗe ana ɓata lokaci a shafukan sada zumunta.

Ga ni nan, ina kallon wayata a gidana da ke Landan, kuma na yi allurar riga-kafin korona. Raina ya ɓaci da ganin ƴan uwana a Indiya na aiko hotunan barkwanci kuma suna neman su ci mutuncina. (A matsayina na ƴar jarida, sai raina ya ɓaci dangane da kalamansu na cewa kafafen yaɗa labarai ba sa bayyana gaskiyar labarin.)

Kanun labarai dangane da Indiya a Birtaniya sun ƙunshi hotuna masu kama da na yaƙi kama daga asibitoci da bukatar iskar oxygen da dubban mutane da suka mutu, babu alamun samun sauƙi.

Iyalina dukansu masu ilimi, kuma babu wanda annobar ta shafa. Mafi yawan labarai sun nuna annobar korona a Indiya ta sa masu ƙaramin ƙarfi cikin mawuyacin hali - duk da cewa akwai masu arziƙi da dama sun bayyana cewa su ma ba su samu gadan asibiti ba, ciki har da tsohon jakadan Indiya a Brunei da Mozambique da Algeria, Ashok Amrohi wanda ya mutu a filin ajiye motoci a wani asibiti a watan Afrilu yayin da yake jira a ba shi gado.

A cewar ƙungiyar National Domestic Workers Movement, sama da mutum miliyan huɗu ne ke aiki a matsayin ƴan aikin gida a gidajen masu hannu da shuni kamar dangina, amma ƙiyasin da ba na hukuma ba ya ce sun kai mutum miliyan 50.

Abokan aikina da ke aiko da rahotanni daga Delhi sun ce an kori mafi yawan waɗannan ma'aikatan kuma ba a ba su haƙƙoƙinsu ba.

Wannan ne ya sa hoton barkwancin da aka turo ya ɓata min rai. Kuma a dai-dai lokacin ne na ga wani saƙonn Twitter daga wani marubuci da ke zaune a New York: "A shirye na ke in bar zauren Whatsapp na iyalin gidan Desi," ya ce. "Barkwancin da ake yi kan cutar korona ya ishe ni."

Bayan ɗan gajeren bincike a shafukan sada zumunta na gano masu amfani da Whatsapp da ba su ji dadin barkwancin da iyalansu ke yi kan cutar Korona, kuma mafi yawansu Indiyawa ne.

Indiya ce ƙasar da masu amfani da Whatsapp suka fi yawa, da kusan mutum miliyan 340.

Haka kuma, Indiyawa ne suka fi ƴan ko wace ƙasa yawa a sauran ƙasashen duniya, a cewar Majalisar Dinkin Duniya da kusan mutum miliyan 18 da ke zaune a ƙasashen waje.

Asalin hoton, Aishwarya Mullamuri/Instagram @jffpix

"Abin na da alaƙa sosai da yadda kowa ke kallon abubuwa," a cewar Dr Charusmita, wani mai bincike kan yaɗa labarai da ke zaune a Delhi.

"Da a ce wannan hoton wani iyalan masu matsakaicin ƙarfi aka tura wa da ke zaune a Indiya, da yadda za su kalli lamarin zai kasance daban.

Ba an yi ne don a ƙasƙantar da mai aikin ba sai don a zolayi darajarsu.

"Wasu na jin dadin irin wannan rahar da ake yaɗa wa a Whatsapp, wasu kuwa takaici abin ke ba su."

Amma mutanen da ke zaune a ƙasar ba sa son a dinga tuna musu bambancin yadda rayuwarsu da al'adunsu suke, ta ce, saboda suna ganin hakan na jawo musu farin jini.

Dr Charusmita ta ce min an sha aike mata hotuna da bidiyon da ƴan ƙasar mazauna ƙasashen waje ba lallai su fahimci me suke nufi ba, da suka haɗa da zanen barkwanci na mutanen da ke ɗaukar hotunan marasa lafiyan da suka gargarar mutuwa - abin da ke nuna yadda a yanzu har mutuwa ta zama abar wasa da talla a shafukan sada zumunta.

Asalin hoton, Aishwarya Mullamuri/Instagram @jffpix

Sannan ana yaɗa hotunan barkwanci marasa zafi a zaurukan Whatsapp na iyali. An yaɗa wani hoto na Firaiminista Narendra Modi yana wasan motsa jiki na Yoga, yana shaƙar numfashi da hanci ɗaya a rufe.

Sai aka alaƙanta hoton da cewa "firaiministan na shaƙar numfashi da hanci ɗaya don sauran marasa lafiya su shaƙa da ɗayan.

"An sha ba da rahoto kan labaran ƙarya a zaurukan WhatsApp a Indiya, amma bai kai na rahar da ake bazawa ba," a cewar Dr Rohit Dasgupta na Jami'ar Glasgow, wanda ya ƙware a Al'adun Indiya na dijita.

"Idan muka yi dariya, akwai kyakkyawan fata, idan kuma akwai kyakkyawan fata to ana samun sauƙin ciwo."

Sannan akwai batun jin haushin yadda ake sanya ƙasar cikin ƙasashe masu tasowa, duk da cewa kuwa ta samar da miliyoyin alluran riga-kafin AstraZeneca har ma aka fitar da su kasashe da dama da suka haɗa da Syria da Birtaniya.

"Akwai alfahari ma kuma," a cewar Dr Dasgupta. "Duk da cewa a bayyane yake cewa Indiya na buƙatar taimako, Indiyawa a ƙasar na son ku san cewa za su iya taimakon kansu."

Daga baya wanda ya ƙriƙiri hoton barkwancin ya aika min saƙo cewa ba da niyyar wulaƙanta masu aikin Indiya ya yi hakan ba.

Sannan wani ɗan jarida a Delhi ya gaya min cewa a makonnin baya-bayan nan zaurukan WhatsApp sun zama tamkar wajen sanarwar mutuwa.