Afghanistan: Bidiyon ƴan Taliban suna wasa a wuraren shaƙatawar yara sun ja hankalin duniya

Taliban fighters are seen on the back of a vehicle in Kabul, Afghanistan, 16 August 2021

Mutane daga sassa daban-daban na duniya suna ta nuna al'ajabi kan jerin wasu bidiyo na mayaƙan Taliban a wuraren shaƙatawar yara da wuraren motsa jiki suna ta tsalle-tsalle.

Bidiyo da hotunan sun yaɗu kamar wutar daji a ranar Alhamis inda mutane ke tofa albarkacin bakinsu.

Wannan lamari na zuwa ne kwana biyu bayan da ƙungiyar ta gama ƙwace iko da ƙasar daga hannun gwamnati, bayan janyewar dakarun Amurka da suka shafe shekara 20 suna yaƙi.

Babban abin da ya fi bayar da mamakin shi ne yadda ba a saba ganin mayaƙan na Taliban suna duk wani abu da ya danganci wasa ko raha na - sun fi mayar da hankali wajen yaƙi.

Yawo da bindigar AK47 da aka fi saninta da Kalashnikov a Taliban, ita ce alama da ke nuna ƴan Taliban a ko yaushe, saboda ba sa yawo sai da ita.

Don haka ganinsu a irin wannan yanayi na wasa da dariya ya jefa mutane cikin mamaki da tunanin anya ƴan Taliban din da aka sani a baya ne ko kuwa wasu sabbi ne.

Me bidiyon suka ƙunsa?

Bidiyo daban-daban da suka kai huɗu ne suka yaɗu a shafukan sada zumunta.

Na farko yana nuna mayaƙan Taliban din ne dukkansu ba sa ɗauke da bindigar Kalashnikov, sun ajiye su a gefe, a filin wasan yara, wato Amusement Park.

Sun shiga cikin motocin da ake fi sani da Bumper Cars suna ta tuƙawa cikin nishadi suna karo da juna.

Sannan an gan su suna hawa irin dokin nan na wasan yara suna ta sukuwa.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Wasu na ganin hakan ba komai ba ne tsabar shafe shekaru ana yai ne ya sa an Taliban ke cikin nishadi yanzu

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A bidiyon an ga yadda yara da mata da wataƙila suka je wajen shaƙatawar, suna tsaye suna kallon mayaƙan Taliban.

Bidiyo na biyu kuwa, ƴan Taliban aka gani shi ma dai a wajen wasan yara, suna ta tsalle-tsalle a kan wani abu da ake kira Bouncing Castle.

Shi dai Bouncing Castle ana hawa kansa ne a yi ta tsalle ana faɗawa kai kamar dai shillo. Shi ma yawanci yara aka fi gani suna wasa a kai.

Amma a wannan bidiyon sai ga ƴan Taliban ɗin har wasu na ƙoƙarin cire rawaninsu, wataƙila don su fi jin daɗin tsallen da kyau. Suna kuma ta sheƙa dariya.

Bidiyo na uku kuwa nuna ƴan Taliban ya yi a wajen motsa jiki. Sun hau kan abin motsa jikin da ak fi sani da Tred Mill wanda yake yi kamar mutum na tafiya ne a kai.

Sai dai shi a cikinsa ba su cire rawanin ba, amma ga alama wasu ma a tsorace suke da shi don kar su faɗi, wataƙila saboda rashin sabo.

Na ƙarshen kuwa ba a wajen wasa aka ga mayaƙan Taliban din ba. An gansu ne a cikin wani babban falo a fadar gwamnatin Afghanistan.

Sun barbaje a kan kujeru suna kwasar girki, loma ba kama hannun yaro.

Wasu labaran masu alaƙa

Me mutane ke cewa?

Mutane a faɗin duniya, ciki har da Najeriya na ta tsokaci kan wannan gagarumin sauyi da aka gani tattare da mayaƙan Taliban.

Kusan mutum 26,000 ne suke tattauna batun a shafin Facebook kawai a ranar Laraba.

Ga dai abin da wasu ke cewa:

Ita ma wata ƴar Najeriya Rahama Abdulmajid ga abin da ta ce:

Asalin hoton, Facebook

Mutane da dama dai na ganin ƴan Taliban ƙara'i suke yi, tun da su a tsaunuka da daji suka saba rayuwarsu.

Don haka yanzu dama ta zama a cikin gari ta samu shi ya sa suke ɗan watayawa, kamar yadda masu iya magana kan ce rai dangin goro ne sai da ban ruwa.

Wasu kuwa tababa suke kan anya wadannan 'yan Taliban din farko ne kuwa 'yan gargajiya da aka sani? Ko sun zamanantar da kungiyar tasu ne?

Ra'ayin wasu kuma na cewa so suke su sauya tsohon tarihin da aka sansu na tsattsauran ra'ayi don duniya ta karɓe su a dama da su a siyasance.

Wasu ko gani suke shekara 20 din da ƴan Taliban suka shafe suna yaƙi ai yanzu lokacin da ya kamata su ji dadi ne ya zo.

Yayin da wani ɓangaren ke cewa da yawan ƴan ƙungiyar fa ba su mori ƙuruciyarsu ba da irin wasannin nan na yara, don haka yanzu duniya sabuwa.

To ko ma dai mene ne, a iya cewa ƴan Taliban sun ba da mamaki ƙwarai a wannan gaɓa. Yanzu kuma sai a zuba ido a ga yadda mulkinsu a ƙasar Afghanistan zai kasance.