Satar Dalibai: Yadda ƴan bindiga suka jefa ɗalibai mata cikin fargaba da damuwa a Zamfara

Makaranta a Zamfara

Asalin hoton, Getty Images

Ƴan bindiga masu satar mutane sun jefa ɗalibai a makarantun kwana a Najeriya cikin yanayi na zullumi da tsoro da fargaba da kuma damuwa.

Wasu ɗaliban makarantun sakandaren mata a jihar Zamfara da BBC ta samu zantawa da su da kuma iyayensu sun bayyana irin yadda yawaitar sace-sacen ɗalibai ya jefa ɗaliban cikin fargaba inda wasunsu suka ce zaman zullumi da kwanciya cikin fargaba ya jefa su cikin tsananin damuwa.

Ƴan bindiga musamman a jihohin arewa maso yammacin Najeriya sun kafa kahon zuka kan makarantu, inda aka sace dalibai da malamai da kashe ƴan makaranta da dama kuma har yanzu ana garkuwa da wasu ɗaliban.

Ko a ranar Laraba a makon nan ƴan bindiga sun sake abkawa wata makaranta a yankin Maradun a Zamfara inda suka yi awon gaba da ɗalibai da dama, kuma a yankin ne aka saci ɗaliban kwalejin noma ta Bakura da ɗaliban sakandaren garin Jangebe a Talatar Mafara.

Mahaifiyar ɗaya daga cikin ɗaliban ta ce "tsoron ƴan fashi masu satar mutane da fargabar za a iya abkawa makarantarsu ya sa ƴarta ta kasa yin bacci tsawon mako ɗaya."

"Wannan yanayin har yana neman taɓa ƙwaƙwalwarta saboda girman damuwar da ta shiga," in ji ta.

Wannan yanayi da ƴan bindiga suka addabi arewa maso yammacin Najeriya da kuma yadda ake abkawa makarantu ba zato ba tsammani a sace ɗalibai, ya sa hukumomi a jihar Zamfara daukar matakin rufe makarantun bayan daukar sabbin matakai na tsaro da suka ƙunshi hana cin kasuwar mako-mako.

A nasu ɓangaren wasu makarantu na mata a jihar Zamfara inda matsalar ƴan fashi ta fi yin ƙamari, ɗaliban sun ce ana koya masu matakai na kariyar kai da kuma yin shirin da ya dace a lokacin bacci don kada ƴan bindiga su mamaye su.

Matakan kare kai

Ɗaliban sakandare da BBC ta zanta da su sun bayyana irin matakan kare kai da aka koya masu musamman a lokacin da za su yi bacci.

Sun ce an buƙaci kullum su kasance cikin shiri duk lokacin da za su kwanta bacci da dare. "Ana buƙatar komi ya kasance a kusa da mu lokacin kwanciya, kuma an ce mu dinga kwanciya da hijabi da takalminmu da audugar mata a kusa da mu," in ji ɗaya daga cikin ɗalibar sakandaren kwana a Zamfara.

Wata kuma ta ce an koya masu yadda za su rike makami tare da shirin ko-ta-kwana inda ta ce a kullum suna kwanciya da tufafin da ya dace da safa da kuma riƙe wuƙa.

Shiga damuwa

Asalin hoton, Getty Images

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Sai dai matakan kare kai da ake koya wa ɗaliban da kuma rahorannin yawan sace-sacen dalibai ya jefa wasunsu cikin tsoro da damuwa.

Mahaifiyar ɗaya daga cikin ɗaliban a Zamfara ta ce ƴarta takan yi mafarkin yan bindiga sun shigo makarantarsu za su sace su, wannan ya yi tasiri sosai a rayuwarta har ta kai ba ta iya bacci, in ji ta.

Ta ƙara da cewa satar ɗaliban makarantar Yauri a jihar Kebbi shi ya ƙara razana 'yarta bayan satar ɗaliban makarantar Jangebe da aka yi a Zamfara.

Ta ce bayan ƴarta ta dawo hutu ne ta fara ba ta labarin irin halin da take ciki a makaranta da irin matsalolin da take fuskanta.

Kuma lokacin da aka kira ta cewa ƴarta ba ta da lafiya a makaranta, nan take ta fahimci cewa damuwa ce ke damunta saboda labarin da ta ke ba ta na mafarkin da ta ke yi.

Ta ce yarta ta samu bacci sosai bayan ta dawo da ita gida, kuma har takan zauna cikin mutane a yi hira da ita tana dariya da murmushi sabanin lokacin da tana makaranta.

Dukkanin iyaye sun fahimci abin da ake nufi da idan an sace wa mutum dansa. Kuma babban burin mahaifi da mahaifiya shi ne tabbatar da ƴaƴansu ba su faɗa hannun ƴan bindiga ba musamman mata da ke da rauni.

Ko kafin a fara garkuwa da mutane, Najeriya na cikin ƙasaashen da ke sahun gaba na yawan yaran da ba su zuwa makaranta.

A arewacin kasar kashi daya cikin biyu bincike ya nuna cewa ke zuwa makaranta, kuma sace sacen ɗalibai babban kalubale ne ga ilimi a kasar.

Fiye da ɗalibai 1,000 aka sace daga makarantu a arewa maso yammacin Najeriya, wanda ke nuna wani mummunan ci gaba mai matukar tayar da hankali a matsalar satar mutane domin neman kuɗin fansa.

Idan aka biya kudin fansa za a ci gaba da garkuwa da mutane - wannan wata sana'a ce da ke kara habaka wanda lamari ne mai razanarwa ga iyaye a Najeriya.

Ƴan sanda da sojoji duka suna ƙarƙashin ikon gwamnatin tarayya - kuma biyan kuɗin fansa, ya ƙara haifar satar mutane a matsayin wata babbar hanyar samun kuɗi.

Wasu hukumomi sun hana biyan kudin fansa, kamar a jihar Kaduna.

Gwamnatin Najeriya kuma ta daɗe tana musanta cewa akwai alaka da ke tsakanin yan bindiga masu satar mutane domin kuɗin fansa a arewa maso yammaci da kuma Boko Haram a arewa maso gabashi

Amma yadda ake ci gaba da satar da dalibai ya nuna akwai alaƙa tsakaninsu.

Ƴan ƙasar da dama sun yi imanin cewa akwai raunin a ɓangaren tsaro da gwamnoni waɗanda ba su da iko a kan tsaro a jihohinsu.

Akwai matakan tsaro da aka ɗauka a wasu makarantu, amma akwai makarantu da dama a yankin arewa da babu inuwar jami'ar tsaro.

Wasu makarantun sun ɗauki ƴan banga aiki amma wannan ya zama ba shi da tasiri a kan' yan ta'addan da ke dauke da muggan makamai.

Ko da yake jami'an tsaro na yaƙi da ƴan fashi a yankin, inda suka tarwatsa ƙauyuka da ke dazukan yankin da ƴan bindigar suka mamaye.

Amma wani rahoto da wata ƙungiya mai zaman kanta a jihar Zamfara ta fitar da ke cewa ƴan bindiga sun mamaye ƙauyuka sama da 70, muhimmin babu ne mai tayar da hankali da kuma nuna girman matsalar tsaro a yankin.

Timeline Factory

Hit link on top ⬆️ to find your timeline.