Yadda aka saba haihuwa: ‘Karairayi’ shida kan haihuwa da fina-finan Hollywood ke yaɗawa

  • Lucia Blasco
  • BBC News Mundo
Katherine Heigl during a childbirth scene in the 2007 movie Knocked Up

Asalin hoton, Universal Studios/BBC Mundo

Bayanan hoto,

Wasan Knocked Up wanda aka yi a 2007, wanda tauraruwar fina-finai ta Katherine Heigl ta fito a ciki,yana daya daga cikin fina-finan Amurka da aka nuna yadda ake haihuwa sabanin yadda a zahiri ake ahiuwa

A yayin da sau da dama fina-finan Hollywood na Amurka kan nuna yadda ake haihuwa, abubuwan da suke nunawar yawanci ba su da alaka ainihin abin da ke faruwa a dakunan haihuwa.

Wuraren nunin fina-finai na Amurka sun sha nuna yadda ake haihuwa, amma kuma akasari ba su yi kama da yadda yake faruwa da gaske ba.

Sau nawa muka taba ganin matan da ke cikin yanayi na dimauta, kana kuma nan da nan jakar ruwan da jariri ke kwance ta fashe ba tare da wata-wata ba? Kana mazajensu fa da ake nunawa sun kasa zaune sun kasa tsaye, daga karshe sukan suma a tsakiyar dakin haihuwa?

Daga bisani akwai kuma kyawawan jarirai da aka ajiye a hankali kan wani mashimfidi, suna kallon saman rufin dakin ko kuma kyamara.

Idan muka duba littafin This is Going to Hurt, wanda a ciki likitan Birtaniya Adam Key ya bayyana komai kan abubuwan da ke faruwa a dakunan haihuwa - tare da sharhin da wasu kwararru uku suka yi - mun bankado karairayi shida game da haihuwa da masana'antar shirya fina-finai ta Hollywood ta Amurka ke ci gaba da nunawa.

1. Ba sama muke kallo ba

A lokutan akasarin haihuwar da ake yi, abu na farko da ke fara fitowa daga kofar farji shi ne kan jariri.

Wannan ma yana faruwa a cikin fina-finai.

Amma kuma jariran da ake nunawa kansu na kallon sama ne, saboda ku kalli kyakkyawar fuskarsu. Hakan ba ya nuna ainihin abin da ke faruwa da gaske.

Fiye da kasha 90 bisa dari na jarirai na fitowa ne a dunkule - kansu na kallon kasa, habarsu na manne a kan kirjinsu, duwawunsu sun yi sama, kana kafafu da hannayensu a lankwashe kuma a manne kusa da jikinsu.

Hakan na nufin fuskokinsu na kallon bayan mahaifiyarsu kana duka kyamarori za su kalli kan jaririn ta baya ne.

Asalin hoton, Getty Images

"A yanayin kwanciyar jarirai a ciki da aka sani galibi jariran kan juya suna kallon kasa, ko kuma akalla zuwa gefe daya,'' in ji likitan mata da yara Damián Dexeus, daga Barcelona, kasar Sifaniya.

"Kuma dalilin wannan hadewa shi ne saboda alkinta wuri ga jariri: Idan suna kallon kasa, za su iya buda sararin kugun uwar," in ji shi.

"Yawanci a cikin fina-finai, za ka ga jarirai na kallon sama da idanunsu a bude - har ma da murmushi! Ba a saba ganin haka ba, ko shakka babu," a cewar likitan.

Har ila yau ba a haihuwar jarirai a wanke tas kamar na cikin fina-finai.

"Ba a haihuwar jarirai a wanke tas haka, in ji Dakta Dexeus.

Asalin hoton, Getty Images

Ya bayyana cewa a baya, al'adar da aka saba ce a asibitoci a wanke jariri da zarar an haife shi, a wanke masa wani datti - wani farin abu mai kama da kitse wanda ke rufe fatar jikin jariri a lokacin haihuwa - daga nan sai su mika wa uwar jaririnta a tsaftace.

2. Yadda jakar ruwan haihuwar ke ainihin fashewa

Nuna jakar ruwan haihuwar da ta fashe cikin lokaci kankane, kunshe da ruwan da jariri ke kwance ciki na fitowa, su ma abubuwa ne da aka saba nunawa a shirye-shiryen gidan talabijin.

Kusan da zarar mai juna biyu ta fara nakuda.

Wani misali: A wani wasan kwaikwayo na gidan talabijin na City TV da ake nunawa, jakar ruwan haihuwa na Charlotte ya fashe a yayin da ta ke cikin wata jayayya a gaban wani gidan cin abinci.

Daga nan ta ruga don samo motar tasi.

Asalin hoton, Getty Images

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

"Gaskiya, ba wani sabon abu ba ne na fashewar jakar (mai dauke da ruwan da jaririn ke kwance yana girma) ta bukaci dubawa a tabbatar da ko shin lallai ne ta fashe ko kuma akasin haka, saboda mai haihuwa ta lura cewa tana rasa wani ruwa daga jikinta, amma ba ta iya ganinsa sosai,'' in ji Dakta Dexeus.

Wannan na faruwa ne saboda ba abu me sauki bane a da ke yawan faruwa kamar yadda wasu da dama ke tunani banbance ruwan kwanciyar jaririn da kuma fitsari, musamman idan akwai wani damshi ko kuma digar wani ruwa.

Amma kuma, galibi fashewar ba tana tuna lokacin haihuwar ba ne, amma daya daga cikin matakan haihuwar ne.

"Yawanci yana faruwa ne a lokacin da mace ta riga ta fahimci cewa ta fara nakuda bayan wasu juyi da ta fuskanta.

"Daya daga cikin matakan nakuda ne,'' in ji Ann Yates, wata ungozoma a hadaddiyar kungiyar ungozomomi ta (ICM).

"Ko shakka babu, idan jakar ruwan ta fashe kafin lokacin haihuwa, kafin jaririn ya shirya fitowa, hakan na nufin akwai matsala,'' in ji ungozaman, wacce ta taba aiki a bangaren mata masu haihuwa har na tsawon shekaru 40 a wasu sassan duniya.

3. Yanayin yadda ake haihuwa

Daya abin da aka saba gani a fina-finan shi ne yanayin yadda haihuwar ke faruwa, inda mai nakudar ke zama a kan wani teburi mai tsawo.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Akwai yadda ake haihuwa daban-daban sabanin yadda ake nunawa a talabijin

Akwai misalai da dama: daga Ellen Page a Juno zuwa Katherine Heigl a Knocked Up da kuma Jennifer Aniston a Friends.

Tabbas wannan yanayi ne mai kyau a lokacin haihuwa, amma ba shi ne wanda ake yawan amafani da shi a fadin duniya ba.

"A Birtaniya da Amurka, an saba ganin mat ana kishingide a kan teburin haihuwa kana kafafuwansu a dage," in ji Dakta Dexeus.

"Amma a kasashen kamar Spaniya, yanayin da aka fi amfani da shi shi ne lithotomy, wanda mace za ta kwanta, inda za ta lankwace kafafaunta gwiwoyinta a sama amma ba sosai ba."

Baya da wadannan hanyoyi biyu, akwai wasu hanyoyi da dama na haihuwa da ba kasafai ake bayyanawa ba a gidajen sinima da talabijin - a tsaye, a tsugune, a zaune kan kujera da kuma a kwance ta gefen jiki daya.

Hakan ya kuma danganta da matakin haihuwar da mace ta ke ciki.

4. A ina aka bar postpartum?

Ana bayyana Postpartum a matsayin lokutan watanni shidan farko bayan haihuwa.

"Watanni shidan farko bayan haihuwa babban abu ne da ake mantawa da su a cikin fina-finai,'' in ji Dakta Dexeus.

Ba a ciki nuna abubuwa da dama da ke faruwa a lokacin haihuwa a cikin fina-finan Hollywood ba.

Abubuwa kamar fitowar mabiyya ko mahaifa - da kuma rufewar raunuka da kan faru ga uwa a lokacin haihuwa.

Amma ba hakan kadai ba.

Asalin hoton, Getty Images

"A kan nuna tsananin damuwar bayan haihuwa sama-sama a cikin fina-finai," in ji likitan matan, wato wani yanayi da ke shafar mace daya cikin 10 da suka haihuwa a fadin duniya, kamar yadda kididdigar Kungiyar Lafiya ta Duniya (WHO) ta nuna.

Har ila yau fina-finan ba sa nuna yadda shayarwa ke zama da wahala, da yadda haihuwa ke iya shafar mafitsarar mace tare da haifar da cututtukan mafitsarar, har ma da sauye-sauyen da dama na jiki da kan kasance mai wahala ga mata.

"Har ila yau ba sa nuna yadda warkewa daga tiyatar cire jariri ke da wahala," Dakta Dexeus ta ce.

"Hakan kan yaudarar da mu a kan mu rika tunanin cewa haihuwa na da sauki, tana da hadari sosai - saboda ba hakan ba ne a ko da yaushe," in ji ta.

5. Ihu na zafin haihuwa

Wani abu kuma yanayin haihuwa irin na cikin fina-finan sinima shi ne a lokacin da uwa ke kukan haihuwa.

"A baya, iyaye matan da ke haihuwa ba a yi musu allurar barci,'' Josefina López likitar kasar Cuba ta bayyana.

"Da gaske ne juyin nakuda akwai tsananin zafi kuma su kan dauku tsawon lokaci kuma mai haihuwar ta galabaita.

"Amma ba zafin ciwon ne ke tilsata maya yin ihun ba, duk da cewa ko wace mace akwai yanayin juriyarta."

"Idan dai akwai allurar rage jin zafin ciwo, ba a cika samun haka ba."

Asalin hoton, Getty Images

Yates na ganin cewa a wasu lokuta fina-finai kan sa mata kasancewa kamar masu raki a ciki.

"Mata na da kwazo. Wannan wani abu ne na bai daya,'' in ji ungozomanr.

"Kuma su kan iya jure wa haihuwar - wacce ke da zafi, ko shakka babu - sau da dama ba tare da yin ihu ba.''

"Kwarai, a wasu lokuta su kan yi surutai amma ba kamar yadda ake nunawa a cikin fina-finan ba,'' in ji ta.

6. Rashin yin katabus a bangaren mazan

Nuna uba cikin razana da toshewar basira ba wani sabon abu ba ne a cikin fina-finan.

Daya misali shi ne daya daga cikin bangaren wasan da Hugh Grant ya fito a cikin fim din barkwanci na soyaya Nine Month - wanda ya yi irin abubuwan da bas u kamata a ce namiji ya yi a dakin haihuwa ba.

"Akwai maza masu tsoro da fuskokinsu kan nuna razana a lokacin haihuwa. Kana akwai ma wadanda su kan suma," in ji Dakta Dexeus.

Asalin hoton, Getty Images

"Yadda ake nuna iyaye a dakunan haihuwa a cikin sinina na da ban takaici ne,'' in ji likitar.

"Amma kuma har ila yau hakan bai ta ce al'adar ba."

Yates ta ce a cikin fina-finan Hollywood a kan nuna mijin a matsayin wani mutum da bai san me ya kamata ya yi ba a lokacin haihuwa.

"Maza da mata da yawa da su kan raka mai haihuwa na kasancewa a tare da ita yadda ya kamata in ji ungozomar.