Abu biyar da ya sa Dangote ya ci gaba da zama attijirin Afrika tsawon shekara tara

  • Awwal Ahmad Janyau
  • BBC Abuja
Aliko Dangote

Asalin hoton, Other

Aliko Dangote ya daɗe a matsayin wanda ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afrika.

Hamshakin attajirin ya shafe shekara fiye 10 a matsayin attajirin Afrika tun shekarar 2013, kamar yadda alƙalumman jaridar Bloombarg kan attajiran duniya ya nuna.

Alƙalumman baya bayan nan da aka fitar ya nuna arzikin Dangote ya ƙaru, kuma yana yunƙurin kammala shekarar 2021 da arzikin da bai taɓa samu ba cikin shekara bakwai sakamakon haɓakar ribarsa a ɓangaren siminti..

Haɓakar kasuwar hannun jari a kamfaninsa na siminti da kuma tashin farashin man fetur da takin zamani sun taimaka wa Dangote inda dukiyarsa ta ƙaru da dala biliyan 2.3 a 2021 zuwa biliyan 20.1 jumilla, kamar yadda mujallar Bloomberg ta ruwaito.

A wata hira ta musamman da hamshakin attajirin na Afrika ya taɓa yi da attajirin ƙasar Sudan Mo Ibrahim a birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire a shekarar 2019, Dangote ya ce ya faɗaɗa kasuwancinsa na siminti a sassan Afrika da suka hada da Tanzania da Habasha da Zambia da Congo Brazzaville da Kamaru da Cote d'Ivoire

Ya ce yana da kamfanoni fiye da biyu a Najeriya da Afrika ta kudu.

Rabon da dukiyarsa ta kai yawan haka tun 2014, lokacin da ta kai dala biliyan 26.7 a watan Yunin shekarar, a cewar jaridar.

Tashin farashin kayayyakin gini a Najeriya, wadda ke da mafi girman tattalin arziki a Afirka, sun haɓaka ƙarfin jarin kamfanin Dangote Cement plc.

Nan gaba kaɗan ake sa ran Dangote zai kammala ginin matatar man fetur kan dala biliyan 19, wadda za ta dinga samar da fetur fiye da abin da kasuwar Najeriya ke buƙata.

A wannan shekarar ce kuma Dangote ya fara fitar da takin zamani zuwa Amurka da Brazil bayan kammala ginin ma'aikatar taki da ke iya samar da taki tan miliyan uku duk shekara.

BBC ta diba wasu abubuwa da suka yi tasiri da har yanzu aka kasa samun wanda ya kere Dangote a matsayin wanda ya fi kuɗi a Afrika, ta hanyar tattaunawa da wani makusancinsa da kuma masani tattalin arziki inda suka fadi abubuwa biyar kamar haka:

Kayan amfanin yau da kullum

Ko wane ɗan kasuwa ko kamfani yana da tsari na kasuwancinsa da abubuwa da yake dogaro da su da tsarin da yake bi da kasuwancin zai bunƙasa.

Dangote ya mayar da hankali ne kan harakar dangin abinci da babban abin da ake gini wato siminti. Kayan abincin sun hada da suga da fulawa da shinkafa da taliya da sauransu.

Kamfanonin Dangote na suga da fulawa da siminti sun mamaye kasuwa a Najeriya inda manyan kamfanoni na kayan zaƙi suke dogaro da shi wajen samar masu da suga.

Masanin tattalin arziki Farfesa Nazifi Darma ya ce ƙila Dangote ya fahimci cewa tsari na rayuwa ya tabbatar da cewa idan har akwai dan adam a raye dole zai buƙaci abinci da muhalli wanda dole a bukaci siminti, kuma idan akwai gwamnati dole za ta ta yi gine-gine.

Yawan ƴan Najeriya

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Masanin ya ce yawan ƴan Najeriya ya taimakawa Dangote zama attajirin Afrika domin Najeriya ta kasance babbar kasuwarsa ga yawancin abubuwan da yake samarwa saboda bukatun ƴan ƙasar.

Ya ce ƙila Dangote ya yi hangen cewa jama'a kullum ƙaruwa suke yi, kamar Najeriya da yanzu ke da yawan mutum miliyan 200 - kuma duk shekara ana haihar sama da miliyan shida wanda wannan ya yi yawan wata ƙasa ta Afrika

A cewar masanin babu abin da zai sa ace a rayuwa ta dan adam buƙata ta abinci da dangoginsa ya ragu, mai yiyuwa wannan yana daga cikin tsare tsaren Dangote na matsakaici da dogon lokaci.

"Ya duba waɗannan alƙalumman na haihuwa da arzikin da kasa ta ke samu da kuma bunƙasar tattalin arziki, wanda zai iya sa ya ci gaba da ƙara ƙarfin kasuwancinsa yana bunkasa kuma yana diba yadda tsare tsaren tattalin arziki yake na ƙasa wanda ake fitarwa a shekara don ya yi tsari yadda zai dace da tsarin kasuwancinsa."

"China ta zama kaɗangaren bakin tulo saboda yawan jama'a - Babu inda ake da babbar kasuwa kamar China. Duk bambanci aƙida da ƙiyayya da wasu kasashe ke yi wa China dole su yi hulɗa da ita saboda tana da kasuwar da suke buƙata," in ji masanin.

Aiki da ƙwararru

Ba a shiga kasuwanci da tafiyar da shi gaba gaɗi.

Ɗaya daga cikin kinshikin nasarorin Dangote shi ne ɗauko kwararru da suka san harakar kasuwanci da hada-hadar kuɗi, in ji Alhaji Shuaibu Idris Mikati, tsohon manajan kamfanin Dangote da ke kula da ɗaukar ma'aikata.

"Ina aikin banki aka kira ni aka ba ni aiki aka ce na bayar da tawa gudunmuwa, kuma akwai ire-ire na da muke aiki a manyan bankuna da aka ɗauko," in ji shi.

Ya ce duk da Dangote ya san kamfaninsa ne amma yadda ya ɗauko ƙwararru domin tafiyar da kasuwancinsa ya nuna cewa ci gaba ya sa a gaba.

Farfesa Darma ya ce duk wanda ya yi shura a kasuwanci dole yana da tsare tsarensa na sirri kuma yawanci ba su yadda wani ya sani ba - wanda shi ne sirrinsu na ci gaba.

Ya ce zurfin tunani da hikimar Dangote da aiki da masana da ƙwararru ya taimakawa masa.

Masanin ya ce akwai yiyuwar Dangote da shi da ma'aikatansa sukan zauna su yi dogon nazari mai zurfi kan ya tsarin jama'a yake shekara zuwa shekara wanda zai ba da tasiri kan abin da jama'a suke bukata.

Za su diba ya tsarin tattalin ariki na gwamnati da siyasa da zamantakewa yake.

Farfesa ya ce idan za ka yi kasuwanci mai girma kamar na Dangote, dole ka zama kana da sanayya da fahimta kan waɗannan abubuwa da za su tafi daidai a yanzu da kuma da abin da zai iya zuwa shekaru masu yawa.

Babu yadda za a yi a ce an wayi gari kamar abin da Dangote yake samarwa bukatarsa ya ragu.

Goyon bayan gwamnati

Duk ɗan kasuwa komi ƙwarewarsa da fahimtarsa da hikimarsa idan bai samu taimakon gwamnati ba yana da wahala ya yi tasiri, kamar yadda masanin tattalin arziki ya jaddada.

Ya ce kamfanoni na kasashen waje da suka baje a shekarun baya tsare tsaren gwamnati ne ya taimaka masu - "kuma zuwan Dangote sai gwamnati ta ga cewa da ka taimakawa wani na waje gara ka taimakawa naka."

Masanin ya ƙara da cewa gwamnati za ta iya diba abubuwa kamar zamansa ɗan ƙasa da kasuwancinsa na samarwa ƴan ƙasa buƙatu na yau da kullum da kuma arzikin da za ta samu

Arzikin ƙasa ya yi tasiri domin a cikin Najeriya ake yin abubuwan da ƴan Najeriya ke buƙata wanda kuma zai samar da ci gaba da kuɗaɗen shiga ta fuskanr ɗaukar ma'aikata da biyan haraji ga gwamnati

Kasuwancin Dangote ya taimaka wajen samar da ayyukan yi a Najeriya.

Kwazo da rashin fariya da kiyaye dokoki

Dangote ya siffantu da wasu halaye kamar yadda ake cewa "Mai nema na tare da samu - himma ba ta ga rago," in ji Mikati.

Ya ce ɗan kasuwa ne mai nuna kwazo da himma wurin neman taro sisi - "yana rigan mutane zuwa ofis - kuma kullum yana shiga gaban ma'aikatansa wurin tunanin yadda za a mayar da taro sisi."

"Ya tashi akan tunanin nema da kiyaye bin dokokin Ubangiji, wanda ya kasance jigon samun ci gabansa."

Yana kiyaye haƙƙoƙin Ubangiji, kamar fitar da Zakkah da Sallah domin ba zan manta ba duk lokacin da ake cikin tattaunawa idan lokacin sallah ya yi zai ce a tashi a tafi a yi Sallah," in ji tsohon ma'aikacin Dangote mai kula da ɗaukar ma'aikata Alhaji Shu'aibu Idris mikati

Ya ƙara da cewa gina jama'a da kiyaye dokokin Ubangiji ne ginshiƙin nasarar Aliko Dangote.

Sannan a cewarsa Dangote mutum ne wanda ba ya nuna riya da nuna isa ko tunƙaho, maimakon haka yana da sadaukar da kai da mayar da kansa ba bakin komi da mutunta mutane - wanda wannan tsani ne na nema.

"Idan ba kasan Aliko Dangote ba idan ka ganshi ba za ka iya gane shi ba."