Matsalar karancin abinci a Madagascar: Yadda wata mata ta ceto kauyensu daga bala'in yunwa

  • Daga Catherine Byaruhanga
  • Africa correspondent, BBC News
Mata da Miji tsaye a gona

Asalin hoton, Sira Thierij/BBC

Bayanan hoto,

Loharano tare da mijinta Mandilimana sun sauya yadda ake noma a yankinsu

Loharano ta yi aiki tukuru domin ceto mutane daga fari da yankinsu ke fama da shi ta hanyar fito da wani tsari da ya ceto su daga matsananciyar yunwa.

Tsawon lokacin da kudancin kasar ya dauka yana fama da fari, ya bar mutane miliyan 1 da dubu 300 suna fadi-tashin neman abin da za su ci, yayin da wasu 28,000 ke fama da tsananin yunwa. Wasu na kiran hakan fari na farko mafi muni da duniya ta fuskanta sakamakon sauyin yanayi, ko da yake wasu sun ce lamarin bai kai haka ba.

Sai dai kauyensu Loharano, Tsimanananda, inda take shugabantar al'umma, Allah ya kubutar da shi daga fari.

Tafiyar minti 45 ne daga garin Ambovombe, wanda shi ne babban gari a birnin Androy, yankin da ya fi kowanne jin jiki sakamakon rashin zubar ruwan sama.

Motar da muke ciki ba ka iya hango ta saboda kura da ta turnuke sakamakon yashin da ke kan hanyar. Yanayin da idan ka kalla ta gilashi zai tabbatar maka kana cikin wata sahara, bishiyoyi sun bushe, ganyayaki sun kade babu komai sai itace.

Da wuya ka yi tunanin wani abu zai iya tsirowa a wajen nan. Amma kauyen Tsimanananda ya fita daban a yankin.

Murmushin Loharano ya haskaka ko ina da wanda ke kusa da ita. Gajera ce, amma mai taushin hali, ba na jin idan za a zabi shugaba za ta zamo zabin farko.

Amma nan da nan da murmushi a fuskarta ta gayyace ni shiga farfajiyar gidanta, tare da cewa na saki jiki tamkar ina dakin tsohuwata.

"Mun sha wuya da bakar yunwa. Muna shuka amma duk lokacin da muka yi sam ba ta fitowa," in ji matar mai shekara 43, a lokacin da take mana bayani kan farin da suka fuskanta a shekarar 2013. Amma da taimakon kungiyar agajin yankin mai suna Agro-ecological Centre of the South (CTAS), a wannan karon komai ya sauya.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Jim kadan bayan isa ta gidan, Loharano ta jagoranci wani dan karamin ajin koyarwa a karkashin bishiyar bedi.

Tana nuna musu hotunan da ke jikin wasu manyan takardu, kan sabbin dabarun noma, tana magana ne da makwabtanta, da mijinta Mandilimana, tana kara shaida musu dabarun kaucewa fari da kuma yadda za a alkinta kasar yadda za a iya shuka.

'Muna da kalacin safe, abincin rana da na dare'

Cikin shekaru bakwai, kungiyar CTAS ta taimaka wajen gabatar da dabarun noman abinci dangin hatsi kamar gero, da sauransu wanda ke fitowa ya yi kyau busasshiyar kasa da aka yi wa dabaru tare da sanya taki mai kyau.

An koyawa mazauna kauyen yadda za su yi shuka ta fito ta yi yabanya, da kokarin kare su daga lalacewa.

"A yanzu, muna da kalacin safe, muna da abincin rana da dare," Loharano ta fada cikin alfahari, a lokacin da take nuna min gonarta, inda ita da mijinta Mandilimana suka noma kayan abinci mai yawa.

A wani bangaren gonar, an shuka gero, wani bangaren wake, wani bangaren kuma dankalin hausa.

"Muna cin gero da sikari, wanna abinci ne mai farin jini ga yara, cikinsu na cika taf da hatsi."

Kungiyar CTAS ta ce ta yi wannan aikin a kauyuka 14 na kudancin Madagascar tare da taimakawa iyalai 10,000.

Sai dai 'yar karamar kungiyar ba za ta iya tallafawa kowa da kowa ba saboda rashin isassun kudade.

Can a babban birnin kasar Ambovombe, alamun wani wuri da aka gama yaki ya nuna karara.

A wani katon fili mai cike da rairayi, iyalai daban-daban sun kafa tantina, akwai tarin gidan sauro, da buhunhunan kayan abinci da ledoji a gefe.

Wadannan mutanen da suka kai 400, sun tserewa bakar yunwar da yankunansu ke fama da ita.

Ba kamar Loharano ba, ba su samu damar yin noma ba, ba bu abinci, sun saida gonaki da dabbobinsu domin su tsira.

''Ya'yana hudu sun mutu'

Ba wai dukiya ko kadara kadai mutanen suka rasa ba.

Mahosoa, wanda ke zaune a sansanin da matansa da 'ya'ya 12, ya shaida min cewa 'ya'yansa hudu kanana ne suka mutu a farkon fara Farin shekaru uku da suka gabata.

"Yunwa ce ta kashe su a kauye. Daya bayan daya suka dinga mutuwa a kowacce rana. Mako guda mukai ba mu ci abinci ba, babu abinci ba mu da ko ruwan sha."

Asalin hoton, Sira Thierij/BBC

Bayanan hoto,

Mazauna sansanin Ambovombe sun tserewa yunwa a kauyukansu

Mahosoa ya shaida min wasu daga cikin 'ya'yansa na zuwa bara a garuruwa, su samu abin da za su sayi abinci.

Ya kara da cewa alkawarin agaji da gwamnati ta yi babu wanda ya zo gare shi.

Gwamnati ta rarraba kayan abinci ga yankunan da suka fi shan wuya, tare da sanar da gudanar da gwamman ayyukan ababen more rayuwa da za su sauya yankunan.

Sai dai duk da hakan Shugaba Andry Rajoelina na shan suka kan gazawar daukar matakin gaggawa kan fari da tashe-tashen hankulan da kasar ke ciki na shekaru, wanda fari ya samu wurin zama a Madagascar.

Wasu mazauna yankunan sun ce lamarin mai tsohon tarihi ne.

"A lokacin yakin kin jinin mulkin mallakar Faransa, mutanen yankin Antandroy [daga yankin da Androy ya fito] sun yaki masu mulkin mallakar Faransar, sun yi amfani da dabarun yaki," in ji wani malamin jami'a Dakta Tsimihole Tovondrafale.

Ya ce saboda wannan ne ya sanya Faransa ta dauke idonta daga yankin, ko yi musu aikin ci gaban kasa.

"Ba su yi tunanin yadda za su yi hanyoyi ba, ko haka rijiya, kuma har yanzu haka siyasar Madagascar ta ke tun bayan karbar 'yancin kai."

Yawancin masu sharhi kan lamuran siyasa na dora laifi kan gwamnati da tafiyar hawainiya wajen magance matsalar yunwa da kudancin kasar ke fama da ita, sai dai ministan muhallin Madagascar na kallon abin ta wata fuskar daban.

Dakta Baomiavotse Vahinala Raharinirina ya ce fari "ya samo asali ne daga sauyin yanayi". Wannan ya so ya yi kama da abin da shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana, kan cewa sauyi da dumamar yanayi na kara jefa duniya cikin matsalar fari.

A baya-bayan nan wani sananne kan yanayi a hukumar yanayi ta duniya, ya wallafa rahoto akan farin da Madagascar ke fama da shi, ciki har da aikin da Dakta Rondro Barimalala, wani kwararre kan yanayi ya yi, inda ya musanta cewa sauyin yanayi ne ya haddasa fari.

Masu bincike sun gano cewa, duk da an samu damuna mai albarka, da yiwuwar kasruwar fari, sauyin da aka samu na zubar ruwan samaba zai zamo shi kadai wajen ingiza sauyin yanayin da zai yi tasiri ga dan adam ba.

Map

Ko ma yaya lamarin yake kan ainahin illar da rashin zubar ruwa zai haddasa, tabbas dubun-dubatar mutanen da lmarin ke shafa na karuwa zai kuma ci gaba a shekaru masu zuwa.

A karkashin aikin da ta ke yi na inganta kasar noma a kauyen da ta ke shugabanci, Loharano na cike da farin cikin yadda al'ummar yankin suka kaucewa tashin hankalin da wasu yankunan Madagascar ke fuskanta na fari.

Sai dai abin da ciwo, ganin tarin wadanda ba su samu taimakon ba.

"Ina jin bakin ciki, ganin mutane na mutuwa saboda yunwa. Wata rana wani ba shi da komai, idan na tambayi dalili.

"Sai ta ce, saboda ba su da abin da za su ci, sun kwana ba su sanya ko kwayar hatsi a bakinsu ba. Sai na ce ta debe wani daga cikin waken da na noma ta kai wa 'ya'yanta su ci."