Hikayata 2021: Labarin 'Butulci' da ya zo na biyu
Hikayata 2021: Labarin 'Butulci' da ya zo na biyu
Latsa hoton sama don sauraron karatun labarin:
Wannan labarin haƙƙin mallakar BBC ne. Ba a yarda wani ko wata su yi amfani da shi ta ko wane salo ba, ko da yaɗa shi ne ta shafukan sada zumunta. Idan aka yi hakan kuma, to BBC za ta ɗauki mataki har da na shari'a.
BUTULCI
Dattijiwa da budurwar da suke sanye da fararan kaya nake kallo haɗe da mamakin abin da ya kawo ni duniyarsu, ban zan ce taɓa tozali da su a duniyata ba. Ƙara na saki sanadiyar raɗaɗin da ya ratsa dukkan sassan jikina lokacin da na yi yunkurin tashi zaune.
"Sannu 'yata!" Muryar dattijiwar ta ratsa masarrafar sautina yayin da take ƙarasowa inda nake.
Busasshen jinin da na yi tozali da shi a jikina ya haifar mini da mummunar faɗuwar gaba, sai a lokacin na fahimci a asibiti nake, kamar yadda na fara tuno ƙaddarar da ta faɗa mini, wacce ko makiyina ba na fatan ta gare shi.
Runtse idanuwana na yi hawaye suka fara tsere saman fuskata, ƙwaƙwalwata ta shiga hakaito mini komai garai-garai.
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
Na fi minti huɗu ina danna amsakuwwar motata, babu alamar maigadi zai buɗe mini ƙyauren gidana.
A matse nake na yi tozali da salulata wadda garin sauri kada na iske cinkoso a asibiti na manta ta a gida, ga shi ina da daɗaɗan albishirin da nake son isar wa maigidana wanda likita ya faɗa mini kasancewar ba ya gari.
Da hanzari na fita daga motar ina shiga ta ƙaramar ƙofa, na ci karo da maigadi yana bacci.
"Ikon Allah! Baba maigadi baccin hantsi ake sha." Na furta a fili.
Da kaina na buɗe kyauren ba tare da na tashe shi ba, kasancewar ban cika son katse wa mutum bacci.
Kafin na isa ma'adanar motoci na ji ana taɓa wuyana, cikin matuƙar tsoro na saki sitiyarin motar ina addu'a, a tunanina aljannu ne suke taɓa ni. Daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba.
Firgigit na farka daga bacci sakamakon ruwan sanyin da na ji a jikina. Ido na ƙura wa mutumin da na yi tozali da shi wanda nake da yakinin shi ya tayar da ni, kafin na ƙare wa matsakaicin ɗakin da na tsinci kaina kallo.
Da ƙyar na iya faɗin, "Waye kai? Ina ne nan? Me na yi maka ka sato ni?"
Maimakon ya ba ni amsa sai ya cilla mini baƙar leda haɗe da juyawa zuwa ƙofar ɗaki, kafin ya yi taku huɗu na sha gabansa. Cikin tsiwa na sake faɗin, "Malam tambayar ka nake yi!"
"Amsarki ko? Ni Ozil ne, nan ɗaki ne, amsar tambayarki ta uku bani da ita. Abinci aka umarce ni na kawo maki, in kin ga dama ki ci, in kuma kishiyarta matsalarki."
Kallon mamaki nake yi masa, kafin na ankara sai ƙarar rufe ƙofa na ji.
Hawaye masu zafi zuka zubo mini ina tunanin rashin imanin wanda ya sato ni, shakka babu an yi wa satar tawa shiri bisa la'akari da abin da ya faru da na riƙa tunowa a cikin kwanyata daki-daki.
Ranar farinciki a rayuwata an saka almakashi an datse mini shi, kasancewar zuwana asibiti likita ya tabbatar mini ina ɗauke da juna biyu.
Haka rayuwata ta ci gaba da tafiya cikin ƙunci da kunar zuciya, na gaji da zaman ɗakin nan, burina kawai na fita na koma gida kwatankwacin yadda makaho yake muradin ido.
Na yi baƙi, na rame tamkar wacce ta yi jinya. Na mayar da sambatu abincina matuƙar kewar dangina ta addabe ni.
"Bebina kana ganin za mu yafe wa wanda ya nisanta mu da babanka a lokacin da na san da wanzuwarka a duniyata? Kana ganin an mana adalci? Ina da yaƙinin babanka yana can cikin kewarmu, ina ma zai ji mu! Da ya cece mu ko bebina?"
Waɗannan jumlolin sun zame mini karatuna, ina yin su haɗe da shafa cikina.
Na kaɗa, na raya Ozil ya ƙi taimako na, a cewarsa abinci kaɗai aka ba shi damar kawo mini, abin haushi da taikaci tuwo da miyar karkarshi kowacce safiya.
Na ci wa kaina alwashi amfani da fasahata don kuɓuta daga gidan nan, kamar yadda aka yi amfani da hikima wajen sato ni.
Sai na daidaici lokacin zuwan Ozil, na zuba miyar karkashin da yake kawo mini daidai ƙofar ɗaki, na ƙara da ruwa yadda duk wanda zai taka sai ya faɗi. Allah da naSa iko Ozil yana shigowa ya faɗi ƙasa warwas!
Ban yi wata-wata ba na iso wajensa haɗe da shammatar shi ta hanyar amfani da gwiwar hannuna na daki bayan wuyansa.
Take ya sheme kasancewar daga an daki mutum a wajen yakan suma na wucin gadi.
Da sauri na lalubi waya a aljihunsa, na ci sa'ar samun kuɗi bayan wayar.
Sauri-sauri na rufe sa a ɗakin na fice da gudu, sai da na yi tafiya mai nisan gaske sannan na fara tozali da ɗaiɗaikun mutane suna shawagi saman ababen hawa, a lokacin ƙarfina ya ƙare, ga shi tun fitowata daga ɗakin nake ƙoƙarin kiran mijina amma babu sabis.
Jiri ya kwashe ni na zube, duk yadda nake muradin ƙara taku amma na kasa! Sai na fashe da kuka gwanin ban tausayi ina rarrafe tsoro ya cika mini zuciya, ban damu da ciyawa da ƙayoyin da suke sukar mini jiki ba, burina na yi tozali da wanda zai taimaka mini.
Allah da naSa iko sai ga motar matafiya, ina tsayar da su suka tsaya, ba mu tsaya ko'ina ba sai tashar garinmu. Daga nan na tari mai a-daidaita-sahu sai gidana.
Kamar beben da ya ga ɓataccen karensa haka mai gadi ya bi ni da kallo irin na mamaki. "Hajiya ke ce kika dawo?" Ya yi mini tambayar cike da farincikin gani na.
Da yake hankalina gaba ɗaya ya yi ciki, ba wata gamsasshiyar amsa na ba shi ba, ya ba ni hanya na wuce.
Duk taku guda zuwa falon bugun zuciyata ƙara tsananta yake, kewa da muradin ganin mijina sun cika mini zuciya na matsu na yi tozali da kyakyawar fuskarsa.
Da karfi na ci burki daidai falon sakamakon tashin amsa-amon muryar da nake kewa da bege da take ratsa ni.
Sai dai ba a ɗauki wani lokaci ba na ji muryar ta fara yi mini wani irin ɗaci, saboda mugayen kalaman da take furzarwa masu kamar ruwan darma a kunnena.
"Da alama mahaifin Fatima so yake na shafe babinta a doron ƙasa don ya fiye taurin kai da yawa.
Tunda na sa aka yi kidinafin ɗinta mun buƙaci ya bayar da kuɗaɗe amma ya tsaya yana neman jan zancen, yana so ya shigo mana da jami'an tsaro cikin harkar.
Hello kina ji na!" Ya ɗan tsahirta, da alamu magana wacce suke wayar take yi masa don kalamansa na ƙarshe suka tabbatar mini waya yake. Damar da ni ma na samu kenan na fara naɗar sautinsa da wayar Ozil ta hannuna.
"A'a kada ki damu ai mun yi kyakkyawan shirin da asirinmu ba zai taɓa tonuwa ba. Dama fa na sa an yi kidinafin ɗinta ne don na samu kuɗin aurenki, amma kuma mun saka masa kuɗin fansar ya tsaya yana jan ƙafa." Ya sake yin shiru da alamu yana sauraron maganar wacce suke waya.
"Kada ki damu insha Allahu babu matsala, yanzu ma na canza shawara muna karɓar kuɗin fansarta zan sa su Ozil su ƙara mata gudu gari mai arahar gyaɗa, kin ga shikenan ke sai na samu kuɗin aurenki, mu yi auren mu babu wacce za ta takura mana." Ya sake yin shiru.
"Don Allah farka daga baccin da kike yi, kin fi kowa sanin na auri Fatima don na mallaki dukiyar babanta bayan na kawar da shi.
Ganin kawar da shi ɗin ta gagara ne kawai muka shirya wannan ɗauke ta ɗin don na yagi rabona na sallameta.
A duniyata ke kaɗai nake yi wa kallon mace, saboda kasancewarki mafarkina kuma muradina, ina miki albishir zan shayar da ke soyayya har ƙarshen numfashina."
Jin ƙafafuwana suna barazanar kasa ɗaukata ya sa na fara tunanin bai kamata na bari Samir ya san na dawo gidan ba.
Don haka da sauri na bar gidan sai gidanmu, cikin kuka na faɗa jikin mahaifiyata.
Ban ɓata lokaci ba na kunna mata rikodin ɗin da na yi wa Samir, ta razana sosai da mamakin butulcin Samir.
Babu ɓata lokaci babana ya tura 'yan sanda aka yi awon gaba da shi, ba a sha wahalar shari'a ba saboda muryar Samir da muke da a hannu, sannan an samu lambar Ozil a wayarsa da duk irin yadda suka tsara komai.
A hanyarmu ta dawowa daga kotu ne aka samu wasu suka kawo mana farmaki, ni dai tunda na ji shigar wani ƙarfe mai wuta a kafaɗata sai yanzu da na farka na ga ma'aikatan jinya a kaina.
"Ina iyayena?" Na yi musu tambayar a kasale.
"Ga mamarki nan, Abbanki yana can ɗakin maza cikin kulawa shi ma." Muryar ƙanwar mamata ta ratsa ni.
Ina waigawa na ga mahaifiyata a wani gado ƙanwarta zaune kusa da ita.
"Abin farinciki ma an samu nasarar kama waɗanda suka yi muku haka, bincike ya tabbatar yaran butulun mijinki ne ." Ta sake faɗi.
A raina ina mamakin yadda wai miji zai iya cutar da matarsa. Karona na farko da na ji lallai ba a banza aka samar da karin maganar NAMIJI ƘARIN KUNAMA ba.
Ƙarshe