Wane tasiri kauracewar difilomasiyya za ta yi kan wasanni Olympics na Beijing 2022?

  • Daga Dan Roan
  • BBC Sports Editor
Dan sanda na magana ta wayar salula, ya yin da wani mai gwagwarmaya dan Tibet, da daliban kungiyar 'yantar da al'ummar Tibet ke daga kyallen da ke nuna rashin goyon bayan China karbar bakuncin gasar hunturun ta 2022, a shalkwatar kwamitin gasar da ke Beijing

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Masu zanga-zangar na so amfani da lokacin gasar wajen yada manufarsu

Yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan yadda ake take hakkin dan adam wanda ya zamo kusan taken 'yan wasanni a shekarun nan, wasu daga cikin masu masu karbar bakuncin wasanni sun fara fusata mutane kamar yadda China ke janyo ce-ce-kuce.

Kasar da za ta karbi bakuncin gasar Olympics ta lokacin hunturu a 2022 na fuskantar turjiya, sakamakon kasashe kamar Amurka, da Australia, da Birtaniya sun kauracewa halartar wasan, saboda yadda gwamnatin China ke gallazawa da cin zarafin tsirarun kabilar Uyghur.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam da gwamnatocin kasashen yammacin duniya, na zargin China da kisan kare dangi a yankin Xinjiang.

Sai dai China ta musanta hakan, tare da cewa sansanin da ta ke tsare da mutanen ana kokarin sauyawa Musulmai na kabilar Uyghur masu tsaurin ra'ayi tunani.

Haka kuma, dangantaka tsakanin kasar da kasashen duniya ta yi tsami, sakamakon yadda take taka rawa da yi wa dimukradiyya kafar ungulu a yankin Hong Kong, da kuma damuwar da ake nunawa a baya-bayan nan kan 'yar wasan tennis 'yar China Peng Shuai, wadda ta ɓata ɓat daga idanun jama'a bayan ta zargi wani babban jami'in kasar da cin zarafinta ta hanyar lalata da ita.

Duk da cewa hukumomin China sun soki yadda ake yada batun an tsare ta ba da son ranta ba da sauran batutuwan take hakkin dan adam, amma batun na ta na ci gaba da zama abin damuwa.

Ga kalilan daga cikin shugabannin kasashen yammacin duniya da suka bayyana cewa wakilansu ba za su halarci wasannin Olympics, ana kallon hakan a matsayin mai saukin dauka, yayin da kauracewa abubuwa irin hakan wani mataki ne da ke sanya 'yan wasa kauracewa zuwa baki daya.

Ba sabon abu ba ne daukar matakin. Shekaru uku da suka gabata kasashen Turai ciki har da Birtaniya suka sanar da janye jami'an diflomasiyyarsu a lokacin gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha, bayan harin da aka kai Salisbury da gubar Novichok.

Hadarin da ke cikin aike 'yan siyasa Beijing domin halartar gasar na nuna kamar an bai wa gwamnatin Shugaba Xi Jinping wata dama ta ci gaba da cin karansu babu babbaka, wanda ke kallon gasar da matakin daukaka ga kasar wajen karbar bakuncin ta.

Yayin da China ke zargin Amurka da amfani da siyasa wajen shirya mata makarkashiya, ta sha alwashin daukar matakin da ya dace.

Sai dai babu alamun hakan ya zo da mamaki, musamman ganin kasashen Italiya da Faransa sun ki amincewa kauracewa China, inda shugaba Macron ya ce matakin ba shi da wani amfani.

Sai dai watakil ya dan yi tasiri ga wadanda za su shiga filayen wasannin da za a gudanar da kasar.

Yayin da gamayyar kungiyar 'yan kabilar Tibet, da Uyghur, da Kudancin Mongolian, da yankin Hong Kong, da masu rajin kare hakkin dan adam na Taiwan da suka hada karfi tare da fitar da maudu'in #NoBeijing2022, sun yi maraba da wannan matakin.

Yawancin masu fafutuka na ganin wannan ya yi kadan, kamata ya yi su ma 'yan wasan da za su zo daga kasashe wajen China su dauki irin matakin, haka masu daukar nauyi, da 'yan jarida domin a matsawa China lamba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masu rajin kare hakkin dan adam sun yi kiran a kauracewa China

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wasu na tambayar ko cikakken kauracewa gasar wasan na hunturu ya dace a yi a halin yanu, musamman a kasar da ake zargi da kisan kare dangi, yauhe komai zai sauya?

Hakika kungiyar mata masu wasan tennis ta duniya (WTA), ta sha yabo a yammacin duniya, kan daukar matakin gaggawa na janyewa daga gasar, kan ci gaba da nuna rashin jin dadi da abin da ya samu Peng Shuai, wani misali da ba safai ake ganin kungiyar wasanni sukutum guda suka dauka kan wata mamba cikinsu.

Kin shiga a dama da su a gasar Olympics, ka iya zama wata karin hanyar wayar da kai da nunawa duniya irin abubuwan da China ke yi da ke janyo mata zarge-zarge da ake yi mata.

Amma wadanda suke sukar matakin, na ganin tamkar yakin cacar baka ne ya barke tsakanin China da kasashen kamar yadda ya faru a shekarun 1980 da 1984, wanda ya dan yi tasirin siyasa, karshe kuma lamarin ya shafi 'yan wasa.

Su kuma sauran na ganin shigen matakin da aka dauka a zamanin yaki da wariyar launin fata a kasar Afirka ta Kudu tsakanin shekarun 1970 zuwa 1980 a bayyane ta ke karara mataki irin hakan ka iya janyowa kasa sauya wasu daga cikin tsare-tsarenta.

Sai dai wasu na ganin maimakon kauracewa wasanni irin wannan kamata ya yi a ba su kwarin gwiwa, da amfani da harkokin diflomasiyya wajen ganin an magance matsalar.

Wannan shi ne batun da FA ta kare a lokacin da aka soki matakin bai wa Qatar bakuncin wasan kwallon kafar duniya a shekarar 2022, kasar da duk da sauye-sauyen da aka yi, har yanzu ana take hakkin ma'aikata musamman 'yan kasar waje,da haramta luwadi, wanda shi ne babban abin da ke damun kungiyoyin kare hakkin dan adam.

A wata sanarwa da hukumar kwallon kafa ta FA ta fitar ta ce "Kamar yadda muke nunawa, mu na son anin an samu wata dama ta tattaunawa, da ganin an kawo sauyi a Qatar d ma kasashe makofta da ke yankin Gabas ta Tsakiya, inda ake ci gaba da fuskantar zarge-zargentake hakkin dan adam."

Sai dai da alama ba kowa ya aminta da hakan ba. Yayin da lamarin janyewa daga halartar gasar wasan Olympics da ke Beijing ke karbar bakunci a shekara 2022, ba abun mamaki ba ne idan masu fafutuka sun sake yunkurowa kamar yadda suka yi a shekarun da suka gabata.

Inda za su nemi daga murya kan hakkin mata, da na musulmai na kabilar Uiyghur har da batun muhalli da sauyin yanayi.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Batun Peng Shuai ya ja hankali da allawadai daga sassa daban-daban na duniya

'Yancin fadar albarkacin baki na samuwa ne kadai a wuraren da aka aminta, shafukan sada zumunta na takaita batutuwan da suka shafi gwamnati, sai dai hatta 'yan wasa ba su da ikon hakan a kasar da ta yi kaurin suna wajen daukar mataki kan masu aikata hakan.

Musamman bayan shugaban hukumar WTA Steve Simon a baya-bayan nan ya ce lamari ne mai matukar daga hankali, kan hadarin da 'yan wasa ke fuskanta da wanda za su fuskanta a lokacin China za ta karbi bakuncin gasar a shekarar 2020.

Wani dan wasan kwallon kwando Enes Kanter, ya janyo gagarumar magana bayan sukar Shugaba Xi, tare da nuna goyon baya ga kungiyar 'yantar da yankin Tibet a watan Oktoba.

Tuni aka cire da soke sunansa daga fitaccen shafin sada zumunta na kasar Weibo, aka kuma cire sunansa daga 'yan wasa.

Har wa yau, an dakatar da nuna wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, tashar talabijin din China a shekarar 2019, bayan tsohon dan wasan tsakiyar kungiyar Mesut Ozil ya yi tsokaci kan yadda ake cin zarafin musulmai na kabilar Uyghurs.

Kungiyoyin rajin kare hkkin dan adam sun roki hukumar IOC ta nemo wata kasar da za ta karbi bakuncin gasar Olympics.

Sai dai danbarwar da ke lullube cikin bakuncin da Beijing za ta karba na da yawa, lamarin ya janyo ayar tambaya kan wadanda za su dauki nauyin gasar, da dangantakarsu da China da sauransu.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch, ta zargi IOC da hada kai da shugaban China Xi bayan shugabanta Thomas Bach ya yi tattaunawar bidiyo da 'yan wasan tennis ta China Miss Peng a wani abu da ake ganin mataki ne da IOC ta yi na taimakawa kasar binne abin da ke kasa.

Sai dai hukumar ta musanta wannan zargi.

IOC na cewa, "babu wata rawa da ta ke takawa wajen sauyin siyasar kasar, ko sauya yadda duniya ke kallon China a lokacin da muka bai wa kasar damar karbar bakuncin wasan wanda ta fafata da wasu kasashen kuma an bi dukkan tsari da dokokin da ya kamata."

Koma dai yaya ta kaya, ba zabin 'yan wasa ba ne zuwa Beijing domin gasar, yayin da kuma rikicin siyasa ke kara tsami, ana ci gaba da yin matsa lamba, kuma su ne ke han tambayar ko ya dace su yi wasa a kasar, an kuma bar su da zabi mai wuyar sha'ani kn matakin da za su dauka da zarar sun shuga kasar China.

Da dama na ganin an sanya su a tsaka mai wuya.