An soke shirin gina dandalin fim a Kano

Muhammadu buhari Hakkin mallakar hoto State House
Image caption Batun gina katafaren dandalin shirya fina-finan ya janyo cece-kuce.

Gwamnatin Najeriya ta soke shirinta na gina katafaren dandalin shirya fina-finai a jihar Kano sakamakon adawar da jama'a suka nuna.

Mai bai wa Shugaba Muhammadu Buhari shawara kan harkokin majalisar wakilai, Kawu Sumaila, ya ce shugaban ya saurari koken jama'a musamman malaman addini da suka nuna adawa da lamarin.

Ya kuma nemi masu sana'ar fim da su fahimci halin da gwamnati ta tsinci kanta a ciki.

Batun gina dandalin, wanda aka tsara yi a kauyen Kofa, ya fuskanci suka daga sassa da dama na jihar, inda malamai suka rinka sukar shirin a masallatan Juma'a.

Kazalika kafafen yada labarai sun cika da muhawara kan lamarin, wanda aka shirya zai lashe makudan kudade.

Shi dai Kawu Sumaila ya ce tun asali dama ba Shugaba Buhari ne ya bayar da umarnin gina dandalin ba ko kuma ya ce a sanya sunansa.

Dan majalisar tarayya ne da ke wakiltar yankin ya nemi a yi, ita kuma hukumar shirya fina-finai ta yi yunkurin aiwatarwa saboda yana cikin kasafin kudi na bana.

'Raddi'

Sai dai wani fitaccen jarumi kuma daraktan fina-finan Kannywood, Falalu Dorayi, ya shaida wa BBC cewa ba su ji dadin soke gina dandalin fim din ba, yana mai cewa mutane sun yi wa shirin gurguwar fahimta.

A cewarsa, "Ya kamata mutane su sani cewa dandalin ba wurin holewa ba ne; wuri ne da za a dauko kwararren mutum a ba shi shugabancinsa, kamar yadda aka yi a hukumar tace fina-finai. Za a bar 'yan fim su gina garuruwa ta yadda duk rawar da za a taka a kowanne fim ba sai an je wani wurin ba za a yi a can. Mutane ba su tambayi yadda za a gudanar da wurin ba, amma suke ta sukar shirin."

Ya kara da cewa da an gina dandalin da dubban mutane sun samu ayyukan yi.

Labarai masu alaka