Ya kubuta daga gawurtaccen kada a Australia

Gawurtaccen kada a kasar Australia Hakkin mallakar hoto
Image caption Gawurtaccen kada a kasar Australia

An ceto mutumin nan da ya shafe kwanaki uku a wani tsibiri, bayan da wani gawurtaccen kada ya kai masa farmaki a kasar Australia.

Mutumin ya makale har na tsawon kwanaki uku bayan da kadan ya rutsa shi ya kuma kafa hakoransa a cikin kwale-kwalen mutumin.

Ya ce ya samu tserewa zuwa kan tsibirin dake gabar tekun Queensland, bayan da ya rika wani irin tuka kwale-kwalen cikin saurin da bai taba yin irin sa ba.

Rashin kyaun yanayi da kuma karancin kadawar igiyar teku ce ta hana shi barin tsibirin.

Da safiyar Asabar ne dai masu aikin ceto a jirgi mai saukar angulu suka kubutar da shi daga tsibirin.