Zanga-zanga: An toshe kafofin sada zumunta a Habasha

Hakkin mallakar hoto AFP

Tun a daren Jumma'a ne hukumomi a kasar Habasha suka toshe kafofin sada zumunta sakamakon zanga-zangar da ake gudanarwa a wasu sassan kasar.

Daruruwan masu zanga-zangar ne dai suka yi fitar dango da sanyin safiya a babban dandalin birnin Addis Ababa dauke da kwalaye suna rera wakokin nuna kin jinin gwamnati.

Sun kuma yi kiran da a kawo karshen abinda suka kira kisan al'ummarsu da kuma mutunta 'yancin biladama.

'Yansanda a birnin na Addis Ababa sun tarwatsa masu zanga-zangar ,tare da cafkewa da kuma lakadawa da dama duka da jkkata wasu.

Wasu rahotanni sun ce an gudanar da irin wannan zanga-zanga a garuruwa da dama a Oromia, yanki mafi girma a kasar da kuma birnin Gondar dake arewacin kasar.

Mazauna yankin na Oromia sun yi ikirarin cewa an hallaka daruruwan mutanensu yayinda aka jikkata dubbai, tun bayan da zanga-zangar ta fara a cikin watan Disambar bara.

Labarai masu alaka