Nigeria: An sace 'yan kasar China 2 a jihar Nassarawa

Hakkin mallakar hoto Getty

'Yansanda a jihar Nasarawa Nijeriya sun ce wasu 'yan bindiga sun sace 'yan kasar China biyu dake aiki a wani kamfanin hakar ma'adinai.

Kakakin rundunar 'yansanda a jihar Numan Umaru Isma'ila shaidawa BBC cewa, da misalin karfe biyu da minti rabi na ranar Jumma'a ne 'yan bindigar da suka far wa mutanen, a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Abuja daga kauyen Ajada.

Ya ce mutanen XJieng AI Jung mai shekaru 50, da Wenso Ping mai shekaru 45 na tafiya tare da wani jami'n tsaro, wanda shi kuma suka harba a kafa, kuma yanzu haka ana yi masa magani a wani asibiti.

Rundunar 'yansandan ta ce ta tura jami'anta cikin dazuka domin farautar 'yan bindigar, tare da hadin guiwar wasu 'yan banga da kuma shugabannin al'ummar yankin.

Labarai masu alaka