An fatattaki mayakan I-S a Syria

Birnin Manbij na kasar Syria
Image caption Dakarun Syria sun kwato birnin Manbij

Dakarun da Amurka ke mara wa baya a arewacin kasar Syria sun kwato ikon kusan daukacin birnin Manbij daga hannun mayakan IS.

Hadakar dakarun Kurdawa da sojojin sa kai na sun yi ta fafatawa har na tsawon makonni don kwato muhimmin yankin dake kusa da kan iyakar kasar Turkiyya.

Sannu a hankali ne dai suka kutsa kai cikin birnin.

Kungiyar dake sa ido kan kare hakkin biladama dake da mazauni a Birtaniya ta ce wasu yan tsirarun mayakan na I-S din ne kawai suka rage a tsakiyar birnin na Manbij.

Kwace wannan yanki mai matukar muhimmci ka iya zama wani babban koma baya ga kungiyar ta I-S.

Labarai masu alaka