Gudunmawar Bollywood ga kasar India

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption India ta samu 'yancin kai ne a shekarar 1947

A ranar 15 ga watan Agusta ne kasar Indiya ta ke bikin murnar samun 'yanci kai daga turawan na Ingila, mulkin mallakar da ya zo karshe a shekarar 1947.

Indiya dai ta samu 'yancin kai bayan fadi-tashin da wasu 'yan gwagwarmaya suka shafe tsawon lokaci suna yi.

Mutane irinsu Gopal Krishna Gokhale, su ne suka fara kaddamar da kiraye-kiraye ga al'ummar kasar da su fito su bayyana bukatarsu ta samun 'yancin kai, lamarin da ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi.

A duk rana irin ta yau firai ministan da ke kan mulki na daga tutar kasar tare da yin jawabi ga miliyoyin Indiyawa, hakan wata al'ada ce da kasar ta gada daga wajen firai ministan farko, Jawaharlal Nehru.

Gwagwarmaya

A shekarar 1929, jam'iyyar National Congress ta ayyana ranar 26 ga watan Janairu a matsayin ranar samun 'yancin kasa, sai dai ta rika yin taruka a boye saboda gudun fushin Ingila.

Haka aka rika tafiya har zuwa lokacin da Mohandas Karamchand Ghandi, ya dawo kasar sakamakon kiransa da manyan 'yan siyasar kasar suka yi na ya zo domin ya taimaka musu a kawo karshen mulkin mallaka.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mahatma Ghandi ya taka muhimmiyar rawa wajen samun 'yancin kai na India

Zuwan Mahatma Ghandhi ne ya sauya tafiyar siyasar kasar, kasancewarsa mutum mai tsananin son zaman lafiya da daidaito ta fuskar zamantakewa, ya shiga gaba don tabbatar da cewa turawa sun daina matsawa Indiyawa ta fuskar haraji da bautar da su da sauran su.

Sai dai yunkurin da 'yan jam'iyyar National Congress suka fara na ganin Indiya ta samu 'yanci, ya samu tsaiko a lokacin da yanki Pakistan mai rinjayen Musulmai ta ki amincewa da zama karkashin Indiya, ta kuma yi yunkurin ballewa kwata-kwata.

Yunkurin Pakistan ne ya raba hankulan turawa, suka rasa ta inda zasu fara, saboda haka aka jibge sojoji a tsakanin Pakistan da Indiya domin ganin an dakile 'yan fafutukar, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane miliyan daya.

Daga bisani turawa sun ayyana Pakistan a matsayin 'yantacciyar kasa a ranar 14 ga watan Agusta, 1947, watau ta girmi Indiya da kwana daya wajen samun 'yanci.

Duk da alkawura da Gwamnan Indiya Clement Attlee ya yi, na cewar za a bai wa kasar 'yanci a watan Yunin 1948, manyan 'yan siyasa sun ki amincewa da bukatarsa, inda a daren ranar 15 da misalin karfe 11 na dare, suka hadu domin bayyana matsayarsu kan gwagwarmayar da ake ta yi ta samun 'yanci.

Cikin wadanda suka halarci zaman akwai shugaban kasa Rajendra Prasad, da wasu manyan kungiyoyi na mata.

Gaba daya mahalarta taron sun mika kansu don ganin an fitar da kasar daga kangin talauci, fatara da kuma bauta.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jawaharlal Nehru shi ne Firaministan India na farko bayan samun 'yancin kai

Firai minista Jawaharlal Nehru, ya yi jawabi mai ratsa zuciya a taron, inda ya rika karfafa gwiwa kan muhimmanci tashi domin a kwaci 'yancin kai.

Haka kuwa aka yi, washegari dole turawa suka ayyana Indiya a matsayin 'yantacciyar kasa don kaucewa asarar rayukan da aka kwashe watanni ana yi.

Amma duk da haka kasar ba ta fara aiki da kundin tsari na kashin kai ba sai a ranar 26 ga watan Janairun 1950.

Shugabannin farko

Bayan samun 'yancin ne, al'umma kasar suka rika kiran sunan Mahatma Ghandi da jinjina masa sakamakon irin gudunmuwar da ya bayar a nasarar da aka samu.

Wasu na bayyana sunansa a matsayin sabon shugaba, sai dai a nasa bangaren, ya nuna sam bai sha'awar mulki, sai ma kira da ya yi ga al'ummar kasar mabiya addinin Musulunci, mabiya addinin Hindu da mabiya addinin Sikh da su yi hakuri, su zauna lafiya da juna.

Daga bisani aka nada Jawaharlal Nehru firai minista, sai kuma Lord Mountbatten a matsayin Gwamna (kafin kudin tsarin mulkin kasar ya fara aiki).

A bangaren Pakistan kuma aka rantsar da Muhammad Ali Jinnah a matsayin Gwamna.

Tattalin arziki

Tattalin arzikin India a kullum yana habaka ne ta hanyar kimiyya da fasaha da likitanci da kuma harkar fina-finai.

Bangarorin kimiyya da kiwon lafiya kawai na bayar da kaso 35 cikin dari ga tattalin arzikin kasar.

Kasar ta Indiya na kwararrun likitoci wadanda ke aiki asibitoci daban-daban na duniya, yayin da kasar ke da asibitoci da kayan aiki na zamani, lamarin da yasa dumbin mutane, musamman daga kasashe masu tasowa ke zuwa kasar domin neman magani.

Har ila yau kasar ta yi fice wajen samar da magunguna a duniya.

Wannan bangaren ma yana taimakawa kasar wajen bunkasa tattalin arzikinta.

A bangaren kere-kere kuwa, India tana kera ababen hawa kamar su Jirgin sama da motoci da babura da kuma kekuna.

Kuma ana fitar da irin wadannan kayayyaki zuwa kasashen ketare, wanda a bangaren na kere-kere kawai India na samun kaso 45 cikin dari na kudaden shigarta. Sai kuma bangaren fina-finai wato na Bollywood.

Bollywood

Bayan harkar fina-finai ta Amurka, wato Hollywood, Bollywood shi ne na biyu a duniya.

Fina-Finan Bollywood na taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar, domin yana bayar da kaso 5.1 cikin dari ga tattalin arzikin kasar, baya ga samar da ayyukan yi ga dumbin matasa.

Image caption Shahrukh Khan na daya daga cikin jaruman fina-finan Bollywood da suka yi fice a duniya

A duk shekara masana'antar Bollywood tana samar da kudin shiga akalla dala biliyan takwas, ko fiye da haka ga Indiya.

Baki daya Indiya na samun kudaden shiga kusan dala tiriliyan biyu daga wadannan hanyoyi uku.

Labarai masu alaka