Pakistan:An gano jirgin da ya bata a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto AFP

Kasar Pakistan ta sanar da gano jirgi mai saukar angulu mai daukar mutane shida da ya yi batan dabo a Afghanistan kwanaki tara da suka gabata.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta ce yan kasar Pakistan da matukinsu dan kasar Rasha, sun isa birnin Islamabad bayan kubutar da su da aka yi ta hanyar musaya a kan iyaka.

Jirgin ya yi saukar gaggawa ne a yankin dake karkashin ikon kungiyar Taliban dake Afghanistan.

Akwai rahotannin da ba a tabbatar da su ba da ke cewa yan Taliban ne suka rike mutanen, duk da cewa Pakistan din bata tabbatar da hakan ba.

Labarai masu alaka