Abubuwa nawa za ku tuna a shekarar 2018?

Ga kacici-kacici

Amsoshin na kasa

Tambaya 1/12

Wace waka ce Umar M Shariff ya fi so?

1. Mariya
2. Madubin Dubawa
3. Jirgin Soyayya
4. Jinin JikinaTambaya 2/12

Wace Daula ce a Najeriya Sayyidina Umar ya taba aika sako?

1. Daular Borno
2. Daular Sakwatto
3. Masarautar Kano
4. Masarautar ZazzauTambaya 3/12

Nawa aka sako daga ‘yan matan Dapchi da aka sace?

1. 107
2. 105
3. 106
4. 104Tambaya 4/12

Wane dan siyasar Najeriya ne yace ya tuba da yin magudin zabe?

1. Sanata Dino Melaye
2. Honarabul Abdul-Aziz Namdaz
3. Sanata Ibrahim Mantu
4. Sanata Bukola SarakiTambaya 5/12

Wane gwamnan Najeriya ne ya zagi sanatocin jiharsa a bainar jama'a?

1. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje
2. Gwamna Kashim Shettima
3. Gwamna Ayodele Fayose
4. Gwamna Nasir Ahmed El-Rufa'iTambaya 6/12

Wace kasa ce ta fitar da Najeriya daga gasar cin kofin duniya ta 2018?

1. Argentina
2. Rasha
3. SenegalTambaya 7/12

Wace kungiyar kwallon kafa ce ta sayi gola mafi tsada a duniya?

1. Liverpool
2. Manchester United
3. Leicester City
4. ArsenalTambaya 8/12

Wane jigon Boko Haram aka kama a wannan watan?

1. Maje Kabir
2. Maje Yusuf
3. Maje Lawal
4. Maje IsaTambaya 9/12

Me yasa aka rufe filin jirgin sama na Abuja?

1. Saboda gyara
2. Saboda hatsari
3. Saboda ruwan sama
4. Saboda shugaban kasaTambaya 10/12

A ina aka gano gawar Janar Idris Alkali?

1. Du
2. Gushwet
3. Jos
4. Barikin LadiTambaya 11/12

‘Yan mata nawa ‘yan boko haram suka sace a Nijar a wannan watan?

1. 13
2. 14
3. 15
4. 16Tambaya 12/12

Me yasa ma'aikaciyar BBC ta kashe kanta?

1. An kore ta aiki
2. Mijinta ya mutu
3. Matsalar damuwa
4. Albashinta ya yi kadanAmsoshi

1. Wace waka ce Umar M Shariff ya fi so?

amsa: Jirgin Soyayya

Umar ya ce duk a wakokin da ya yi, ya fi son wakar Jirgin Soyayya wacce aka yi a fim din Mansoor.


2. Wace Daula ce a Najeriya Sayyidina Umar ya taba aika sako?

amsa: Daular Borno

Daular Borno ta yi zamani da Sahabbai, kuma masanin tarihi Alhaji Zanna Hassan Boguma ya ce daular ta kafu ne tun kafin zuwan Annabi SAW.


3. Nawa aka sako daga ‘yan matan Dapchi da aka sace?

amsa: 104

Gwamnatin Najeriya ta ce 'yan matan sakandaren Dapchi 104 kungiyar Boko Haram ta sako.


4. Wane dan siyasar Najeriya ne yace ya tuba da yin magudin zabe?

amsa: Sanata Ibrahim Mantu

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ibrahim Mantu, ya ce yana da hannu cikin magudin zabukan da aka yi a baya amma ya ce ya tuba daga aikata magudin zabe.


5. Wane gwamnan Najeriya ne ya zagi sanatocin jiharsa a bainar jama'a?

amsa: Gwamna Nasir Ahmed El-Rufa'i

Gwamna Nasir Ahmad el-Rufai ya zargi Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hunkuyi da Sanata Danjuma Laah da hada baki domin hana majalisar dattawan Najeriya amincewa da bukatarsa ta cin bashi daga Bankin Duniya inda ya ce "wadannan dattijan [sanatocin Kaduna] banza ne... domin su makiyan jihar Kaduna ne, ba sa son ci gaban jihar."


6. Wace kasa ce ta fitar da Najeriya daga gasar cin kofin duniya ta 2018?

amsa: Rasha

Argentina ta cire Najeriya daga Gasar Cin Kofin Duniya, inda Najeriyar ta samu maki uku,kuma matsayi na uku a rukunin D, abin da ya fitar da ita daga Gasar Cin Kofin Duniya a kasar Rasha


7. Wace kungiyar kwallon kafa ce ta sayi gola mafi tsada a duniya?

amsa: Liverpool

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta sayi golan Roma, Allison a kan fam miliyan 66.8 (Yuro miliyan 72.5), abin da ya sa ya zama golan da ya fi tsada a duniya.


8. Wane jigon Boko Haram aka kama a wannan watan?

amsa: Maje Lawal

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta cafke Maje Lawan a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke garin Banki a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.


9. Me yasa aka rufe filin jirgin sama na Abuja?

amsa: Saboda gyara

Hukumar kula da filayen jiragen saman Najeriya (FAAN) ta ce an bude filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, bayan rufe shi da aka yi na wasu sa'o'i sakamakon wani hatsari.


10. A ina aka gano gawar Janar Idris Alkali?

amsa: Gushwet

Rundunar sojojin Najeriya ta gano gawar Janar Idris Alkali mai ritaya a wata rijiya da ke Gushwet a gundumar Shen ta karamar hukumar Jos South a jihar Filato.


11. ‘Yan mata nawa ‘yan boko haram suka sace a Nijar a wannan watan?

amsa: 15

Wasu 'yan bindiga da ake tunanin 'yan Boko Haram ne sun sace 'yan mata 15 a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin Nijar.


12. Me yasa ma'aikaciyar BBC ta kashe kanta?

amsa: Matsalar damuwa

Vicki Archer, 41, 'yar kimanin shekara 41, na da matsalar damuwa kuma sau biyu tana yunkurin kashe kanta, in ji wani bincike da wata kotu ta yi.


 • JAN
 • FEB
 • MAR
 • APR
 • MAY
 • JUN
 • JUL
 • AUG
 • SEP
 • OCT
 • NOV
 • DEC

Abubuwa nawa za ku tuna a shekarar 2018?

Ga kacici-kacici

Maki:
Kun samu