Gane mini hanya 28/09/2019
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane mini hanya: Ilimi a jihar Yobe

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren shirin gane mini hanya

Harkar ilmi a Najeriya na daga cikin batutuwan da a kodayaushe ake kokawa a kasar ganin yadda bangaren ya shiga cikin wani mawuyacin hali.

Jihar Yobe da ke arewacin kasar, na daga cikin jihohin da ke fuskantar wannan kalubale, kuma a sakamakon haka ne Gwamnan jihar, Mai Mala Buni ya yi shelar ta-baci kan harkar ilimi, bayan hawansa kan karagar mulki.