Gane Mini Hanya 22/02/2020

Gane Mini Hanya 22/02/2020

Latsa lasifikar da ke sama don sauraron shirin:

A makonnin baya ne muka samu bakuncin wasu malaman Jami'ar Bayero ta Kano a ofishin Sashen Hausa na BBC da ke London.

Malaman, karkashin jagorancin Farfesa Umar Pate sun zo ne da nufin hada karfi da Sashen Hausa na BBC wajen gudanar da ayyukan yada labarai.

Ziyarar na zuwa ne bayan da Hukumar Jami'o'i ta kasa NUC ta rarraba karatun aikin jarida har zuwa gida bakwai wajen samun digiri a jami'o'i.

A kan haka ne Umaymah Sani Abdulmumin ta tattauna da Farfesa Umar Fate, shugaban Tsangayar Sadarwa a jami'ar Bayero ta Kano, domin jin karin bayani kan rabe-raben.