Lafiya Zinariya: Me ke sa mata kunzugu da tsumma ko safa?

Latsa hoton da ke sama don jin cikakken shirin:

Mata, musamman wadanda suka fito daga gidajen marasa galihu na fuskantar barazanar kamuwa da wasu cututtuka, saboda rashin samun abubuwan da suka dace su yi amfani da su wajen kula da kansu a yayin da suke jinin al'ada.

A wasu lokutan 'yan mata kan yi amfani da takarda ko tsumma har ma da safa don tare jinin da ke zuba daga jikinsu.

Lamarin da likitoci ke gargadin cewa rashin tsaftar wadannan abubuwa ka iya shafar lafiyar iyayen gobe.

Ga wasu shirye-shiryen na baya da za ku so ku karanta da saurara