Gane Mini Hanya 29/03/2020 tare da shugaban kamfanin sarrafa shinkafa na Tiamin

Gane Mini Hanya 29/03/2020 tare da shugaban kamfanin sarrafa shinkafa na Tiamin

Latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron cikakken shirin:

A 'yan shekarun da suka wuce ana samun karuwar kamfanonin sarrafa shinkafa a Najeriya.

Ana dai danganta hakan da matakan da gwamnatocin kasar ke dauka na bunkasa noman shinkafar a cikin gida, kasancewarta cimakar da aka fi mu'amala da ita a Najeriyar.

Kamfanin sarrafa shinkafa na Tiamin da ke Kano, na daya daga cikin irin wadannan manyan kamfanoni.

Kwanakin baya da shugaban kamfanin, Alhaji Aminu Ahmad ya kawo mana ziyara sashen Hausa na BBC, Ahmad Abba Abdullahi ya tattauna da shi, inda ya fara da tambayarsa halin da ake ciki wajen aikin samar da shinkafar.