Lafiya Zinariya: Camfe-camfen da ake yi wa mata masu haila

Latsa hoton da ke sama domin jin cikakken shirin:

Wasu al'umomi a wasu bangarori na duniya na nuna kyama ko wariya ga mata masu jinin al'ada.

Hakan ya biyo irin kallon da suke yi wa matan da ke cikin wannan yanayi.

Lamarin da kan sanya matan cikin yanayi na takura duk kuwa da cewa duk wata mace da ta kai munzali dole ne sai ta yi jinin na al'ada.

Mata masu haila ne ke daukar ciki su hayayyafa kuma ta haka al'umma ke ci gaba da wanzuwa a doron kasa.