Gane Mini Hanya 21/03/2020

Latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron shirin:

Yayin da cutar coronavirus ke ci gaba da addabar kasashen duniya, wani bangare da take neman durkusarwa shi ne tattalin arziki da kuma ayyukan raya kasa na gwamnatoci.

Tuni dai cutar ta sanya farashin danyen man fetur a kasuwar duniya ya fadi warwas, lamarin da ya jefa kasashen da tattalin arzikinsu ya dogara kan man fetur cikin karin hatsari.

Najeriya na daya daga cikin wadannan kasashe kuma tuni gwamnati ta ce cutar za ta shafi kasafin kudinta na bana, yayin da gwamnatocin jihohi su ma cikinsu ya duri ruwa saboda yadda galibi suke dogara kan kaso daga tarayya.

A filinmu na Gane Mani Hanya, Is’haq Khalid ya tattauna da gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdulahi Sule kan wannan batu, da ma takaddamar da aka yi kan tura tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu zuwa hijira a jihar ta Nasarawa.

To amma gwamnan ya fara ne da bayanin irin matakan da jihar ke dauka don yaki da Coronavirus.