Gane Mini Hanya: Tasirin makarantun allo na zamani a Jihar Kebbi

Gane Mini Hanya: Tasirin makarantun allo na zamani a Jihar Kebbi

Latsa hoton sama ku saurari rahoton Haruna Ibrahim Kakangi

A Najeriya, daya daga cikin hanyoyin da ake ganin za su taimaka wajen rage yawan yara masu barace-barace da sunan almajiranci kan titunan kasar ita ce barin yara su yi karatun addini a gaban iyayensu.

A dalilin haka ne yanzu haka ake samun karuwar makarantun allo irin na zamani, inda iyaye ke kula da ciyarwa da walwalar yaransu.

BBC ta ziyarci jihar Kebbi, inda Haruna Ibrahim Kakangi ya hada mana rahoto na musamman kan matsalar yara masu barace-barace da kuma tasirin makarantun allo na zamani.