Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ba zan sasanta da Dogara ba — Jibrin

A farkon makon nan ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta kaddamar da bincike kan zargin cushe a kasafin kudin bana, da ake yiwa shugabannin majalisar wakilan kasar.

Kakakin Hukumar Wilson Uwujeren ya ce an aikawa da majalisar takardar ana neman wasu bayana a kan batun, kuma ya ce nan gaba akwai yiwuwar gayyatar jagororin majalisar domin yi musu tambayoyi.

Toshon shugaban kwamitin majalisar na kasafin kudi Hon Abdulmummini Jibrin, shine ya kaiwa da hukumar ta EFCC korafe korafe kan zargin cewa an tafka badakala a kasafin kudin.

A filinmu na Gane Mini Hanya, Yusuf Ibrahim Yakasai ya yi hira ta musammam da shi, inda ya fara da tambayrsa ko yaya ya ji da matakin na EFCC.

Labarai masu alaka