Algeria ta fito da sunayen 'yan wasanta

Algeriya ta saka sunayen Nadir Belhadj da Faouzi Chaouchi a cikin jerin 'yan wasan data zaba na wucin gadi da zasu taka mata leda a gasar cin kofin duniya a kasar Afrika ta Kudu.

Kocin kasar Rabah Saadane ya ce "zaban 'yan wasan ba karamin ciwon kai bane gare ni amma dai nayi la'akari da 'yan wasan da suka buga wasan zagayen kusada na gasar cin kofin Afrika".

Tawagar 'yan wasan Algeriya:

Masu tsaron gida: Lounes Gaouaoui (ASO Chlef), Faouzi Chaouchi (Entente Setif), Mohamed Lamine Zemmamouche (MC Alger), M'bohi Rais Ouheb (Slavia Sofia, Bulgaria)

Masu buga baya: Abdelkader Laifaoui (Entente Setif), Madjid Bougherra (Rangers, Scotland), Carl Medjani (Ajaccio, France), Rafik Halliche (Nacional Madeira, Portugal), Anther Yahia (Bochum, Germany), Habib Belaid (Boulogne-sur-Mer, France), Nadir Belhadj (Portsmouth, England), Djamel Mesbah (Lecce, Italy)

Masu buga tsakiya: Hassan Yebda (Portsmouth, England), Medhi Lacen (Racing Santander, Spain), Yazid Mansouri (Lorient, France), Adlene Guedioura (on loan at Wolverhampton, England from Charleroi, Belgium), Riad Boudebouz (Sochaux, France), Djamel Abdoun (Nantes, France), Fouad Kadir (Valenciennes, France), Mourad Meghni (Lazio, Italy), Karim Ziani (Wolfsburg, Germany), Karim Matmour (Borussia Moenchengladbach, Germany)

Masu buga gaba: Abdelkader Ghezzal (Siena, Italy), Rafik Djebbour (AEK Athens, Greece), Rafik Saifi (Istres, France)