Japan ta janye daga daukar gasar 2018

Hukumar kwallon kafa ta kasar Japan ta janye daga neman damar daukar bakuncin gasar cin kofin duniya da za ayi a shekara ta 2018, amma ta ce zata nemi daukar bakuncin gasar shekara ta 2022.

Ficewar Japan daga neman, ya bar Ingila da sauran kasashe shida masu neman daukar bakuncin gasar ta shekara ta 2018 a yayinda hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA zata sanar da kasar da zata dauki bakuncin gasar a watan Disamba.

Kasashen Australia da Russia da Amurka da kuma hadin gwiwar Belgium/Netherlands da Spain/Portugal duk suma suna nema.

Shugaban hukumar kwallon Japan Motoaki Inukai ya ce sun janye ne don su maida hankali wajen daukar bakunci a shekara ta 2022 tayin la'akari da cewar FIFA na son baiwa nahiyar Turai dama a shekara ta 2018.