Real Madrid ta sha a hannun Osasuna

A gasar La Liga ta Spaniya Real Madrid ta sha da kyar da sidin goshi inda ta doke Osasuna daci uku da biyu.

Tun daga farkon wasan dai sai Osasuna ta fara zira kwallo kafin Madrid ta farke har sai ana sauran minti daya a tashi wasan sannan Cristiano Ronaldo ya ciwa Madrid din kwallon daya bata nasara a wasan.

Barca wacce ke saman tebur da lallasa Vilareal ne daci hudu da daya.

Sevilla wacce take ta hudu kuwa ta samu galaba ne akan Athletico Madrid daci uku da daya.