Boateng zai iya bugawa Ghana kwallo

Boateng
Image caption Boateng na cikin 'yan wasan da zasu bugawa Black Stars leda a Afrika ta Kudu

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta amince tsohon dan wasan Jamus a matakin 'yan kwallo 'yan kasada shekaru 21 Kevin Prince Boateng ya koma bugawa Ghana kwallo.

Abinda hakan ke nufi shine dan wasan zai takawa Black Stars leda a gasar cin kofin duniya a wata mai zuwa.

Boateng na taka leda ne a Portsmouth ya ce yafison bugawa Ghana kwallo duk da cewar Jamus aka haifeshi.

Dama dai Kocin Ghana Milovan Rajevac ya saka sunan Boateng cikin jerin 'yan wasa talatin daya gayyata don fara horo.

Mahaifin Boateng dan Ghana ne kuma kawunshi ya takawa Ghana leda a shekarar 1990.

A halin yanzu dai FIFA ta cire batun kayyade shekarun dan wasa kafin ya canza kasar da yakeson bugawa kwallo.

A bayan dai duk dan wasan daya wuce shekaru 21 ba zai iya kara canza kasar da zai dunga bugawa kwallo ba.