Raul ya jin jinawa Ronaldo

Dan wasan da yafi kowanne tsada Ronaldo
Image caption Dan wasan da yafi kowanne tsada Ronaldo

Dan wasan Real Madrid Raul Gonzales, ya jin jinawa takwaransa Christiano Ronaldo yana mai cewa cikakken jagora ne.

Raul ya bayyana hakan ne sakamakon rawar ganin da Ronaldo ya taka a wasan da Real ta yi da Real Mollorca, inda ya zira kwallaye uku.

Raul yace Ronaldo ba karamin shugaba bane wanda ya kamata ayi koyi da shi, kuma babu shakka yana taimaka mana sosai.

Amma anasa martanin Ronaldo, ya alakanta nasarar tasa da gudummawa da kuma juriyar takwarorin nasa.

Kwallayen da ya zira dai sun kara Real Madrid kwarin gwiwa a yunkurin da take yi na cimma Barcelona domni lashe gasar La liga.