Chelsea ta lashe gasar Premier

'Yan wasan Chelsea na murnar kofin Premier da suka dauka
Image caption 'Yan wasan Chelsea na murnar kofin Premier da suka dauka

Kungiyar Chelsea ta lashe gasar Premier ta Ingila bayan ta lallasa Wigan Athletic daci takwas da nema a wasan da suka buga a filin wasa na Stamford Bridge.

Dama dai Chelsea na bukatar nasara ne a wasan don ta daga kofin kuma ta hana Manchester United lashe gasar a karo na hudu a jere.

A lokacin wasan dai Anelka ya zira kwallaye bu, sai Drogba yaci uku a yayinda Lampard da Kalou da kuma Ashley Cole suka zira kwallo dai dai.

Wannan shi ne karo na hudu da Chelsea ke lashe gasar ta Premier a tarihin ta. Kuma karo na farko a hannun Carlo Ancelotti.