Brazil bata gayyaci Ronaldinho ba

Robinho
Image caption Matashin dan wasa Robinho na daga cikin wadanda aka gayyata

Ba a gayyaci tsohon gwarzon dan kwallon duniya Ronaldinho cikin jerin 'yan wasan da Brazil ta gayyata don fara horo.

Brazil wacce ta lashe gasar cin kofin duniya har sau shida na rukunin H ne tare da kasashen Ivory Coast da Portugal da kuma Koriya ta Arewa.

Cikakken jerin 'yan wasan Brazil:

Masu tsaron gida: Julio Cesar (Inter Milan), Doni (AS Roma), Gomes (Tottenham Hotspur)

Masu buga baya: Maicon (Inter Milan), Daniel Alves (Barcelona), Michel Bastos (Olympique Lyon), Gilberto (Cruzeiro), Lucio (Inter Milan), Juan (AS Roma), Luisao (Benfica), Thiago Silva (AC Milan)

Masu buga tsakiya: Gilberto Silva (Panathinaikos), Felipe Melo (Fiorentina), Ramires (Benfica), Elano (Galatasaray), Kaka (Real Madrid), Julio Baptista (Roma), Kleberson (Flamengo), Josue (VfL Wolfsburg).

Masu buga gaba: Robinho (Santos), Luis Fabiano (Sevilla), Nilmar (Villarreal), Grafite (VfL Wolfsburg).