Hukumar FIFA ta kara baiwa Afrika ta Kudu kudi

Ana ci gaba da ayyukan gine gine a filayen wasa
Image caption Ana ci gaba da ayyukan gine gine a filayen wasa

Mutumin da yake jagorantar shirye-shiryen gasar cin kofin duniya da za a yi a Afrika ta Kudu, ya tabbatar da cewa hukumar FIFA ta kara baiwa Afrika ta Kudu dala miliyan dari domin karfafa mata gwiwa.

Babban sakataren hukumar Jerome Valcke, ya shaidawa BBC cewa hukumar ta sanya hannu kan karin kashi 25 cikin dari a taron kwamitin ta na zartarwa da ka yi a watan Maris.

Yace an bada kudadanne domin tabbatar da cewa kasar ta samar da masaukin 'yan wasa akan lokaci.

A yanzu dai kudaden da aka ware domin shirya gasar sun tashi daga pan miliyan 282 zuwa pan miliyan 349.

Mista Valcke yace wannan karin ba zai shafi kasafin da hukumar ta ware domin shirya gasar ba.